bayyinaat

Published time: 05 ,September ,2018      22:00:47
Idan muka yi duba zuwa ga tsarin halitta gaba daya zamu ga yana da wani daidaito a cikinsa, da kayatarwa da take nuna mana mai halitta shi da yake tafiyar da shi guda daya ne.
Lambar Labari: 214
Idan muka duba dalilan da suka gabata zamu ga cewa lallai Allah (s.w.t) ba ya bukatar wani mai taimako a cikin ayyukansa, ba kuma zai yiwu ba wani ya taimaka sa, kuma ba mai iya samar da wani abu sai shi, don haka dukkan ayyuka da muke iya gani na bayi sai da izininsa da ikonsa suke samuwa.
Amma wannan ba yana nufin Allah ya tilasta bayi a kan ayyukansu ba ne, domin izinin Allah da ikonsa a kan halittunsa musamman mutane da su suna da irada da nufi da zabi, ya ta’allaka ne da su a matsayinsu na wadanda ya halitta su masu zabi.

Kadaitaka A Cikin Halittawa
Akwai dalilai da dama da suke nuni da kadaitakar mai yin halittu da zamu yi nuni da wasu daga ciki a nan a takaice;
1- Kayatarwa Da Daidaito A Tsari
Idan muka yi duba zuwa ga tsarin halitta gaba daya zamu ga yana da wani daidaito a cikinsa, da kayatarwa da take nuna mana mai halitta shi da yake tafiyar da shi guda daya ne.
Akwai misalai da zamu iya gani a cikin rayuwarmu ta yau da kullum, muna iya kallon ajin karatu da ya kunshi dalibai da kowannensu yake zaune a wajansa, da malami daya da kowanne yake sauraronsa, da mun kaddara cewa ajin yana dauke da malamai sama daya, kuma kowanne daga cikinsu yana bayar da karatu ga dalibai da suke gabansu shin za a samu daidaito a wannan tsarin?!
Don haka kamar yadda kididdigar malamai masu bayar da karatu ga dalibai ayyanannu a ajin karatu zai kawo lalacewar tsari da hargitsi da kwaramniya, haka ma idan ya kasance mai tsara wannan halitta da ya kasance mai kididdiga da ba a samu wannan daidaito da tsari da muke iya gani ba a cikin halittu.
 
2- Alaka Tsakanin Tsararru
Idan muka yi duba zuwa ga halittu kamar rana da wata da duniya da sauran duniyoyi gaba daya zamu samu cewa suna da alaka ta maganadisu a tsakaninsu.
Haka nan idan muka sake duba rana da wata da tasirin duhu da haske a kan sauran halittu kamar duwatsu da teku da kasa da shuke-shuke da dabbobi kuma da mutane zamu ga suna da alaka tsakaninsu.
Idan muka sake duba iska da tasirinta a kan mutane da ruwa da dabbobi da shuke-shuke zamu sake ganin wata alaka ta musamman, misali; mutum yana bukatar iskar da shuka take fitarwa, ita kuma tana bukatar iskar da mutum yake fitarwa, irin wannan alakoki masu yawa da ba zasu kirgu ba suna nuna mana kadaitakar tsari tsakanin dukkan halittu, wannan kuma yana nuna mai tsarawa guda daya ne.

3-Rashin Samun Tsarin Wani Ubangijin
Da hankali ya yi duba sai ya kasa samun wani tsari daban da ya saba da na wannan ubangijin guda daya makadaici, don haka sai ya yi hukunci da cewa ba mai samar da wanna tsararru sai shi guda daya, domin da ya kasance akwai wani bayansa da ya yi nasa halittu, kuma ya zo da nasa tsarin.
Imam Ali (a.s) yana cewa da dansa Hasan (a.s): Ka sani ya dana, cewa da ubangijinka yana da abokin tarayya da manzanninsa sun zo maka, kuma da ka ga alamomin mulkinsa da ikonsa, kuma da ka san ayyukansa da siffofinsa, sai dai shi ubangiji guda daya ne kamar yadda ya siffanta kansa, ba mai kishiyantar sa a mulkinsa, kuma shi ne mai halitta komai .
 
Idan Ka Ce:
Me zai hana a samu ubangizai masu yawa da zasu yi yarjejeniya a tsakaninsu domin su tsara ayyukan bayi ta yadda ba za a samu wani sabani ba a tsakaninsu kamar yadda yake tsakanin ma’asumai a tarihin rayuwarsu, kamar annbin rahma da wasiyyinsa imam Ali (a.s), Yusuf da babansa Ya’akub (a.s), Isa da Yahaya (a.s).

Sai Na Ce:
Wadannan da ka fada na daga bayin Allah (s.w.t) suna da sharadin su zama masu kaskantar da kawuka domin Allah ya zabe su daga cikin bayinsa madaukaka, don haka ne ya zama wajibi a kansu su kasance sun siffantu da siffofin bayi na gari, kamar kaskantar da kai, hada da cewa Allah ya yi musu dabaibayi da dokoki da sharudda masu wahala.
Amma ubangiji madaukaki ya daukaka da ya siffantu da siffofin ababan halitta, domin shi ubangiji kaskanci ne da tawaya gare shi ya kasance mai kaskan da kai, don haka ne ya zama yana daga siffofinsa na kamala ya kasance mai jiji-da-kai, mai takama, mai girman kai, mai danne kowane abu da karfinsa.
Hada da cewa yarjejeniyar da take tsakaninsu wadannan bayi na gari da ka ambata tana karkashin biyayya ne ga ubangiji madaukaki, don haka ne da mun kaddara ubangizai masu yawa da zasu kasance karkashin wata yarjejeniya, da sun kasance wadanda ake yi wa iyaka kenan, da kuma haka ne da ba su cancanci ubangizantaka ba, sakamakon tawaya da rauni da kaskancin biyayya ga waninsu.
Kaddara kasancewar dokar ta zo daga garesu ne, ba ya warware matsalar, domin ta kowane hali iradar kowannensu ba ita take wakana ba, domin kowannensu yana jefar da abin da ya yi nufi ne domin daukar abin da suka yi karo-karo wanda yake bai kebanta da dayansu ba, wanann kuwa ya rushe cikar samuwa da kamala.

Kadaitaka A Cikin Ibada
Bisa bincike da ya gabata a nan ne zai bayyana garemu a fili cewa; Babu wanda ya cancanci ibada sai Allah madaukaki. Don haka ne ma tun da shi ne mai samarwa, mai ni’imtawa, masani da maslahar bayi, shi ya sa ya kadaita da cancantar wannan ibada.
Kamar yadda dole ne wanann bautar ta kasance kamar yadda ya so ta hannun wanda ya so, don haka da wani daga bayi zai yi bauta kamar yadda Allah ya umarta, amma sai ya zamanto bai yarda da wanda ya aiko masa ba, ko kuma ba shi da soyayya da biyayya ga shi wanda ya aiko masa ko ya yi umarni da ya bi shi, da Allah ba zai karba daga gareshi ba.


Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
www.haidarcenter.com


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: