bayyinaat

Published time: 09 ,September ,2018      21:21:53
Aure shine asasi na farko domin tubalin ginin iyali, kum ashine tubalin gina al'umma, ta yadda za a yi ginin babba wajan cigabantar da al'umma, kuma rashin sa na kawo faxuwar al'umma da rashin ci gaban ta.
Lambar Labari: 222
AURE
Aure shine asasi na farko domin tubalin ginin iyali, kum ashine tubalin gina al'umma, ta yadda za a yi ginin babba wajan cigabantar da al'umma, kuma rashin sa na kawo faxuwar al'umma da rashin ci gaban ta.
Aure a mahangar musulunci wani rukuni ne mai qarfi wanda ake qulla shi a bisa asasi da qa'idoji da ladubba, gami da sunnoni da kevantattu dokokin da suka shafe shi, cikin sa akwai haqqoqi da wajibobi, waxanda ke wajabta lada ko azaba gurin mahalicci.
Lokacin da aka qulla wannan alaqa mai tsarki a kan waxannan qa'idoji da haqqoqi, za a samu fa'ida a rayuwar ma'aurata, kai har ma 'yayan da zasu haifa, waxanda zasu zo qaraqshin waxannan qa'idoji da tsaruka, ta hanyar haka ne za a toshe qofar varna cikin mutane sai al'umma ta zama ingantacciya ta gari.

MANUFA DA FA'IDAR AURE
Kamar yadda aure ya ke shine bulon farko, wajan ginin iyali da al'umma, yana da manufofi da natijoji tare da fa'idoji kamar haka : 'akwai qosar da sha'awa da neman zuri'a, cikar mutuncin mutum, hutu da nutsuwar rai, kamewa da sauran su.
Musulunci a matasyin sa na addinin Allah ya xauki aure da muhimmanci, kuma ya kwaxaitar da samari yin aure, sannan shi aure abu ne na larura, ma'ana ya zama dole ga wanda ba zai iya kare kansa ba, domin sababi na na tsira daga fasadi da in kaxaici, sannan hanya ne ta wanzuwar zuri'a sannan da cigaban ta da tarbiyya iyali da xaukar wahalhalun su matuqar ana buqatar su.
Dole ne a buqaci haihuwa, wasu malaman na cewa : muddin ana buqatar samar da zuri'a dole ne a haxu tsakanin namiji da mace (saduwa), sakamakon haka ne za a iya samun yaqini da wanzuwar zuria, muddin suna rabe to ba za a tava kaiwa ga kamala ba da wanzuwar sum sabida zuwa wanna kamalar, da buqata daga raxaxin kaxaici, da samun shiriyar hankali, da shiga cikin al'umma, ba abinda zai samar da waxannan abubuwan idan ba aure ba, domin ta hanyar qulla aure ne, namiji zai zama namiji, mace ma ta zama mace, ta wata fuskar kuma mutumtakar su ba zata tava cika ba sai a qaraqshin inuwar aure.

KWAXAITARWAR MUSULUMCI A KAN AURE
Yin aure tsakanin samari, na kare haxurran da za a iya fuskanta lokacin samarta, da rage yaxuwar cututtuka, addinin musulumci na son a yi aure lokacin samartaka kafin gushewar daxi da kuzarin quruciya.
Domin yin aure lokacin da mutum ya fara manyantaka na rage xanxano da zaqin aure, a kwai ruwayoyi da yawa da ke nuni kan haka (yana daga arziki mutum kada 'yar sa ta yi jini a gidagidan sa) (haqiqa budurwa kamar xan itaciya take, idan ya nuna ba a tsinke shi ba, rana zata vata shi, iska ta sheqar da shi) ('yan mata idan abinda ke riskar mata ya riske su, basu da wani magani banda aure, idan ba haka ba kuwa, to babu aminci a kan su na vaci sabida mutane ne)
Musulumci na xaukar gwaurantaka da qin aure, sababin hanya da faxawa varna, sabida haka musulumci ya qarfafa a bisa yin sa, ya kuma xauki yin sa a matsayin sharri da varna.
Manzon Rahama (SAW) na cewa : " duk wanda ke son tafarki na to ya so sunna ta daga cikin sunna ta shine aure"

KALLO
Kallon namiji ga mace da kallon mace ga namiji, yana sanya zuciyar xayan su ta karkata ga xaya, sau da yawa kallo shine farkon hanyar qulla alaqa tsakanin masoya, wani lokacin kuma kallo shin hanyar tada fitinaga namiji da mace, musamman idan kallon ya kasance ba qaqqautawa shi yake sa dogon tunani da bincike a kan abinda ido ya gani, daga nan sa zuciya da rai karkata zuwa abinda ya gani.
Haqiqa mummunan kallo na tayar da sha'awa, ta yadda tasirin sa zai iya tayar da sha'awa da qoqarin kawar da ita ta kowace hanya.
Manzon Rahama (SAW) ya ce : "kada ku yi kallon da ke bin kallo, haqiqa  baka da kallo , ... idan ba kallo xaya ba"
Daga Imama Sadiq (AS) : " kallon farko naka ne, na biyu kuma a kan ka yake (ba naka bane) na uku kuma cikin sa akwai halaka".
Imama Sadiq (AS) : "kallo bayan kallo na shuka sha'awa a zuciya"  saboda kashe wutar shaawa da kariya bisa fitina, tsarin musulunci ya hana mummunan kallo ya kuma yin kira zuwa runtse gani a bisa muharrami ya hana bayyanar da ado da sassan jiki da za su iya tayar da fitina voyayyu.
(ka cewa muminai maza su runtse ganin kuma su kame farjin su, ka kuma cewa muminai mata su runte ganin su da al'aurorun su, kada su dinga bayyanar ga kwalliyar su sai ga mazajen su).
Haqiqa qurani ma girma ya umarci muminai da su dinga kame ganin su, kada su yi kallo zuwa matar da ya halatta su aure ta, haka ma ya umarci mata da irin wannan abin da ya umar ci maza da shi, ya kuma uamrci mace ta voye ganin ta, ta hanyar rufe jikin ta gaba xayan sa matuqar zai tayar da sha'awar namiji misal : qafar ta jiknin ta da da gashin ta har ma da quwawun ta, savanin mae da waxannan abubuwan , basu cika tayar mata da sha'awsa ba, duk da haka an hana namiji bayyanar da wani abu da zai iya tayar wa da mace sha'awa.
Haka kallon fuskar matar da ake fuskanta, idan har da wata manufa an hana, amma idan ba manufar komai babu laifi, haka ma a halin larura, ya halatta namiji ya kalli jikin mace ita ma ta kalli nasa, kamar wajan aikin likita idan ya zama babu yadda za a yi tilas sai namiji likita ya kalli jikin macen babu yadda za a yi, amman idan da yadda za a yi bai halatta ba.
Maufar hana kallo shone hana tashin shaawa, saboda haka kowane irn launin kallo da ke tayar da shaawa da kwaxayi bai halatta ba.
Koda kuwa kallon hoto mai motsi ne da mara motsi, kamar kallon fina-finai da hotuna masu tsirara, wannan duk bai halatta ba sabida zai iya tayar da shaawa.
Tarihi na bayyana mana qisso shin waliyyan Allah, waxanda suka fi qarfin kwaxayin su da jin daxin su, da shaawar su, suka rayu rayuwa ta ladabi da xaukaka, da jin daxin ruhi, wanda zuciyar su bata samu damar da su yin mummunan kallo ba, daga cikin irin qissoshin akwai wannan, ....
Akwai wani mutum sunan sa  Dauda Abudullahi, shi xalibin wani mutum ne, ya je wajan wani daga cikin abokan sa, sai mutumin ya sauke shi a gidan sa, mutumin yana da mata 'Zarka'a' matar kuma kyakykyawa ce, sai mai gidan bayan ya sauke baqo a gidan sa ya fita neman buqatun sa na yau da kullum ya kuma gaya matar sa a kan cewa ta kula masa da baqo, har sai ya dawo, ta kula sasai wajan yi masa hidima, yayin da ya dawo gida sai ya cewa Duda Zarka'a ta kula da kai kuwa? Sai Dauda ya ce ban san ta ba Zarqa'a ko Kahla'a , sai mai gidan ya kira matar ta sa ya ce ban yi miki wasiyya da ki kula da wannan baqon ba!? Sai ta ce ka yi min wasiyya mana wasiyya da makaho, wallahi ba tava xaga kan sa ya kalleni ba.
Haqiqa idan mutum ya kare kansa daga kallo mummuna, da rashin kallon guraren da zasu tayar masa da hankali, zai zama mai iko kan zuciyar sa da shaawar sa da kwaxayin sa sai ya zama kammalalle mai qarfin nufi da tataccen ruhi, kallon guraren tayae da fitina shine matakin kaucewa da qulla mummunar alaqa tsakanin mace da namiji.
Manzon Rahama (SAW) na cewa : " zidar idanuwa itace kallo"
Xan Abbas ya faxa cikin tafsirin sa cewa : da namiji zai kasance a cikin tafiyar sa, sai ya gamu da mace, to ya rintse idon sa sai idan ya ga zai vata sannan ya kalle ta, idan kuma ya ji tsoron zai fitinu da ita to ya kame ganin sa.
Imama Sadiq (AS) : "kallo kibiya ce daga kibiyoyi shaixan ".

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: