bayyinaat

Published time: 05 ,September ,2018      22:31:17
DABI’U DAGA MAGANGANUN MANZON ALLAH (S.A.W): Manzon Allah (s.a.w) a wata ruwaya yake cewa: (( Na horeku da kyawawan dabi’u, lallai kyawawan dabi’u ba makawa suna Aljanna, kar kuyi mummunan halaye, tabbas munanan haliye ba makawa suna cikin wuta))
Lambar Labari: 217
Cigaba daga kashi na farko Magana akan Aklak, inda a nan kuma zamu kawu: Kyauwawan Dabi’u a cikin Ruwayoyi da kuma Dabi’u daga Maganganun Imamai Ma’asumai (a.s). za kuma mu shiga wasu daga cikin littatafan AKLAK ta yadda zamuga Maganganun da Malamai sukayi a kan Aklak. Dafatan zamu amfana da wannan aikin insha Allah.
DABI’U A CIKIN RUWAYOYI:
kyawawan Dabi’u suna daya daga cikin madaukakiyar daraja a cikin ruwayoyin Musulunci:
DABI’U DAGA MAGANGANUN MANZON ALLAH (S.A.W):
Manzon Allah (s.a.w) a wata ruwaya yake cewa: (( Na horeku da kyawawan dabi’u, lallai kyawawan dabi’u ba makawa suna Aljanna, kar kuyi mummunan halaye, tabbas munanan haliye ba makawa suna cikin wuta))(1)
An ruwaito daga wajensa (s.a.w) a wata ruwayar ta daban ya ce: { Tabbas bawa yana samun darajar mai Azumi mai tsayuwar dare sanadiyyar kyawawan dabi’un shi}(2) .
HIKAYA:
Wani mutum ya zo wajen Manzon Allah (s.a.w) ta gaban shi sai ya ce: { Ya Manzon Allah, meye addini? Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ba shi amsa  cewa: (( Kyawun dabi’u)). Sannan ya zo masa ta daman shi ya ce: meye addini? Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce mashi: (( Kyawun dabi’u)). Sannan  ya zo mashi ta hagun shi ya ce: meye addini? Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce mash: (( Kyawun dabi’u)). Sannan  ya zo mashi ta baya ya ce mashi: meye addini? Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce mashi: (( wai shin baka ganewa ne? Addini shine kar kayi fushi)).
DABI’U DAGA MAGANGANUN IMAMAI MA’ASUMAI (A.S):
Imam Ali (a.s) ya fadi girman dabi’u yake cewa: Tabbas mu koda ba muyi Imani ba bama kwadayin aljanna, bama jin tsoron wuta, bama tsammanin a zaba ko sakamako to a tareda haka abin da yafi dacewa mu binkito kyawawan dabi’u, domin suna kawu tsira da rabauta da samun dacewa)(1) .
Imam Sadik (a.s)  ya ce: Tabbas kyawun dabi’u yana goge kura-kurai kamar yadda rana take narkar da kankara.(4) .
Kamar yadda ya nuna girman kyan dabi’u  yake cewa: Tabbas Allah madaukakin sarki yana bawa ladan kyan dabi’u kamar yadda yake bawa Mujahidi a cikin tafarkin Allah da yake yin sammako yake kuma dawuwa da yammaci)(5) .
Imam Bakir (a.s) ya ce: kyan dabi’u yana cikin alamomin imani: (( Tabbas mafi kamalar muminai a imani shine wanda yafi su kyan hali))(6) .
Wasu daga cikin malamai da yawa sunyi kokari wajen bada lokacin su da zube basirar su, sunyi rubutu akan kyawawan dabi’u domin suma su bada gusumuwar su ga al’umma baki daya. Da yawa daga cikin wadannan littattafan da suka rubuta sun kawu irin dabi’un Manzon Allah (s.a.w) da kuma dabi’un iyalen gidanshi tsarkaka, kai dama wasu daga cikin dabi’un Sahabban shi managarta.
WASU DAGA CIKIN KYAWAWAN DABI’U.
A bayanin daya gabata munyi bayani akan muhimmancin kyawawan dabi’u a cikin addinin musulunci mai bayyanawa. A wannan karon zamu bayyana wasu kyawawan siffofin da kowanne musulmi yake bukata don gina alakokin zamantakewa masu kyau da zasu kai shi ga rabauta.
Zamuyi sharhin wasu dabi’un da kur’ani mai girma da ruwayoyin Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka karfafa yin su.
GASKIYA:
Gaskiyar na nufin Magana da rashin yiwa wasu karya tana cikin dabi’u masu kyau. Allah (T.A) yana fada a cikin kur’ani mai girma: (( Ya ku wadanda suka yi imani kuji tsoron Allah ku kasance tareda masu gaskiya))(1) .
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ku zama masu gaskiya, domin gaskiya tanada albarka, karya kuma shu’umace(8) .
Kamar yadda Imam Ali (a.s) ya ce: (( Gaskiya tana tserar da kai ko da kaji tsoron ta, karya kuma zata halakar da kai ko da ka amince mata))(9) .
Munin karya babba ne yana kuma da hatsari har ya kai ga manyan mutane suke nisancewa kankanuwar karya ma ko karyar da ake yenta saboda barkwanci.
Faiduk kashani ya fada a littafinsa Almahajjatul Baida’u: (( Wani mutum ana ce mashi Abdullahi bn Amir ya ce: Wata Rana Manzon Allah (s.a.w) ya zo gidanmu lokacin ina yaro. A lokacin na shagala da wasa, sai naji muryar mahaifiyata tana kirana tana cewa: kai dana zo kusa dani zan baka wani abu. Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce ma babata: me kike son ba shi? Sai ta amsa cewa: Dabino zan bashi. Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Idan baki ba shi dabino ba za  a rubuta miki laifin karya daya(10) .
BOYE SIRRI:
Boye sirri yana daga cikin abinda zamu iya cewa shima daya ne daga cikin kyawawan dabi’u wanda ake so mutum ya siffantu da shi. Idan mutum yasan sirrin wani mutum, kuma wannan mutumin baya son wasu su san wannan sirrin, lallai wannan abin ya zama sirrin wannan mutumin, bai halatta mutum ya sanar da wasu wannan sirrin ba ba tareda yardar wannan mutumin ba.
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: (( Duk wanda yaji maganar wani mutum ba kuma ya son a fadi maganar to ta zama amana koda bai nemi ya boye ta ba))(11) .
Kamar yadda ya wajaba mutum yayi kokari gwargwadon iyawarsa kar ya sanar da wasu sirri kansa ko da kuwa abokai ne, sau dayawa wata rana zasu iya zama makiyan wannan mutumin.
Imam Ali (a.s) yana cewa: ka kiyaye sirrinka da kanta, kar ka gayawa wani. Domin in amintacce ne wataran zai rikice ya yada sirrinka, ko in Jahili ne ba a yarda da shi ba zai yiwu ya ha’ince ka wata rana sai ya yada sirrinka(1) .
AFUWA DA SASSAUTAWA:
Allah mai girma da daukaka, da kuma Imamam addini sun karfafa kan cewa da mutum zai yiwa wani mutum ta’addanci, abin da yafi wannan mutumin ya yiwa wanda yayi masa ta’addanci afuwa maimakon yayi kokarin daukar fansa da ramuwa.
Allah (T.A) yana cewa a cikin kur’ani mai girma: ( Duk wanda yayi afuwa ya gyara ladanshi yana wajen Allah)(2) . Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Bana baku labarin fiyayyun dabi’un Duniya da Lahira ba? Yiwa wanda ya zalunce ku afuwa, ka sadar da zuminci da wanda ya yanke maka da kyautatawa wanda ya munana maka da bawa  wanda ya hana ka))(3) .
Zamuci gaba a kasha na uku insha Allah, inda zamuci gaba da Magana akan AFUWA da sauran bangarori na kyawawan dabi’u.
Aliyu Abdullahi Yusuf:  What’s app, Telegram, Istagram Number: +2348037493872. Da sauran social Media.
 

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: