bayyinaat

Published time: 09 ,September ,2018      21:24:31
Lambar Labari: 223
SHA'AWA
Shaawa ta kasu kashi-kashi a kan xan Adam, amman shaawar jinsi ta fi, itace tsakanin mace da namiji, ita wannan shaawar itace tushe wajan qulla alaqa tsakanin namiji da mace, sai dai alaqar zata iya zama mummuna ko kyakyawa.
Shaawa a wajan malaman xabi'a tana tare da mutum ne tun lokacin da aka haife shi, tana kuma girma tare da girman sa, sannan ta bayyana a hankali a hankali, har zuwa kaiwar sa matsayin balaga, a lokacin ne tasirin ta zai bayyyana a jikin sa.
Shaawa wata aba ce wadda dole mutum ya shayar da ita, kuma ya kjawar da ita, abin tambaya a nan shine, ta wace hanya za a shayar da ita? Bayan bincike mai zurfi an gano hanyoyi uku waxanda za a  iya amfani da suwajan kawar da ita.
1-    Ta hanyara adanne shaawa, wannan hanya ta kasu gida uku kamar haka,
a-    Wa'azi da faxakarwa, ana danne sha'awa ta hanyar wa'azantarwa da faxakarwa, wannan na samuwa ne sakamakon wa'azi da faxakarwa da za'a yiwa matasa ko wasun su a kan kamewa da danne shaawa.
Idan suka wa'azantu ko suka faxakantu, saika ga suna da qarfin iko kan danne shaawar su, saboda haka yiwa matasa nasiha a kan danne shaawa yana da muhimmanci sosai, sadai wannan hanyar bata fiya wadatarwa ba kan shayar da shaawa.
b-    Sai hanyar tsarewa da hana fita, da barazana tare da tsoratarwa a kan shayar da shaawar, wannan hanya itace ake yiwa matasa xaurin talala da ita, inda ake hana su fita tare da cuxanya da wasu, ana yi musu barazana a kan shayar da shaawar su, a gaskiya wannan hanya ita ma tana da rauni sosai, domin ta na sa matasan yin amfani da wasu hanyoyin don ganin sun shayar da shaaawar su, kamar yin amfani da wasu abubuwan irin su istimna'i (wasa da al'aura , ko wani abu domin biyan buqata).
Idan mace ce kuma, ta ke wasa da mace 'yar uwar tako wasu abubuwan kamar: roba, xan yatsa ko wasu abubuwan makamantan waxannan, har ta kawar da shaawar ta, waxannan abubuwan na jawo mtsala ga matasan mata da maza, don suna tare da illoli, kamar sanya raunin jiki da gavovi, kuma suna bin mutum har zuwa bayan ya/ta yi aure don basa gamsuwa ko su sa gamsarwa tare da wadatuwa dole sai sun yi amfani da wannan hanyar da suka saba, domin ta lalata musu xabi'a, da fatan Allah ya kare mu baki xaya.
c-    Akwai wata hanya da matasan da aka tsare ke bi don biyan buqatar su, hanyar shan kwayoyin magani don biyan buqatar su, wanna hanyar tana da munin gaske, tana kuma da illa ga lafiya da jikin mutum.

2-    Hanya ta biyu itace mafi munin hanya wajan shayar da shaawa, daga cikin hanyoyin sune hanyoyin fasiqanci kamar : zina, tsakanin namiji da mace ake yin ta, ita haramun cea qashin kanta, sannan tana da illoli ga mai yinta a kan sa da cikin mutane.
Zina na karya tushen iyali ta yadda zai zama babu tsatso ingantacce, tana yaxa cututtuka da vata tarbiyya da rashin mutunci, da sauran miyagun abubuwan da ina ke haifarwa.
Sannan maxigo da luwaxi, su waxannan munin su yafi yawa a kan na zina, domin luwaxi da maxigo na yanke zuria, kuma ya yaxa al'fasha cikin al'umma.

3-    Sai hanya ta uku itace hanyar da musulunci ya zava wato hanyar aure,  auren kuwa na dindindin ne ko na qayyadajjen lokaci (mutu'a), shia aure ya zama hanyar kawar da shaawa tare da kawar da varna cikin al'umma, domin da aure ne kawai za a iya gina iyali, a kare faxuwar zuria da lalacewa xabi'a, da kuma kange al'umma daga cututtukan zamani.
Saboda haka matasa su sani, aure shine hanya xaya tal da musulunci ya zavawa mutum wajan sayar da shaawar sa.


ZANCE DA YIM MAGANA TSAKANIN NAMIJI DA MACE
Tsarin musulunci ya sanya qa'idoji da ladubban yin magana tsakanin namiji da mace, a bayyane yake cewa xabi'ar mutum na kai shi ga yin magana da mace, ko mace ta yi magana da shi, a zahiri musulunci bai hana wannan bamuddun maganar babu fitina a cikin ta, irin wannan magana babu laifi.
Yanayin magana ko tattaunawa tsakanin mace da namiji, abu ne da ya yaxu lokacin saqon musulunci, sai dai a bisa tsarin tsarki da kamewa, hanyoyin da aka gina al'umma kammalalla maxaukakiya.
Manzon Rahama (SAW) ya kasance yana tattaunawa da mata, ya bayyana musu dokokin musulunci da ladubban sa, ya kuma amsa musu tambayoyin su, koda kuwa waxanda suka shafe su ne kai tsaye, kamar hukuncin haila da sauran su.
Mae kan iya tsayar da shi a kan hanya kamar yadda maza ke yi, ta tambaye shi abinda ya dame ta, na hukunce-hukuncen shari'a.
Sahabbai sun kasance suna tambayar matan Manzon Rahama (SAW) abinda suke buqata na ilimin addini, su kuma suna gaggawa wajan amsa tambayoyin da suka shafi hukunce-hukunce, da sauran abinda ya shafi rayuwar duniya.
Tarihi ya bayyanar mana cewa : wata mata ta je wajan Manzon Rahama (SAW) a kan tana son ya aure ta kuma wata ta je tana son ya aurar da ita wajan wani sahabin sa.
Wasu matan kuma, sun yi magana cikin masallacin Manzon Rahama (SAW) wanda wasu manyan sahabbai suka halatta.
Zainab 'yar gidan shugaban muminai Ali (AS) ta yi huxuba cikin masallacin kufa, da gidan sarki da gidan hukuma (asham), bayan shahadar xan uwan ta Imam Hussain (AS).
Mace da namiji daidai suke, wajan horo da kyakykyawa da hani da mummuna, wanda hakan baya yi yuwa sai hangarwa da nunawa zuwa ga abinda ake umarni zuwa gare shi bisa nasihar musulunci, ya yi kira da yin kykyawar magana, a cikin kowane zance. Domin tsarin musulunci bai kange mace ba, tare da hana ta ta'ta gudun mawar wajan gina al'umma, kai musulunci ya ma yi kira ne zuwa haxa hannu tsakanin namiji da mace wajan yin waxannan aiyyukan, saboda haka musulunci bai hana zance da tattaunawa tsakanin namiji da mace ba, muddun za a yi maganar a kan ladabi da kamewa.
Inda aka hana zance ko magana shine inda idan aka yi zai tayar da fitina da shaawa.  Duk zance ko magana mummuna, ka aka voye wata niyya mummuna a cikin ta, haram ne a yi wannan.
Dangane da amsar mace ga wanda ya yi mata magana ya danganta ga yadda ya yi mata  naganar, a bayyane ya yi mata ko ba'a bayyane ba, amman tsarin musulunci ya hana mace ta yiwa namiji magana mai jiyar da daxi, ta yadda zata iya tayar masa da shaawa, shima an haranta masa jin muryar wacce zata tayar masa da shaawa, koda kuwa waqoqi ne masu tayar da shaawa, haka nan an hana zolaya a cikin zance ko magana, tsakanin mace da namiji.
An rawaito daga abi Bashir ya ce : 'na kasance ina koyawa wata mata karatun al'qurani, sai na zolayeta da wasu kalmomi, da naje wajan Abi Ja'afar Imam Baqir (AS), me ka gaya mata? To kada ka sake.1
A taqaice dai zance ba haram bane tsakanin namiji da mace a tsarin musulunci, sai da zancen ya zamo mai amfani wanda babu varna a cikin sa.
Amma zancen da ya zama a cikin sa babu wani amfani, kuma babu varna kamar dai hira kan al'amuran duniya, a haqiqanin sa ba haram bane, saida hakan bai inganta ba a tsarin musulunci, kuma bai qarfafa shi ba, domin wani lokacin wannan kan zamo abinda ya gina varna.
Manzon Rahama (SAW) ya ce : 'mazauna uku na kashe zuciya, zama tare da mu'amala, zamatare da mata da zama tare da masu dukiya"2
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: