bayyinaat

Published time: 09 ,September ,2018      21:11:14
aikin hajji ya samu kulawa da himmatuwar musulmi da manya-manya malaman su tare da dukkanin sabanin mazhabobin su tun ranar farko da aka wajabta shi duk da sassabawar makarantun su na tunani da aqida da fiqihu
Lambar Labari: 221
da sunan Allah mai rahama mai jin kai
dukkanin godiya ta tabbaga ga ubangijin talikai tsira da aminci su kara tabbata ga mafi darajar halittun Allah muhammadu da iyalansa tsarkaka la'ana madawwamiya kan makiyansu da masu inkarin falalarsu
aikin hajji ya samu kulawa da himmatuwar musulmi da manya-manya malaman su tare da dukkanin sabanin mazhabobin su tun ranar farko da aka wajabta shi duk da sassabawar makarantun su na tunani da aqida da fiqihu, malamai sun yi rubuce-rubuce sun amfanar da zaurukan nazarin muslunci da rubutun su mai daraja game da aikin hajji da hukunce–hukuncesa  cikin litattafan fiqihu, haka ma game da sirrikan hajji da hikimomin sa  cikin litattafan irfani.
duk sa'ilin da  ilimi da fanni da sana'a  da fannonin fasahar zamani suka samu cigaba sai kaga mutane sun qara kusantar qara bincike kan ilimin addini,sai kwaxayin samari da suke cikin qishurwar son sanin hikma da falsafar hukunce-hukunce da dalilan shari'a mai tsarki ya qaru, sakamakon abin da ke cikin sa daga albarkoki da tsinkaya da sirrika, sannan kuma manufar aikin hajji da dukkanin ibadu a cikin muslunci shi ne samun azurta da rabauta da samun tsarkakakkiyar rayuwa da tsarkake zukata da haskaka kwakwale da tarbiyar ruhi haka bai tabbata face  ta hanyar aikata shari'a da fuskanta da wayewa da fiqihu.
sannan shi hajji wani qarfafaffen alqawali ne da ya ke tsakanin bawa da ubangijin sa, lalle shi hajji na daga cikin mafi girman farillai tun lokacin halittar Adamu har zuwa tashin qiyama.  

 
إِنَّ أَوَّلَ بَيْتٍ وُضِعَ لِلنَّاسِ لَلَّذِي بِبَكَّةَ مُبَارَكاً وَهُدىً لِلْعَالَمِينَ  
lalle xaki na farko da aka sanyawa mutane da yake bibakka mai albarka wanda kuma ya ke shiriya ga talikai.
cikinsa akwai alfanun duniya da addini wadda ke tattara kan matakai xaixaiku da jama'a da dukkanin zurfinta na tattalin arziqi da siyasa da zamatakewa da wayewa da dai makamantan su…..
hajji ya kasance sannan bai gushe ba ya na matsayin cibiya kuma batu da asasi ga ilimummukan sanin Allah don tsarkake zukata da yaye su da xebe haso tare da Allah matsarkaki cikin madaidaicin tsari da siraxi miqaqqe fuskanin tsantsar kamala da kamala tsantsa gwargwadon ziri biyu ko kuma mafi kusanci daga ubangijin talikai.
hajji cikin ayyukan sa da alamomin sa na ibadu da siyasa ba komai bane face wasu damammaki da kuma masaukar imani wadda mumini da mumina ke motsawa don neman arziqi madawwami, bayan canji mai zurfi na asali cikin suluki.
lalle shi taron hajji da ake yi shekara-shekara na duk duniya ya tattaru kan alfanu mai girma ga dukkanin musulmi, kamar yadda cikin gundarin sa da asalin sa shi ne kusantar Allah ga dukkanin muminai
سئل الامام الصادق  7 عن معنى المنافع في قوله تعالى : (لِيَشْهِدُوا مَنافِع ) أهي منافع الدنيا أم الآخرة ؟ فقال  7: الكلّ
 an tambayi imam Sadiq (as) ma'anar alfanu cikin faxin sa maxaukaki shin alfanun duniya ake nufi ko kuwa na lahira? Sai imam ya ce: dukkanin alfanu.
bai buya ba kan cewa alfanun xaixaiku da jama'a suna game dukkanin fagagen rayuwa tun daga tattalin arziqi da siyasa da wayewa kai hatta alfanun askarawa da wasunsu…
shi hajji addini ne kuma daula ne, shi rayuwa ne kuma al'umma, tsakanin bangunansa biyu ya tattaro duk wata kudura ta tunani da tattalin arziqi da suluki da ilimi.
 hajji mazhari ne ma'abocin haskaka ga kudurar al'umma musulma da izzarta da haxin kanta da qarfinta, lalle shi aikin hajji na koyar da musulmi yaya za su kasance  sai ya basu qarfi da izza  ya haxa sahun su da zukatan su.
Imam komaini (rd) ya ce shi hajji kamar misalin hajjin qirani da kowa ke amfana da shi, sai dai cewa malamai  da masu zurfafa da tsinkaya kan abubuwan da suka damu al'umma musulmi idan sun wurga zukata cikin tafkin ma'anoni, sannan ba su tsaya sunyi qasa a gwiwa cikin kusanta da nitso cikin hukunce-hukunce da siyasarsa da zamantakewa  da sannu za su tsinci gwagwalan a cikin wannan tafki da ciki daga gwagawaln shiriya da hikima da `yanci, da sannu za su sha su qoshi har abada daga tatacciyar hikimarsa da ilimi
sai dai cewa yanzu meye abinyi? ina zamu tafi da wannan baqin ciki mai girma kasantuwar aikin hajji ya wayi gari abin gujewa da hijircewa kamar misalin hajjin qirani? lalle kamar yadda littafin rayuwa da kamala da kyawu ya buya gare mu dalilin hijabin da muka saqa da hannuwanmu, kamar yadda aka binne taskokin sirrikan kyawawan halaye cikin turbayar tunaninmu karkatatta, harshen xebe haso da shiriya ya tabarbabre ya koma harshen firgita da mutuwa da qabari…..
haka aka jarabci hajji da wannan musiba, sai qarshen al'amari ya zamanto miliyoyin musulmi suna tafiya makka duk shekara su taka qasar da annabi Ibrahim (as) ya taka tare da matarsa hajara sai dai cewa babu xaya cikinsu da ke tambayar kansa game da Ibrahim da muhammadu da kuma mai suka aikata? menene hadafinsu?  me suka nufa? ataqaice: lalle wajibi ne kan musulmi baki xayansu da su dage wajen sabunta rayuwar hajji da qur'ani mai girma, da dawo da su zuwa fagen rayuwarsu.
babu shakka bayan farkawar muslunci samari sun nufi rungumar addini, lalle shi hajji ya tufatantattu da sabon bugu kaxan kaxan ya fara komawa haqiqaninsa a cikin duniyar muslunci, muna fatan fuskantar musulmi  ga muslunci da wayewa ta qaru da yunqurinsu da motsinsu na wayewa da kawo gyara.
daga wannan tushen ne muka sanya wannan littafi muna fatan wasu ladubban ma'anawiyya da sirrikan xakin Allah mai alfarma su yaye, da alamomin wurare masu daraja da kaburbura tsarkaka, ya zama tilas ga wanda ya ke son zurfafa da nitso cikin tafkin waxannan ma'anoni  maxaukaka da wannan aiki mai tsananin wahala mai albarka da ya yi bincike ya lura ya sanya hankali cikin ayoyin qur'ani da suke da alaqa da hajji da ayyukansa da hukunce hukuncensa, haka ma ya duba hadisai masu daraja da aka naqalto daga annabi(saw) da imamai tsarkakan gidan wahayi da isma, lalle dukkanin sirrika da aka ambata a baya da sannu za su yaye cikin wannan ibada da waninta…. wadda ta bayyana ta yaye ga malamai da masu dandaqe karatu masu karamci da masana fiqihu da arifai masu girma, kaxai tushenta da mabubbugarta ya kasance daga ayoyin qur'ani da hadisai masu daraja.
lalle shi hajji cikin kowacce shekara ya na ishara  da  bayyana wani babban taro na ibada da siyasar muslunci, ya zama wajibi ga wanda al'amarin ke hannunsu da su tsara da shirya masa wani tanadi don mutane su halarci alfanunsu na addini da duniya  ga dukkanin matakai da cikin kowanne fage.
mai ya fi kyawu daga abin da mahajjata xakin Allah mai alfarma da maziyarta qabarin manzon Allah (s.a.w) da iyalan gidansa a madina haskakakka ke xauke da shi daga wayewa da fahimta da sanin hukunce-hukunce da hikimomi cikin hajji da ziyara suna haskaka da hasken Allah suna xebe haso da ambatonsa.
a bayyana ya ke cewa shi addini bayani ne kan wasu adadin dokoki da hukunce–hukunce da ubangiji da ya sunnanta su kan bayinsa ya    aukar dasu don shiriyarsu, ya aiko da annabawa dasu don mutane su tsaya kan adalci, rayuwarsu ta kasance rayuwa ingantatta, su rayu cikin aminci su rabauta duniya da lahira.
Umar Alhassan Salihu
+2348162040719
+989196659356
Faroukumar66@gmail.com



comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: