bayyinaat

Published time: 05 ,September ,2018      21:54:29
Na’am. Ya ce: To ai da ya halatta bauta ga wanin Allah, da ita tafi cancanta da ta bauta muku da fiye da ku ku bauta mata! Ashe kenan wanda ya umarce ku da bauta mata bai san maslaharku ba da sakamakon al’amarinku! Kuma ba shi da hikima cikin abin da ya kallafa muku.
Lambar Labari: 213



Sa’annan sai Manzo (s.a.w) ya fuskanci Mushrikan larabawa ya ce: Ku me ya sa kuke bautawa gumaka sabanin Allah (s.w.t)? Sai suka ce: Muna neman kusanci da Allah da wannan ne. Sai ya ce da su: Shin ita (gumakan) tana mai ji mai biyayya ga Ubangijinta ne kuma mai bauta gareshi shi ya sa kuke neman kusancin Allah da bauta mata da girmama ta? Sai suka ce: A’a. Ya ce: Ku ne kuka saka ta da hannunku? Suka ce: Na’am. Ya ce: To ai da ya halatta bauta ga wanin Allah, da ita tafi cancanta da ta bauta muku da fiye da ku ku bauta mata! Ashe kenan wanda ya umarce ku da bauta mata bai san maslaharku ba da sakamakon al’amarinku! Kuma ba shi da hikima cikin abin da ya kallafa muku.
Yayin da Manzo ya fadi wannan Magana sai suka yi sabani, wadansunsu suka ce da wasunsu: Allah ya shiga cikin wasu mutane ne da suke da wannan kamanni saboda haka ne muka suranta surarsu muna girmamata saboda mu girmama Ubangijinmu ta hanyar wannan sura da Ubangijinmu ya shige ta ya surantu da ita.
Wasunsu suka ce: Wannan surar ta wasu mutane ce da suka gabata suna masu bauta ga Allah kafinmu sai muka suranta surarsu muka bauta mata domin girmama Allah. Wasu kuma suka ce: Yayin Allah da ya halicci Annabi Adam (a.s) ya umarci Mala’iku da su yi masa sujada domin neman kusanci ga Allah, ashe ke nan mu muka fi cancanta da yin sujada a kan Mala’iku, amma tun da wannan ya kubuce mana shi ya sa muka suranta su muna yi musu sujada domin neman kusanci zuwa ga Allah kamar yadda Mala’iku suka nemi kusanci da Allah ta hanyar yin sujada ga Adam (a.s).
 
Amsa Wa Ra’ayin Farko
Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Kun kuskure hanya kun bace. Amma ku (yana Magana da masu ra’ayin farko) da kuka ce: Allah ya shiga jikkunan wasu mutane ne nagari da kuka suranta surarsu kuna girmamata don girmama wannan surar da ya shiga ciki, da haka kun siffanta Ubangijinku da siffofin ababan halitta, shin zai yiwu Ubangijinku ya shiga cikin wani abu har ya zama wannan abin ya kewaye da shi?. To menene bambancinsa da sauran abin da ya ke abubuwa na shiga cikinsa na daga launi da dandano da kanshi da taushi da kaushi da nauyi da sako-sako? Don me abin da ake shiga cikinsa ya zama Fararre kuma Kadimi ba tare da an samu warewar wannan Kadimi kuma wancan Fararre ba daban-daban? Yaya wanda bai gushe samamme ba kafin waje zai bukaci waje? alhalin shi Mabuwayi Madaukaki ya kasance kuma bai gushe ba yana nan yadda yake.
Idan kuwa kuka siffanta shi da siffar ababan halitta to ya lizimta muku ku siffanta shi da siffar gushewa, idan kuwa kuka siffanta shi da gushewa da faruwa to dole ku siffanta shi da karewa, domin wannan su ne suka hada siffofin masu shiga da wadanda ake shiga cikinsu, kuma dukkan wadannan siffofin masu jirkita ne, idan kuwa zatin Ubangiji Madaukaki bai jirkita ba sakamakon shigarsa cikin wani abu to ashe kenan haka yana yiwuwa!?
Yana yiwuwa kada ya canja ya zama yana motsi yana zama baki, yana fari, yana ja, yana yalo, kuma siffofin ababan halitta suna faruwa a kan mai siffantuwa da su, har ya zama yana da siffar fararru gaba daya, ya zama Fararre, (Allah kuwa ya daukaka daga haka daukaka mai girma). Sa’annan (s.a.w) ya ce: Idan abin da kuke tsammani na Allah yana shiga cikin wani abu to abin da kuka yi gini a kai yana rusa maganarku ne. Sai mutanen suka yi shiru suka ce: Zamu duba al’amarinmu.  

Amsa Wa Ra’ayi na Biyu
Sannan Manzo (s.a.w) ya fuskanci jama’a ta biyu ya ce: Ku ba ni labari idan kuka bauta wa surar wanda yake bauta wa Allah kuka yi mata sujuda, kuma kuka yi mata salla kuka dora fuskokinku masu daraja a kan kasa domin sujada a gareta me kuka rage wa Ubangijin Talikai?, amma kun sani cewa yana daga hakkin wanda ya lizimci a girmama shi da ibada kada a daidaita shi da bawansa.
Shin ba ku sani ba ne cewa da wani sarki ko wani mai girma zaku daidaita shi da bawansa a girmamawa da kaskantar da kai da tsoronsa, shin wannan ba kaskantarwa ba ne ga babba kamar yadda yake girmamawa ga karami ba? Suka ce: Na’am. Sai ya ce: Shin ba ku san cewa idan kuna bautawa Allah ta fuskacin bauta wa surar bayinsa masu bauta a gareshi kuna kaskantar da Ubangijin talikai ba ne? Ya ce: Sai mutanen suka yi shuru kadan suka ce: Zamu duba al’amarinmu.

Amsa Wa Ra’ayi na Uku
Sannan Manzo (s.a.w) ya ce da jama’a ta uku: Kun buga misali da mu da ku kuka kamanta mu da juna, alhali da mu da ku ba daya ba ne, saboda mu Bayin Allah ne ababan halitta da muke biyayya ga abin da aka umarce mu da shi, muke hanuwa da abin da aka hana mu ga barinsa, muke kuma bauta masa kamar yadda ya so, idan ya umarce mu ta wata fuska daga fuskoki sai mu bi shi, kuma ba zamu ketare wannan iyakar ba zuwa ga abin da bai umarce mu ba, domin ba mu sani ba ta yiwu da ya nufe mu da na farko ba ya son mu yi na biyun, kuma ga shi ya hana mu shiga gaba gareshi, yayin da ya umarce mu da mu fuskanci Ka’aba sai muka bi shi, sannan ya umarce mu da bauta a gareshi ta hanyar fuskantarta duk inda muke a sauran garuruwa wanda a cikinta ne muke yi masa biyayya, da wannan ba mu fita daga wani abu na daga biyayya a gareshi ba.
Yayin da Ubangiji (s.w.t) ya yi umarni da sujada ga Adam (a.s) bai yi umarni da yi masa sujada ba saboda surarsa da take ba ita ce shi (Adam) din ba, saboda haka ba ku da ikon kiyasta wancan a kan haka, domin ku ba ku sani ba tayiwu yana kin abin da kuke yi, domin bai umarce ku da shi ba.
Sannan Manzo (s.a.w) ya ce: Shin kuna ganin da wani mutum ya umarce ku da ku shiga gidansa wata rana da kansa shin zaku iya shiga bayan nan ba da umarninsa ba, ko kuma ku shiga wani gidan nasa daban ba wanda ya yi muku umarni da ku shiga ba? Ko kuma kuna ganin da wani mutum ya ba ku tufafi daga tufafinsa ko bawa daga bayinsa ko dabba daga dabbobinsa shin kuna iya karbar wannan?. Suka ce: Na’am. Sai ya ce: To zai yiwu ku dauki wani daban ba wanda ya ba ku ba? Suka ce: A’a, domin bai yi mana izini kan na biyun ba kamar yadda ya yi izini a na farko. Sai Manzo (s.a.w) ya ce: To ku gaya mini shin Allah (s.w.t) shi ne ya fi cancanta kada a shiga gaba gareshi ba tare da umarninsa ba ko kuma sashen ababan mallaka na daga bayi?. Suka ce: Allah ne ya fi cancanta kada a shiga gabansa a mulkinsa ba tare da izininsa ba. Sai ya ce: To me ya sa kuka yi haka? Yaushe ya umarce ku da ku yi sujada ga wadannan surorin? Imam Sadik (a.s) ya ce: Sai suka ce: "Zamu duba al’amarinmu”. Ya ce: "Na rantse da wanda ya aiko shi (s.a.w) da gaskiya kwana uku bai yi musu ba sai da suka zo wajan Manzon Allah (s.a.w) suka musulunta, sun kasance mutane ishirin da biyar ne; Biyar daga kowace kungiya. Suka ce: Ya Muhammad! Ba mu ga Mai dalili kamar naka ba, mun shaida kai Manzon Allah ne!” .







Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
www.haidarcenter.com

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: