bayyinaat

Published time: 05 ,September ,2018      22:03:10
Cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi (n halitta) daga gare Shi , saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba ita ce abin siffantawar ba,
Lambar Labari: 215
A wajenmu siffofin Allah su ne ainihin zatinsa, don haka wadanda suka tafi a kan siffofinsa kari ne a kan zatinsa ko kuma suka kore masa siffofin kamala ba su sami dacewa ba da kamalarsa.
Domin siffanta shi da siffofin kari yana kai wa ga sanya shi abin kididdiga alhalin Allah daya ne ba shi da abokin tarayya, kamar yadda kore masa siffofin kamala yana kai wa ga sanya Allah tauyayye mai neman wanda zai cika shi, don haka sai ya koma daya daga ababan halitta da suke mabukata zuwa ga waninsu.
Shugabanmu Amirul Muminin (a.s) yana cewa:
Cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi (n halitta) daga gare Shi , saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba ita ce abin siffantawar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah (da irin wadancan siffofi) to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi, wanda ya tagwaita Shi kuwa ya sanya Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi, wanda kuma ya jahilce shi zai yi nuni gareshi, duk wanda kuwa ya nuna shi ya iyakance shi, wanda kuwa ya iyakance shi to ya gididdiga shi, wanda ya ce: A cikin me yake? To ya tattaro shi a wani wuri, wanda ya ce: A kan me yake? To ya sanya shi ba ya wani wurin .
Domin mu saukake fahimtar ma’anar siffofin kari da muka kore su ga Allah ga wani misali mai sauki; idan da zamu ce "A” yana da siffofi kamar haka; mai hakuri ne, mai basira ne, mai arziki ne, mai kyauta ne. A nan "A” yana da siffofi guda hudu, amma shi kadai ne. Idan wani ya ce siffofin nasa kari ne a kan zatinsa, wato suna da samuwarsu mai zaman kanta kamar yadda ash’arawa suka fada game da siffofin Allah madaukaki guda bakwai, to a nan yana cewa ne "A” su biyar ne. Wato "A” shi kansa da kuma sauran siffofi hudu. Wannan shi ne dalilinmu na cewa yawan siffofi ba ya nuni zuwa ga yawan samamu a zahirin waje.
Amma daya daga cikin malaman mu’utazila da ya kore siffofin kamala daga Allah kamar cewa; siffar Allah mai iko tana nufin shi maras gajiyawa ne, ya yi haka ne domin gudun kada ya kamanta Allah da bayi, domin yana ganin cewa siffanta Allah da iko ko ilimi, da kuma siffanta bayi da iko ko ilimi yana nufin an kamanta shi da su bayin.
Abin da ya gafala da shi a nan shi ne, idan an siffanta Allah da ilimi ya bambanta da siffanta ba yi da ilimi, domin ilimi a wajan Allah ainihin zatinsa ne, amma ga bayi ba zatinsu ba ne, wani abu ne da yake bijiro musu su siffantu da shi, hada da cewa ilimin Allah ba shi da iyaka domin shi ne ainihin samuwar Allah, amma ilimin bayi takaitacce ne kamar samuwarsu.

Siffofi Tabbatattu (Subutiyya)
Wadannan irin siffofi su ne ake kira da siffofin kamala da kyawu kamar ilimi, da iko, da wadata, da nufi, da rayuwa, wadanda suke su ne ainihin zatinsa, su ba siffofi ba ne da suke kari a kan zatinsa ba . Siffofin duk da sun sassaba a ma’ana amma suna nuni zuwa ga hikika daya ne wanda yake shi ne Allah madaukaki: Wadannan siffofin sun kasu gida biyu kamar haka; Na zati da Na aiki.

1-     Na zati: Siffofin zati kamar samuwa da rayuwa da iko da ilimi, wadanda suke su ne ainihin zatin ubangiji madaukaki, a irin wadannan siffofin ba a iya kore wani bangare nasu daga gareshi madaukaki, ba zai yiwu a ce Allah mai ilimi ne da "A” amma ba shi da ilimi da "B” ba.

2-    Na aiki: Siffofin aiki kamar halittawa da rayawa da arzutawa wadannan su ne siffofin da muke fahimtarsu ta hanyar kallon ayyukansa madaukaki, a irin wadanan siffofin kana iya cewa Allah ya halicci "A” amma bai halicci dansa "B” ba.

Siffofi Korarru (Salbiyya)
Korarrun siffofi su ne siffofin da suke kore duk wani aibu ko tawaya daga ubangiji, wadannan siffofi suna nuni zuwa ga tsarkin Allah daga siffantuwa da siffofin halittunsa na tawaya domin shi kamala ne tsantsa, ba shi da wata tawaya kuma ba a kwatanta wani da shi, misalinsu;
1-    Allah ba jiki ba ne
2-    Ba mai gabobi ba ne
3-    Ba a iya ganinsa
4-    Ba shi da waje
5-    Ba ya bakata
6-    Ba shi da abokin tarayya
7-    Ba shi da sura
8-    Ba shi da motsi ko rashinsa
9-    Ba shi da nauyi ko rashinsa

Saudayawa takaitaccen tunani na dan Adam yakan sanya shi ya jingina iyaka ga ubangijinsa mahaliccinsa, wannan kuwa yana faruwa ne sakamakon iyaka da shi yake da ita, saudayawa zamu ga irin wannan har a cikin rayuwar dan Adam, ta yadda zamu ga mutane masu halaye suna rayawa cewa kowane mutum yana da irin wadannan halayen nasu.
Don haka ne masu hikima suke buga misali da cewa; da za a ce tururuwa ta siffanta Allah da babu wani mamaki idan ta siffanta shi da cewa yana da kafa hudu da kuma antenna biyu a kan idanunsa.
Amma abin mamaki shi ne da aka samu wasu daga jama’ar musulmi da take da littafin shiryiya a hannunta da suka siffanta Allah da jiki, da ana iya ganinsa, da saukowa daga sama, da magana, da mahalli, da sauran siffofin tawaya.
 
Samakon Bincike
Don haka da wannan binciken mun tabbatar da cewa Allah madaukaki ba shi da abokin tarayya a zatinsa, ba shi da tamka a siffofinsa, ba shi da tsara a ayyukansa, babu wani mai cancantar ibada bayansa.



Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
www.haidarcenter.com

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: