bayyinaat

Published time: 05 ,September ,2018      22:34:17
hakika mai hikima cikin littafinsa mai girma ya ce: يَرْفَعْ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنْكُمْ وَالَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ دَرَجَاتٍ
Lambar Labari: 218
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Hakika kowanne irin gini ya doru kan asasi da tushensa kuma daga nan gobensa ke bayyanuwa, ko bahaushe ma na cewa duk wata juma'a tun daga laraba ake gane ta.
Yaya dalibin ilimi zai iya sanin makomarsa?
Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai tsira da aminci su kara tabbata ga mafificin halittun Allah Muhammad da iyalansa tsarkaka.
Bayan haka: hakika mai hikima cikin littafinsa mai girma ya ce:
﴿يَرْفَعْ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنْكُمْ وَالَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ دَرَجَاتٍ﴾.
Allah ya na daukaka darajojin wadanda sukai imani da wadanda aka baiwa ilimi
Babu kokwanto daukakar mutum da girmamarsa da daukakar mukaminsa kadai dai yana cikin iliminsa mai amfani, wanda ya tsayu da gaskiya da iklasi da cika alkawari, duk sanda mutum ya karu da ilimi da aiki sai ya karu cikin daukaka da dagawa da kusanci daga madaukaki mafi daukaka jalla jalaluhu, lallai Allah yana daukaka darajarsa a lahira da karatunsa da ayyukansa
 (yi karatu ka samu daukaka)
babu shakka cewa darajojin lahira cikin aljannoni suna banbanta daga darajojin duniya da darajojin barzahu.
Shi ilimi tsani ne na samun daukaka ga mutum da hawansa zuwa ga kololuwar kamala, da kuma kololuwar mutumtakarsa, ya zuwa abin da Allah ya ajiye cikin halittarsa lafiyayya kuma samammiya daga son kyawu da alheri da kamala.
Lallai Allah matsarkaki yana kaunar masu neman ilimi wadanda suke fitowa daga gidajen su, su tafi neman ilimi dare da rana, kadai dai ya kaunace su saboda shi Allah matsarkaki shi ne ilimi cikin zatin sa da siffofinsa da ayyukansa, shi ne masani mai sani mai yawan sanin gaibobi, ya san abin da yake sammai da abin da yake kasa, ya san sirri da boye, babu wani abu da yake buya daga iliminsa ko da gwargwadon kwayar zarra ne cikin sammai da kasa, ya san abin da rayuka ke boyewa da zukata, ya san mai ha’intar idanu, Allah Azza wa Jalla shi ne tsantsar ilimi, babu wanda ya san shi waye sai shi, idan ya so bawa sai ya bashi daga ilimin sa ya fahimtar da shi rayuwa.
Sai dai cewa wannan ilimi na Allah bari dai da dukkanin wani abu mai kima da daraja, da abin da yake kishinyantar sa cikin duniya da abin da yake sabawa da shi da wani abu jabu da wanda ba a kwadayinsa, sai dai cewa shi yana bayyana mai cudanya da tufafin gaskiya mai yin ado da hakika, wannan shi ne abin da kur’ani mai girma ya yi ishara zuwa gare shi kamar yanda yake cikin fadinsa madaukaki:        
﴿فَأَمَّا الزَّبَدُ فَيَذْهَبُ جُفَاءً وَأَمَّا مَا يَنفَعُ النَّاسَ فَيَمْكُثُ فِي الأَرْضِ﴾،
Amma kumfa sai ya tafi kekasasshe amma abin da yake amfanar da mutane sai ya zauna cikin kasa.
Tafki lokacin da yake tuma yake cakuda igiyar ruwa a samansa za kaga wani yanki na kumfa yana bayyana da za ai tsammanin cewa daga ruwa take, sai dai cewa cikin wannan kumfa babu komai sai iska, idan akwai ruwa ciki to lallai zai zauna cikin tafki.
Cikin duniya akwai sinfi biyu masu kishiyantar juna a ko da yaushe kamar kishiyantar da ke tsakanin dare da rana, sune malamai da jahilai, sakamakon kishiyantar da take tsakanin ilimi da jahilci, sau da yawan lokuta jahili yana rigantuwa da rigar malamai sai dai cewa shi daga jabun kumfa yakeWannan lamari ne mai hatsari sakamakon cudanyar takardu da rikicewar lamari kan mafi yawan mutane, suna bin mutumin da bai kasance malami ba a hakikani da gaskiya, sai dai cewa shi kawai yana nuna cewa yana da ilimi, wannan rikicewar lamari yana gudana cikin da yawa-yawan abubuwa masu karo da juna da kishiyantar juna cikin dukkanin kasashe da zamani.
Mafahim din zamantakewar juna da siyasa nawa ne damu da abubuwa cikin su suke rikicewa tsakanin hakikani da jabu tsakanin gaskiya da karya
Kamar muslunci da ilimi da siyasa da fanni da juyin-juya hali, ta iya yiwuwa mutum ya kasance dan siyasa.
 haka ma musulmi zai iya kasancewa masani wani fanni daga fannoni ko kuma masani fanni musulmi, kuma mu samu dan juyin-juya hali mumini, ko kuma mumini dan juyin-juya hali, banbanci nawa ne tsakaninsu na tushe  
     Bayanin haka: me ye banbanci tsakanin musulmi da dan siyasa da dan siyasa da musulmi? Wannan tambaya bijirarra ce a fage da wannan lokaci.
Domin kaiwa zuwa ga abin da muke muradi daga takaitaccen bayani cikin wannan lamari mai muhimmanci za mu buga misali kan haka domin ya kasance matsayin sharar fage domin shiga cikin maudu’i, daga bayyanannen lamari ne cewa buga misali daga bayan sa akwai hikima da manufofi kamar yanda ya zo cikin kur’ani mai girma:

﴿وَلَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ﴾ ﴿وَمَا يَعْقِلُهَا إِلاَّ الْعَالِمُونَ﴾ ﴿لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ﴾.
{domin su yi tunani} {babu masu hankaltuwa da ita face masu ilimi} {saransu sa tuna}
Wane abu yake banbanta tsakanin mumini Ali bn Abu dalib (a.s) da dan wuta Mu’awiya bn Abu Sufyanu , dukkanin su a wurin wasu musulmai suna siffantuwa da halifancin manzon Allah (s.a.w), sarkin muminai halifa na hudu wurin wasu mutane amma wurin mu Imamiya halifa ne na farko ba tare da yankewa ba ga manzon Allah (s.a.w) kamar yanda Mu’awiya kadai ya fizge sunan halifanci da zalunci da fin karfi a kansa, sai ya zama kowanne daya daga cikinsu yana siffanta da halifancin manzon Allah (s.a.w) dukkanin su su biyun suna sallah suna azumi suna shaidawa da shahada biyu sai dai cewa daya daga cikinsu musulmi ne dan siyasa dayan kuma dan siyasa musulmi, dayansu haske ne kuma gaskiya ne, dayan kuma bata da duhu yaya za mu banbance tsakaninsu, dukkaninsu musulmai ne yan siyasa, sai dai cewa dayansu musulmi ne dan siyasa dayan kuma dan siyasa musulmi?
Muhimmanci banbance wannan maudu’i bai buya ba, lallai ya zama dole a yi Karin bayani kansa daga lafiyayyar mukaddima domin natija ta kasance lafiyayya ta hanyar lafiyar mukaddimar da aka gina kanta daga (sugrayat) da (kubrayat) kamar yanda yake cikin limin mandik.
A takaice muna cewa: lallai banbanci tsakaninsu shi ne lallai shi dan siyasa musulmi yana sanya addini da hukunce-hukuncensa kamar sallah da hajji cikin amfani da su a siyasarsa shin cikin gama garin maslaha ne ko kebantacciya, lallai shi duk da kasantuwarsa musulmi sai dai cewa yana siyasantar da addinin muslunci cikin maslahohinsa, ya dinga amfani da addini cikin bukatun siyasarsa, idan wata rana addininsa da siyasarsa sukai karo da juna lallai zaka same shi yana mai gabatar da siyasarsa da fifita ta kan addini, sai ya fice daga addini yayi munafunci ya dinga rigantuwa da muslunci a zahiri sabanin badini, kamar yanda shugaban shahidai (a.s) ya fada:       
 (والدين لعق على ألسنتهم يحوطونه أينما درّت معائشهم)،
Mutane bayin duniya addini kuma kadai damfare yake kan harsunansu sune kewayawa duk inda rayuwarsu ta juya.
Yana daga cikin munafuncin siyasa dan siyasa ya kasance musulmi, shi ne wanda yake sanya addinin cikin bukatarsa ta siyasa, matukar dai muslunci bai yi karo da bukatunsa na kashin kansa ba da siyasarsa to shi musulmi zai kuma dinga nuna muslunci da sallah, amma idan ya kasance addini yana cutar da siyasarsa lallai zaka same shi cikin gaggawar ya sauya ya bayyanar da ainahin aniyar da take boye cikinsa daga munafunci ya kuma yi wurgi da watsi da addini, ya kasance daga munafukan musulmai, lallai shi yana bayyana muslunci yana boye da kafirci, sai ya dinga shaidawa da kalmomin shahada biyu a zahiri kamar yanda zaka same shi ya na sallah sai dai cewa shi a badininsa cike yake da kafirci, kamar yanda Yazidu bn Mu’awiya (l.a) bayan kashe Shugaban Shahidai Imam Husaini (a.s) ya raira wake yana fadin:  
 (لعبت هاشم بالملك فلا خبر جاء ولا وحي نزل)،
Banu Hashim sun yi wasa da mulki ba tare da wani labari da ya zo ba ko wani wahayi da ya sauka ba.
Bari dai kakansa ma Abu Sufyan ya fadi kwatankwacin haka a lokacin halifancin Usman bn Affan yana mai cewa (Babu wata Aljanna ko Wuta) ya Banu Umayya ku jujjuya wannan mulki kamar jujjuyawar kwallon kafa, zahirinsa daga musulmai amma badininsa daga kafirai, wannan shi ne ainahin munafunci a cikin akida da aiki, wannan Kenan cikin tasnifin dan siyasa da ake kirga shi (dan siyasa musulmi) shi ne wanda yake sanya addini cikin hidimtawa bukatunsa da muradunsa da manufofinsa.
Amma musulmi dan siyasa kamar misalin sarkin muminai Ali (a.s) lallai shi ya ce (lallai Mu’awiya bai fini iya shirya makirci da dabara ba) domin Mu’awiya ya shahara wurin larabawa a wancan lokaci dacewa shi ne yana daga makiran larabawa, kadai dai tsoran Allah ne yake hana Imam Ali (a.s) aikata abin da Mu’awiya ya aikata, sarkin muminai ya kasance yana siffantuwa da zuhudu da tsantseni da tak’wa, abin da yake wajabta masa sanya siyasa cikin hidimtawa addini bawai akasi ba kamar yanda Mu’awiya yayi. Lallai shi tsantseni da tak’wa suna hana sanya addini cikin hidimtawa maslahohin siyasa, bari suna sanya siyasa cikin hidimar addini cikin tabbatar da shi da yada shi, matukar dai siyasa tana hidimtawa addini lallai zai dauketa kayan aiki domin kaiwa ga Allah matsarkaki madaukaki, da wannan ne musulmi yake kasantuwa dan siyasa bawai dan siyasa musulmi ba.
Umar Alhassan salihu
+989196659356
08162040719
Faroukumar66@gmail.com


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: