bayyinaat

Published time: 05 ,September ,2018      22:36:30
Allah yana son masu kyautatawa}(1) . Abin da za a gano a wannan ayar shine Manyan Mutane basa gafartawa wasu kura-kuransu kawai, kai kyautata musu ma suke yi suyi musu alheri ma.
Lambar Labari: 219
Cigaba daga kashi na biyu, yanzu kuma zamuci gaba da Magana akan kyawawan dabi’u da muke Magana akanshi. Inda muke Magana akan yin Afuwa a cikin darasin mu na AKLAK yanzu kuma zamuci gaba.
Allah madaukakin sarki yana fada a cikin kur’ani mai girma: { Wadanda suke ciyarwa a cikin yalwa da cikin tsanani da masu hadiye fushi da masu yiwa mutane afuwa Allah yana son masu kyautatawa}(1) .
Abin da za  a gano a wannan ayar shine Manyan Mutane basa gafartawa wasu kura-kuransu kawai, kai kyautata musu ma suke yi suyi musu alheri ma.
Littattafan Tarihi sun kawu cewa Malikul Ashtar wata rana ya zo wucewa ta kasuwa sai wani Mutum mara natsuwa ya hadu da shi, daman bai san Malikul Ashtar ba sai ya kalle shi kallon wulakanci saboda kayansa basu da kyau sannan ya jefe shi da bushasshen tabo, shi Malik ma bai kula ba sai yaci gaba da tafiyar shi. Nan da nan Mutanen wajen suka cewa wannan mutumin: ka san waye wanda kake jifa kuwa? Sai  ya ce: A’a, sai suka ce masa: Malikul Ashtar ne Babban kwamandan mayakan Amirul Muminina (a.s). sai mutumin yayi nadama a kan abin da yayi, nan da nan ya tafi yana neman Malik sai ya same shi a masallaci yana ta yin sallah. Bayan Malik ya idar da sallar shi  sai Mutumin ya zo ya fadi kasa yana sunbatar kafafuwan Malik, sai Malik ya tambaye shi saboda me kake haka? Sai Mutumin ya ce: Ina son ka karbi uzirina akan abin da nayi maka dazu, nan da nan ya ce mashi: Ba komai wannan ai ba wani abu bane, ya ce na rantse da Allah ban shigo masallacin nan ba sai don in nema maka gafarar Allah(T.A)(2) .
KAN-KAN-DA-KAI:
Ma’anar kan-kan-da-kai shine Mutum yayi mu’amula da mutane cikin kauna da tausasawa da kyawawan dabi’u, ya kuma nisancewa rudi da girman kai, kar ya ga kansa yafi wani.
Daga cikin wasiyyoyin Lukman da yayiwa dansa akwai inda ya ce mashi: [ kar ka yi tafiya a kan kasa cikin takama lallai kai ba zaka iya huda kasa ba, ba ka kuma kai tsahon duwatsu ba](3) .
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: (( Duk wanda yayi kan-kan-da-kai don Allah [ a cikin mu’amalar shi da mutane] Allah zai daga shi [a cikin mutane](4) .
Dole ne mu san cewa kan-kan-da-kai din nan fa dole ya zama don Allah, ba don samun wasu amfanunnukan Duniya da matsayi ba. Imam Ali (a.s) yana cewa: Lallai duk wanda yayiwa mawadaci kan-kan-da-kai saboda kwadayin dukiyarsa yayi a sarar 2/3 biyu bisa ukun addininsa(5) .
Ya zo a cikin ruwayoyi Imam Hasan (a.s) ya zo wucewa ta wani waje sai yaga talakawa suna cin abinci ba komai a akushin sai bushassiyar gurasa. Da suka ganshi sai suka ce: ya jikan Manzon Allah! Bismilla mana kaci abinci. Sai ya zauna a kan gwuwuyinshi yaci abincin tareda su, sannan ya ce: Lallai Allah baya son Mutumin da ya rudu. Sannan Imam ya dauki talakawan nan suka tafi gidanshi yayi musu walima(6) .
NISANCEWA YI DA MUTANE (GIBA):
Giba ita ce Mutum ya fadi aibin wani ya siffanta shi da hali mara kyau a lokacin da baya nan a gaban wasu, saboda idan yana nan yaji maganar ba zai ji dadi ba, ba zai yadda da haka ba.
Allah (s.w.t) ya siffanta giba, wata cin naman wani a cikin kur’ani mai girma da cin naman mutum wato kamar Mutum yana cin naman dan uwanshi daya mutu: { kar kuyi liken asiri kar wasunku suci naman wasu shin dayanku ya so yaci naman dan uwanshi da ya Mutu, kar ku so haka kuji tsoron Allah tabbas Allah mai yawan karbar tuba ne mai jin kai ne(7) .
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Tabbas duk wanda yaci naman namiji ko mace musulma Allah ba zai karbi sallar shi da Azumin shi na kwana arba’in har sai wannan mutumin da akaci namansa ya yafe!(8) .
NISANCEWA KIRKIRO KARYA:
Kirkiro karya shine Mutum ya fadi abin da ba haka ba akan dan uwan shi ko ‘yar uwar shi, wanda idan Mutum yaji ba zai ji dadi ba.
Imam Ridha (a.s) yana cewa: (( Duk wanda yayi mumini ko mumina kage ko ya fadi abin da bai yi ba, Allah zai tsayar da shi ranar Alkiyama a kan tudun wuta har sai ya warware maganar))(9) .
BIN IYAYE BIYU:
Wajibi ne akan kowanne Musulmi ya girmama iyayensa, kar yayi duk wani aiki ko maganar da zata jawo bacin ransu. Allah (T.A) yana cewa a cikin kur’ani mai girma: {{ Ubangijinku yayi wasiyya kar ku bautawa kowa sai shi ku kyautatawa iyaye ko dayansu ya tsufa ko duk su biyun kar ku ce mu kash kar ku kyare su ku gaya musu Magana ta karamci* ka yi musu kan-kan da kai ku tausasa musu ka ce ya Ubangijina ka tausaya musu kamar yadda suka raine ni ina karami}}(10) .
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: [ Duk wanda iyayenshi suka yadda da shi yana da kofofi biyu a bude na gidan Aljanna, idan daya ne ya yadda da shi to kofa daya ce](11) . Manzon Allah (s.a.w) ya ce: kallon iyaye biyu da tausasawa da rahama idaba ne.
GIRMAMA MALAMI:
Ilimi da koyan ilimi suna da madaukakin matsayi a addinin musulunci: Manzon Allah (s.a.w) ya cewa Abu Zarri: (( Ya Aba Zarri Allah yafi son zaman sa’a daya a wajen da ake koyar da ilimi fiye da karatun kur’ani sau dubu goma sha biyu))(12) . Saboda haka malami da mai koyarwa suna da babban hakki a wajen mutum, kamar yadda Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Duk wanda ya sanar da kai harafi to ka zama bawan shi. Duk dai a Biharul Anwar din.
A nan zamu dakata daga dan takaicen wannan rubutu da mukayi Allah ya sa mudace. Munyi bayani akan Ma’anar Aklak, da kuma banbancin ilimin Aklak da sauran ilimummukan addinin musulunci, da kuma yadda kyawawan dabi’u suke janwo Rabauta.
Allah ya fadi sirrin cin nasarar Manzon Allah (s.a.w) a cikin isar da sakon Musulunci wanda dabi’unsa kyawawa ne suka jawo hakan.         Ma’anunin kur’ani suna hukunta cewa kyawawan dabi’u su suke jawo Rabautar mutum Duniya da Lahira.
Munyi Magana akan Gakiya, Boye sirri, Afuwa da sassautawa, kan-kan-da-kai, Giba, Girmama Iyaye da Kuma Girmama Malamai. Aminci ya tabbata ga wadanda suka ga gaskiya kuma suka bita.
Aliyu Abdullahi Yusuf: What’s app, Telegram, Istagram Number: +2348037493872. Da sauran social Media.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: