bayyinaat

Published time: 09 ,September ,2018      21:53:44
Idan har mun yi imani da dukkanin waxannan to don me zamu riqa ganin cewa abu ne mai wuya wanda ya aiko waxannan saqonnin na Manzonci - tsarki ya tabbata a gare shi - a ce ya rigayi imini wajen tsarawa da zartar da shekarun Imam Mahdi (a.s),
Lambar Labari: 226
To idan kuma mas’alar ta kasance ita ce cewa ta yaya aka yi musulunci - wanda ya tsara rayuwar wannan shugaba  da ake sauraro (a.s) - ya zama ya rigayi motsin ilimi a fagen chajawa?
Amsa ita ce: Ba a nan ne kaxai musulunci ya rigayi motsin ilimi ba.
Ashe shari’ara musulunci a dunqule ba ta rigayi motsin ilimi da ci gaban xabi’a na tunanin Xan’adam da qarnoni masu yawa ba?   .
Ashe ba ta yi kira da muryar aza harsashin xabbaqawar da Xan’adam be kai ga cin musu a motsinsa na ci gaba, sai bayan xaruruwan shekaru ba?  
Ashe ba ta zo da shar’o’in da suke cike da hakimar da Xan’adam be iya riskar surrikanta kume be iya fuskar hikimar da ke cikinsu ba har sai bayan wani xan taqi na zamani ba? Ashe saqon sama be yaye sirrika samuwar da ba su tava xarsuwa a zukatan mutane ba, sannan kuma ilimi ya zo yana tabbadar da su yana qarfafafarau ba?   
Idan har mun yi imani da dukkanin waxannan to don me zamu riqa ganin cewa abu ne mai wuya wanda ya aiko waxannan saqonnin na Manzonci - tsarki ya tabbata a gare shi - a ce ya rigayi imini wajen tsarawa da zartar da shekarun Imam Mahdi (a.s),   alhali a ana ban yi magan kan komai ba sai kan lamarin gabata wanda mu kan mu kai tsaye zamu iya riskarsa?  Kuma zamu iya qaro wasu tabbatattun abubuwa da suka gabata waxanda shi da kansa sakon da ya zo daga sama ne yake ba mu labarinsu. (a nan Karin Magana ce marubucin ya yi, Ma’ana waxanda muke samun labarinsu a cikin saqon day a zo daga sama).
Misalin haka: Sama ta bada labarin cewa an yi tafiya da Annabi Muhammadu (s.a.w) da daddare daga masallacin Harami zuwa masallacin Aqsa, kuma wannan tafiyar daren   idan muka so mu fahimce ta a qarqashin gewayen dokokin xabi’a, tabbas bisa haqiqa yana bada labari ne ta hanyar yin amfani da dokokin na xabi’a, bisa yanayin da ba a bawa ilimi  damar ya yi bincike da tahqiqi   a kanta ba, sai bayan xarururwan shekaru, to ainihin wannan kwarewar ta ubangiji da ta bawa Manzon Allah (s.a.w) damar motsawa cikin sauri tun kafin a bawa ilimi wannan damar, ita ce wacce ta bawa na qarshen halifofin da a ka yi nassi da su wannan doguwar rayuwa kafin a bawa ilimi damar yin tahqiqi a kan hakan.   
Na’am, wannan rayuwa mai tsawo da Allah Ta'ala ya bawa mai ceto sha sauraro, da alama abin ban mamaki ne bisa iyakon abin da aka saba a rayuwar mutane, har zuwa yau xin nan, haka ma (akwai ban mamaki a cikin) abin da aka cimma zuwa yanzu ta hanaya gogayyar malamai.
Sai dai, ashe a ce wannan rawar ta musamman da aka tanade ta saboda shi waccce ita ake so wannan mai ceton ya taka, shin ita ma (wannan rawar ta kasance ne) bisa iyakoki da dokokin da mutane suka saba da su a rayuwarsu take, (kuma ta yi kama) da irin abubuwan da suka faru da su a tsawon tarihi?
Ashe ba a jingina masa aikin kawo canji a duniya ba da sake gina ta bisa ci gaba bisa asasin gaskiya da adalci ba?
To don me zamu yi mamaki idan share hanyar zuwan wannan lokacin taka wannan babbar rawa ya siffatu da wasu abubuwa na ban mamaki waxanda suka savawa abin da aka saba kamar tsawon rayuwa mai ceto, sha sauraro? Haqiqa bakuntar (wato ban mamakin) waxannan lamurran da fitar su daga zagayen abin da aka saba duk yanda ya kai, ba yadda za a yi su wuce baquntar (ban mamakin) wannan rawar mai girma wacce ya wajaba ga wanda aka yi alqawwarin zuwansa ya taka!. Idan mun kasance mun yarda da yiyuwar wannan rawar tilo, wato wannan aikin da babu irinsa   a tsawon tarihi, tare da cewa babu wata rawa irin ta a tarihi xan’adam, to don me ya sa ba zamu yarda da yiyuwar wannan rayuuwa mai tsawo ba wacce ba mu sami wata rayuwa mai tsawo makamancinta a irin yadda muka saba rayuwa ba? Kuma ban sani ba shin wannan ya kafu ne bisa sudufa (katsaham) ta yanda zai zama an sami wasu mutane guda biyu waxanda su su kaxai ne zasu zazzage varnan da ke cikin tsarin rayuwar xan’adam su sake gina ta daga farko, sai ya zama ko wanne daga cikinsu ya rayu rayuwa mai tsawon da ta wuce tsawon kwanakin rayuwarmu irin wacce muka saba ninkin ba ninki?
Na farkon su: ya taka tasa rawar a farkon zamani da xan adam ya rayu, wanda shi ne Annabni Nuhu (a.s), wanda qur’ani ya bada labarin sa,   cewa ya zauna cikin mutanen sa shekara gudu ba hamsin, kuma aka ba shi ikon sake gina wata sabuwar duniya daga farko.
ZA MU CI GABA IN SHA’Allah Ta'ala:-

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA    
Mail= munirsaid92@gmail.com
Whatsapp da telegram +2348038557822.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: