bayyinaat

Published time: 05 ,September ,2018      22:26:56
Bayan haka: Tabbas ilimi na Aklak shine: ilimin da yake sanar da mu siffofin ruhi masu kyau da marasa kyau, kamar yadda yake sanar da mu ayyukan kirki da wadanda bana kirki ba. Bugu da kari gashi yana bayyana mana yadda za a samu wasu da yadda za a nisancewa wasu dabi’un.
Lambar Labari: 216
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI.
Dukkan yabo da godiya su tabba ga Allah madaukakin sarki. Tsira da amincin Allah su kara tabba ga Manzon tsira Muhammad dan Abdullahi  da Iyalen gidanshi tsarkaka.
Yau kuma zamuyi Magana ne akan Aklak, da banbancin ilimin aklak tsakanin shi da sauran ilimunmuka na addinin musulunci. Sai kuma Magana akan Gaskiya, Boye sirri, Afuwa da sassauci, kan-kan-da-kai, Giba, Nisancewa Kirkiro karya, Biyayya ga iyaye, da kuma Gimama malami.
MA’ANAR AKLAK:
Bayan haka: Tabbas ilimi na Aklak shine: ilimin da yake sanar da mu siffofin ruhi masu kyau da marasa kyau, kamar yadda yake sanar da mu ayyukan kirki da wadanda bana kirki ba. Bugu da kari gashi yana bayyana mana yadda za a samu wasu da yadda za a nisancewa wasu dabi’un.
BANBANCIN ILIMIN AKLAK DA SAURAN ILIMUMMUKA.
Bayan munyi bayani akan ma’anar ilimin Aklak wato dabi’u masu kyau, zai yiwu mu ayyana wasu wurare mabanbanta dake tsakanin wannan ilimi da sauran ilimummukan addinin musulunci kamar Akida da ilimin Fikihu.
Ilimin Akida yana sanar da mu Allah da sunayensa da siffofinsa, yana kuma siffantawa mutum rayuwa bayan mutuwa da abinda yake jira a cikinta, yana kuma kiran mutum yayi imani da wasu tabbatattun abubuwa kamar samuwar Allah da sakonnin Annabawan Allah da rayuwa bayan mutuwa.
Hakama ilimin Fikihu, tabbas yana sanar da mu hukunce-hukuncen shari’a da ingantattun hanyar yin ibadu da sauke nauyin da shari’a ta dorawa mutum. Misalin haka yana sanar damu yadda ake yin tsarki, alwala, sallah, da kuma abinda zamu karanta a cikin sallolin mu da yadda zamu yi Azumi, aikin hajji, da yadda zamu bada zakka, da yadda ma zamu yi saye da sayarwa. Da sauran ayyukan idaba.
Amma ilimin kyawawan dabi’u shine ya dauki nauyin koyawa mutane kyawawan halaye da kyawawan ayyuka, kamar yadda yake bayyana mana munan halaye da ayyuka marasa kyau da yadda yake siffantawa da ta farkon yake kuma nisancewa ta biyun. Misalin haka kuwa shine tabbas ilimin Aklak yana koyawa mutum yadda zai zamo Jarumi, yanda zaka zauna da ‘yan uwanka mutane lafiya da kuma yadda mutum zai yi kar ya zama marowaci, ka kuma zama mai soyuwa a tsakanin Jama’a.
MUHIMMANCIN AKLAK A MUSULUNCI.
Ana son mutum yasan wadannan abubuwan masu zuwa ya kuma siffantu dasu.
1 Yasan Muhimmancin AKLAK a cikin kur’ani mai girma. 2 Ya karanta ruwayoyin da suka zo daga Manzon tsira Annabin Musulunci Muhammad dan Abdullahi (s.a.w) da Imamai ma’asumai (a.s) akan Muhimmancin AKLAK a musulunci. 3 Ya motsa himmarshi a wajen gyara dabi’unshi ya bayar da kokarinshi akan samun kyawawan dabi’u.
A baya munyi bayani akan ma’anar ilimin dabi’u kyawawa, hakama fifikon wannan ilimi da sauran ilimummukan musulunci. A yanzu kuma zamu bayyana muhimmancin kyauwawan dabi’u da matsayinsu a musulunci.
Allah ( T.A) a kur’ani mai girma ya kira mutum don yayi kokarin samun kyawawan dabi’u, ya kuma nisacewa dabi’un dake kaskantar da dan Adam. Kamar yadda yayiwa Annabi (s.a.w) wasiyya da Imaman tsira (a.s)- tunda sune zakaran gwajin dafin kyawawan dabi’u da kuma ko wane ayyuka na mutum, hakama a cikin maganganunsu da kalmominsu madaukaka domin sun siffantu da dabi’u da siffofi masu kyau.
Zamu fara bayanani da bayyana muhimmancin kyawawan dabi’u da darajarsu a cikin kur’ani mai girma, sannan mu kawu wasu maganganun ma’asumai (a.s).
AKLAK A CIKIN KUR’ANI:
Zamu tabo abin da ya zo a cikin kur’ani na AKLAK:
DABI’U MASU KYAU SUNE SIRRIN CIN NASARAR MANZON                                              ALLAH (S.A.W):
Allah ya fada mana a cikin kur’aninsa mai girma cewa sirrin cin nasarar Manzon Allah (s.a.w) a cikin Isar da sakon addinin shi da kiran mutane zuwa musulunci ya tabbata ne a cikin madaukakan dabi’unshi ne, Allah yake cewa: {{ فبما رحمة مّن الله لنت لهم ولو كنت فظّا غليظ القلب لانفضّوا من حولك فاعف عنهم واستغفر لهم وشاورهم فى الامر فاذا عزمت فتوكّل على الله انّ الله يحبّ المتوكّلين   
{ Ba don rahamar Allah ba da bakayi musu taushi ba, da ka zamanto mai mugun hali mai kaushin zuciya da sun waste sun bar gefenka, kayi musu afuwa ka gafarta musu ka shawarce su a cikin al’amari, idan kayi nufin yanke al’amari to ka dogara ga Allah tabbas Allah yana son masu dogara   da shi}(1) .
HIKAYA:
Malaman tarihi sun tabbatar da cewa: wata Rana Manzon Allah (s.a.w)  yana zaune tareda Sahabbansa, sai wani Mutumin kauye ya ganshi sai ya taho wajenshi, lokacin da mutumin ya gane shine Manzon Allah (s.a.w) sai ya kusanto shi cikin fushi, ya kama abayar Manzon Allah (s.a.w) ya matse Annabi da ita matsewa mai tsanani har ya shake Manzon Allah (s.a.w). sai mutumin cikin kaushi ba ladabi ya ce: Ni talaka ne, ka bani daga cikin dukiyar da Allah ya baka! Sai Manzon Allah (s.a.w) ya dago kanshi yana murmushi ya kalle shi cikin tausasawa sannan ya waiwaya wajen Sahabbanshi yana son su taimakawa wannan mutumin talaka.
Da yin wannan aikin ne Manzon Allah (s.a.w) ya sa wannan Balaraben kauyen ya nutse cikin kogin koyi da jin nauyin mummunan abin da ya aikata.
KYAUWAWAN DABI’U SUNA JANYO RABAUTA:
 Allah madaukakin sarki yana fada a cikin littafinshi mai girma Alkur’ani cewa: siffantuwa da kyawawan dabi’u da halaye na gari da nisancewa halayen banza da munanan dabi’u suna jawu rabauta da dacewa, kuma yana tsoratar da wadanda suke tsarkake kawukansu sai a Jarrabe su da munanan dabi’u, bayan ya rantse da nafsun Mutum yake cewa: ( Hakika wanda ya tsarkake kanshi ya rabauta* Wanda ya rufe tada laifuffuka hakika ya tabe)(2) .
MUGUN HALI YANA JAWU RASA IMANI:
Ya zo a cikin kur’ani mai girma cewa: tabbas idan mutum yayi munanan ayyuka marasa kyau bai kuma nisancewa munanan dabi’u ba, to lallai makomar lamarinshi zai zamo kin yadda da samuwar Allah da karyata ayoyinshi a karshe kuma zai rasa Imaninsa gaba daya. Allah mai girma da daukaka yayi Magana akan wasu mutane Ashararai inda yake cewa: { Sannan Akidar wadanda suka munana aiki ya zama munana saboda sun karyata ayoyin Allah kuma suke yiwa ayoyin Allah izgilanci}(1) .
ثم كان عقبة الذين أسئوا السوأى أن كذّبوا بئايت الله وكانوا بها يستهزءون                 ))
A KULA:
Karuna daya ne daga cikin wadanda suka siffantu da son Duniya da dabi’un alfasha, bai kasance yana sauraron nasiha da da’awar Annabi Musu (a.s) ba, don haka bai yi Imani da Allah ba, al’amarin shi dai ya kai ga an saukar masa da azabar Allah.
Ka duba kur’ani mai girma ka karanta bayanan kissar rayuwar shi da abubuwan lura da suke ciki.
Zamuci gaba insha Allah a kasha na biyu inda zamu kawu kyawawan dabi’u a cikin ruwayoyi, da Dabi’u a cikin Maganganun Imamai Ma’asumai (a.s). Allah yasa mudace.
Aliyu Abdullahi Yusuf: What’s app, Telegram, Instgram Number: +2348037493872. Da sauran Social Media.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: