bayyinaat

Published time: 09 ,September ,2018      21:46:44
Wannan tambaya ce da ilimi ke yi wa kansa a yau, kuma ya tsaya kai da fata wajen bada amsa kuma bai gushe ba sai da ya bada sama amsa da xaya a bisa asasin matakin ilimi.
Lambar Labari: 225
Amma yiwuwa ta ilimi, a yau a ilimance ba a samu wani da ya kafa xalili ya kuma fayyace kore yiwuwar hakan ta vangaren nazari ba   . Kuma wannan binceke ne wanda a haqiqa yana da alaqa da yadda aka fassara yadda haqiqar saqar manyanta da tsufa suke a wajen Xan’adam, shin wannan lamarin yana yin bayanin wata doka ta xabi’a da ta tilasta saqar jikin Xan’adam da jijiyoyinsa - bayan sun kai mutuqa wajen nuna (manyantaka) - su rika bushewa a hankali a hankali har su wayi gari suna da qarancin ikon yin aiki wajen ci gaba da aiki har zuwa lokacin da zasu dena aiki baki xaya, ko da kuwa mun raba ta daga tasirin ko wani irin abu da ko wane irin dalili daga wajen jiki? Ko kuma wannan bushewar da cin karon da ke cikin tanadin sakar jiki da jijiyoyinsa wajen yin ayyuka a cikin sa, yana kasancewa ne sakamakon tashi-faxi da abubuwan da ke wajen jiki na daka kwayoyin cutuka ko guba da suke shiga cikin jiki ta hanyar abin da mutum yake ci na daga abinci mai maiko ko wani abu daban?.
Wannan tambaya ce da ilimi ke yi wa kansa a yau, kuma ya tsaya kai da fata wajen bada amsa kuma bai gushe ba sai da ya bada sama amsa da xaya a bisa asasin matakin ilimi.
Idan kuma muka xauki bangaren mahangar ilimin da ta fassara manyanta da raunin tsufa ta siffanta shi da cewa hakan na faruwa a sakamakon tashi faxi da gogayyar da jiki yake yi tare da wasu ayyanannun abubuwan da ke waje, a nazarce ke nan wannan yana nufin cewa idan muka raba saqar jikin mutum, wacce ita ke samar da jikin mutum daga ainihin waxannan abubuwan da suke da tasiri (wajen sa mutum ya tsufa) to lalle rayuwar mutum zata yi tsaho ta wuce matakin tsufa daga baya sai ta yi galaba a kansa daga qarshe.
Idan kuma muka yi riqo da xaya mahangar da ta karkata kan cewa tsufa doka ce ta xabi’a ga tsarin kwayoyin da garkuwar jiki shi a kan kansa, da ma’anar cewa haqiqa shi jiki a cikin hanjinsa yana xauke da kwayar da zata kawo qarshensa ba makawa, bisa shuxewa daga marhalar girma da tsufa tare da tuqewa zuwa ga mutuwa.     
Nake cewa: idan muka yi duba zuwa wannan mahangar wannan ba ya nufin rashin yiyuwar qaddara kowane irin sauyi a wannan doka ta xabi’a, balle ma a bisa tsammanin samuwar ta - doka ce mai chanja wa; domin a cikin rayuwarmu ta yau da kullum muna samu, kuma saboda malamai a xakin gwaje-gwajensu na ilimi suna ganin cewa haqiqa tsufa a matsayinsa na tsarin jikin Xan’adam ba shi da lokaci ta yiyu ya zo wa mutum da wuri, kuma ta yiyu ya yi jinkirin zuwa ya qi kuma bayana sai bayan tsahon wai lokaci, har yakan zama cewa mutum ya yi shekaru masu yawa amma yana da xanyantakar gabban jiki, kuma alamun manyantaka ba su bayyana a jikinsa ba, kamar yadda likitoci suka bayyana haka   . Ballantana ma haqiqa malamai, a aikace sun iya yin amfani da yanayin yadda wannan dokar da xabi’ar da muke magana kanta take canajawa, sai suka tsawaita rayuwar wasu daga cikin dabbobi sau xaruruwan ninki idan ka kwatanta da rayuwar ta ta asali; kuma sun yi wannan ne ta hanyar halittar yanayoyi da abubuwan da suka temaka wajen jinkirta mothin dokokin tsufa.
Da wannan ya tabbata a ilimance cewa lalle jinkirta ko tsawaita wannan dokar ta hanyar samar da yanayi da sababai na musamman lamari ne mai yiyuwa, kuma idan har ilimi bai iya jinkirta wannan ga wasu daga cikin halittu ba kamar mutum, to wannan be kasance ba face sai don bambanci daraja ko mataki da ke tsakanin wahalar gudanar da wannan lamarin kan Xan’adam, da kuma wahalar yin hakan danagane da sauaran halittu. Kuma wannan na nufi cewa lalle ilimi ta nahiyar nazari da mahanga bisa gwargwadon abin da mafuskantarsa (hasashensa) mai motsi (ta nan gaba) take bayyanawa, kwata - kwata a wajensa ba abin da ke nuna rashin yiwuwar tsawaita rayuwar Xan’adam, daidai ne mun fassara tsufa da ma’anar tashi-faxi ga cakuxexeniyar da ke yin tasisi a cikin jiki daga waje ko kuma yana kasancewa ne sakamokon doka ta xabi’a da ke xamfare da kwayoyi rayuwar ko halittar jiki wacce take shimfixa wa jiki hanya zuwa mutuwa da qarewa.
Kuma daga wannan zamu raiarayo cewa haqiqa tsawon rayuwa gun Xan’adam da wanzuwarsa qarnoni masu yawa abu ne mai yiwuwa a hankalce kuma mai yiwuwa ne a ilimance, sai dai har yanzu be gushe ba (yana cikin abin da) be yiwuwu a ilimance ba, sai dai hasashen ilimi na tunkarar hanyar tabbatar wannan abu mai yiwuwa a kan doguwar hanya ta tabbatawa a aikace.
Bisa wannan hasken (da bayanin da ya gabata), zamu xauki rayuwar Imam Mahdi (a.s) da abin da ke kewaye da ita na daga tambayoyi da neman qarin bayani, sannan kuma mu yi hasashe kan cewa:
Bayan tabbatar yuwuwar yin rayuwa mai tsawo a hankalce da ilimance kuma ya tabbata cewa ilimi na tunkarar hanyarsa ta chanja wannan yiyuwar ta mahanga zuwa yiyuwa ta aiwatarwa (a aikace) a hankali a hankali ba wata ma’ana ta yin mamaki da zasu yi saura in banda (yin mamaki kan cewa) Imam Mahdi (a.s) ya rigayi shi kansa ilimin. (wato tun kafin ilimi ya ma fara tunanin yiyuwar haka balle ya kai ga gano shi a nazari har zuwa zartar da shi a aikace ta hanyar gwada shi a kan wasu dabbobi, tuni hakan ya wakana a cikin rayuwar Imam Mahdi (a.s) a aikace), sai ya zama abin da ke yiyuwa a nazarce ya zamo mai yiyuwa a aikace a cikin shi kansa Imam Mahdi (a.s) tun kafin ilimi a cikin ci gabansa ya kai matsayin iya yin wannan canjin a aikace, ya zama kamar wanda ya rigayi ilimi wajen gano maganin meningitis  ( cutar da ke kama fata wacce ta ke kaiwa cutar ta kai ga kwakwalwa a sakamakon virus ko kumburi ) ko maganin ciwon daji.   

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA    
Mail= munirsaid92@gmail.com
Whatsapp da telegram +2348038557822.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: