bayyinaat

Published time: 09 ,September ,2018      20:46:19
CI GABAN 'SIRRIN ZAMAN DUNIYA DUBE GA MA'ANA' sai ya tafi gurin malamin yana kuka ya nemi taimako. Sai malamin ya tambaye shi ya ce: 'me ka ke nema? me ya sa ka yanke kauna? sai dogari ya ce
Lambar Labari: 220
Gabatarwa
Da sunan Allah Mai rahma Mai jin kai. Allah Ya yi dadin tsira ga Shugabanmu Annabi Muhammad da Iyalan gidanshi tsarkaka. Dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, Wanda Ya tsiri halitta dukkanta daga ciki ya kyautata surar Dan’Adam a bisa kyawun daidaito, Ya kuma saukar mashi da shiriya domin isa ga kamalar da aka halicce shi domin ta, ta hanyar ManzanninShi (AS), wadda daga cikinsu Ya yiwa Shugaban Ma’aika (S.A.W.A.) tambari da, ‘Kuma, lalle hakika kana a kan halayen kirki manya’ (Al-Qur’an: Al-Qalam: 4).
Mun kudiri aniyar zabo Qissoshi ko labarai masu dauke da darusa saboda yadda labarai suke da matukar tasiri wajen isar da sakon abin da ya faru ga mutanen baya domin ya zama izna ko darasi ga na yanzu da wadanda za su zo. Dan haka mun tsamo wadannan qissoshi ne daga littafa daban-daban, wasu ma daga cikin littafan yaren Farisa ne wato Farisanci, inda a karshe za mu kawo sunayensu.

1. CI GABAN 'SIRRIN ZAMAN DUNIYA DUBE GA MA'ANA'
sai ya tafi gurin malamin yana kuka ya nemi taimako. Sai malamin ya tambaye shi ya ce: 'me ka ke nema? me ya sa ka yanke kauna? sai dogari ya ce: 'sarki ne ya zabe ni domin na nemo mashi bishiyar rabauta wadda 'ya'yanta suke dauke da ruwan rayuwa ta har abada, amma na dauki tsawon shekaru ban sami inda take ba, ban da isgili da dariya ba abin da na fuskanta daga jama'a. sai Malamin ya yi dariya ya ce: ya kai bawan Allah mai tsarkin zuciya! ai ba komai bace wannan bishiya sai bishiyar ilmi a zuciyar dan'Adam. Itace doguwar bishiya mai ban al'ajabi, tabbas shine ruwan rayuwa ta har abada.
Ai kuskure ka yi da ka tawo neman sura wato zahirin sunan abu maimakon ma'anarshi, waccan babbar ma'anar ta Ilmi ai tana da sunaye barkatai. Wani lokaci ana kiransa bishiya, wani lokacin kuma Rana, haka kuma ana kiran sa da teku wani lokacin kuma hadari, ilmi yana da dubunnan tasirori da alamomi, mafi kankantar tasirinsa shine 'rayuwa ta dindindin'.
Ilmi da Sani abu daya ne. Kamar mutun daya mai dauke da sunaye da alamomi da dama. Misali mahaifinka za ka ga yana da sunaye da yawa alhali shi daya ne, gare ka uba ne amma ga mahaifinshi da ne, ga wani makiyi ne amma ga wani masoyi ne ko aboki. Dan haka duk wanda ya yi dubi ga suna kawai ba tare da ya yi tunani akan ma'anar abu ba; to kuwa wannan mutun zai dawwama cikin dimuwa kamar kai. Kai ma sunan bishiya ka rika maimakon sirrin bishiya, dan haka ka saki suna ka kama ma'ana da sifa domin isa ga hakikanin abu. Dukkan rarraba da sabani suna tsirowa ne daga suna, amma a tekun ma'ana akwai nutsuwa da hadin kai ka ji bawan Allah'.

2. A DUK HALITTAR ALLAH AKWAI KYAKKYAWAN DALILI
Wata rana wasu mutane biyu matafiya suna tafiya a lokacin zafi, to da zafin rana ya tsananta ya kasance akwai matukar wahala su ci gaba da tafiyar, sai su ka ga wata babbar bishiya a kusa da inda su ke, sai su ka rakuba karkashin inuwarta domin su huta.
A yayin da su ka kishingila, sai dayansu ya daga kai sama ya dubi bishiyar nan sai yace: "wannan wacce irin banzar bishiya ce haka. ba ta ko 'ya'ya balle mu ci, ga itacenta ma ko makamashi ba zai yi ba"
"kada ku zama butulu mana," inji bishiyar ta mayar mashi da jawabi. "ai kuwa na kasance mai matukar amfani a gare ku a wannan lokaci, saboda na kare ku daga matsanancin zafin ranar nan. Amma duk da haka za ku ce min mara amfani!"
Masu karatu abin girmama wa mu sani babu wani abin halitta da za a ce ba shi da amfani. Addinin musulunci yana koya mana kimanta da mutunta halittu komai kankantar su, domin duk abin da muka gani yana daga cikin ni'imomin Allah Ta'ala. Ta yadda za mu ga yadda shugabannin shiriya suke mana nasiha dangane da ni'imomi kamar haka:
- Ma'aikin Allah (Sallallahu alaihi wa Aalihi wa sallam) yana cewa: 'Duk wanda ba ya ganin ni'imomin Allah Ta'ala a kanshi, sai a abin cinsa da abin shansa da tufafinsa kadai; to wannan ya takaita aikinsa kuma azaba ko horonsa yana kusa' (al-Kafi, mujalladi na 2, shafi na 316, lamba ta 5).
- Al-Imam al-Hassan al-Mujtaba (alaihis-salam) yana cewa: 'ana jahiltar ni'ima a yayin wanzuwarta; sai bayan ta gushe kuma sai a fadaka da kima da mafaninta.' (Bihar al-Anwar, mujalladi na 78, shafi na 115, lamba ta 12).
dan haka dangane da ni'ima godiya ake yi ga wanda ya ba da ita, Shi kuma sai ya kara wa bayinShi. Allah Ya saka mu cikin masu godiya.

3. MU NISANTA KANMU DAGA GURIN ZARGI
Wata rana wani manomi ya yi sabuwar shuka sai Zalbe (tsuntsu ne mai kama da balbela amma ya fi ta girma, yana kiwo a bakin ruwa) suka je suka tone masa ita, suka lalata ta. Da manomin nan ya ga haka sai da yamma likis ya je ya saka tarko na raga (net) a gonar, kashegari da zuwan sa kuwa sai ya samu a tarkon wani zalbe masu yawa da kuma Babba-da-jaka guda daya.
"Ina rokon ka ka sake ni" inji Babba-da-jaka, ya ci gaba da cewa "na rantse ban ci hatsin ka ba, ban kuma yi maka wata barna ba, babu ruwana kamar yadda za ka iya gani ina kula da mahaifiyata da mahaifina, ina..."
sai Manomin ya katse shi yace: "yi min shiru duk abin da kace zai iya kasancewa gaskiya, to amma na kama ka tare da wadanda suke yi min barna, dan haka yau za ka dandanda abin da abokan tarayyar ka za su ji".

4. ALHERI DANKO NE
Wata rana ana matukar zafi , wata Tururuwa ta fita neman ruwa. Bayan ta sha yawon nema sai a karshe ta iske wata korama. Sai ta hau kan wata ciyawa domin isa ga ruwan, tana kokarin haka sai ta zame ta fada ruwan.
a daidai wannan hali ashe wata Harbiya ta gan ta, nan da nan cikin zafin nama ta kawo mata dauki, ta hanyar tsinko ganyen bishiya ta jefa kusa da tururuwa domin ta kama ta kubuta. haka kuwa  aka yi tururuwa ta kama ganyen nan ta hau ya kawo gaba ta samu ta iya fitowa zuwa tsandauri.
To a daidai wannan lokaci, akwai wani mafarauci kuma da ya jefo tarkonshi na raga zai kama wannan harbiya.
Da tururuwan nan ta ga haka sai ta hau kafar mafaraucin nan ta gartsa mashi cizo a agara, sai zafi ya sa wurgar da tarkon gefe guda, ita kuma harbiya ta samu damar kubuta, ta tashi ta gudu.

5. LABARIN WANI BAWA MAI SADAUKAR WA
Abdullahi bin Jafar wato mijin Sayyida Zainab al-Kubra (salamullahi alaiha), ya kasance daga cikin mafi kyautayi na zamaninshi. Wata rana yana wuce wa ta gefen wata gonar dabino, sai ya ga wani bawa ya na yin aiki a gonar, a daidai lokacin kuwa an kawo wa bwan nan abincinsa, yana kokarin fara ci; sai ga wani kare ya zo gurin, yana kada bindinsa alamun yana jin yunwa.
Sai Bawan nan ya gutsirar masa abincin ya ba shi, Karen ya cinye. sai ya kuma gutsiro masa ya jefa masa, Karen nan ya kuma cinye wa, haka Bawan nan ya yi ta yi har abincin nan ya kare duka ga Karen nan, shi kuma bai ci ko kadan ba.
Sai Abdullah ya tambayi Bawan nan yace: 'to abincin ranar naka har guda nawa ne?' sai Bawan yace: 'shine dai wannan da ka gani'. Sai Abdullah ya ci gaba da cewa: 'to me yasa ka gabatar da bukatar kare a kan taka?' sai yace: 'wannan Karen ya zo daga nesa ne kuma yana jin matsananciyar yunwa, ni kuma ba zan ji dadi ba ace ya wuce ta nan gurin alhali yana mai jin yunwa'. Sai Abdullah ya ce: 'to kai kuma ya za ka yi da yunwar yau? sai yace: 'da hakuri da kuma tsayuwa wajen jure yunwa a haka har na kai dare'.
A yayin da Abdullah ya ga irin wannan sadaukar wa ta wannan Bawa, sai ya ce: 'wannan Bawa ya fi ni sadaukarwa; saboda haka domin zaburar wa akan aikin alkhairi, sai ya sayi gonar dabinon da kuma Bawan daga ma'abocinsu, sannan ya 'yan ta bawan kuma ya ba shi gonar dabinon da duk abin da ke cikinta.
- Imam Ali (alaihissalam) yana cewa: Sadaukarwa shine mafi kololuwar karimci. Haka nan ya kuma cewa: Sadaukarwa sifa ce ta mutanen kwarai (Ghurar al-Hikam, lamba ta 986).
- Haka nan Imam (AS) ya kuma cewa: da sadaukarwa ne 'yantattu su ke zama bayi. (kamar na baya, lamba ta 4187)

To alhamdulillahi ‘yan uwa masu karatu a nan ne muka kawo qarshen Sashe na shida  a wannan darasi namu na Akhlaq, dan haka sai a saurare mu a fitowa ta gaba wato ‘Mu koyi kyawawan dabi’u na bakwai’.

Hassan Adamu



Littattafan da aka duba sune:
1. al-Kur'ani mai tsarki
2. Al-Kafi
3. Bihar al-anwar
4. 100 moral stories
5. Labaran Masnavi maulavi
6. Hikayathaye shanidani
7. Ghurar al-Hikam
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: