bayyinaat

Published time: 10 ,September ,2018      02:01:17
To don me ya sa zamu yarda da labarin annabi Nuhu wanda ya kusa shekara dubu a qalla, amma ba za mu yarda da na Imam Mahdi (a.s) ba?
Lambar Labari: 227
Na biyunsu kuma: da sannu zai yi na sa aikin nan gaba kuma shi ne Mahdi (a.s) wanda zuwa yanzu ya zauna cikin mutanensa sama da shekara dubu kuma idan ranar da aka yi masa alkawar ta cika da sannau za a ba shi dama da ya kuma yi wa duniya sabon gini fil.
To don me ya sa zamu yarda da labarin annabi Nuhu wanda ya kusa shekara dubu a qalla, amma ba za mu yarda da na Imam Mahdi (a.s) ba?  
Kuma zuwa yanzu mun rigaya mun san cewa: lalle rayuwa mai tsaho mai yiwuwa ce a ilimance, sai dai idan muka qaddara cewa ba abu ne mai miyuwa ba, kuma dokar tsufa da girma ba zai tava yiyuwa ga xan’adam din yau, kuma ba zai yiwu ma ga ci gaban da yake samu ya yi galaba kan dokar tsufa ba, haka ma canjawar yanayinsa da sharuddansa, to me hakan yake nufi? Wannan na nufin cewa tsawon kwanakin mutum kamar - Nuhu ko Mahdi (a.s) - har qarnoni masu yawa, ya kasance rayuwa ce wacce take bisa savanin dokokin xabi’ar da ilimi ya  tabbatar da ita, ta hanyar gwaji, da karantar abubuwa a zamanance, da wannan zai zama cewa wannan mu’ujizar ta vata dokar xabi’a a wani yanayi ayyananne, don kare rayuwar mutum, wanda aka xorawa kare saqon sama kuma wannan mu’ujizar ba tilo ba ce a ire-irenta, ko kuma ba abin mamaki ba ne a wajen aqidar musulmin da wance ta samo asali daga qur’ani da sunna,   dokar tsufa da manyantaka ba ta fi qarfin dokar nason da zafi yake xauka daga wani jiki zuwa wani jikin da be kai shi zafi har su daidaita a - zafi - ba, sai ga shi Allah Ta'ala ya tashi dokar daga aiki don ya kare rayuwar Annabi Ibrahim (a.s) a yayayin da ya zama kaxai hanyar da ta rage wajen kare rayuwar Annabi Ibrahim (a.s) ita ce ta hanyar vata wannan dokar, don haka sai aka ce da wuta a yayin da aka wurga shi a ciki, {sai muka ce ya ke wuta ki kasaance sanyi da aminci ga Annabi Ibrahim (a.s)}   sai ya fita daga cikinta kamar yadda ya shiga da qoshin lafiya ba wata ba abin da ya same shi, qari a kan cewa akwai da yawa daga cikin dokokin xabi’a da aka vata aikinsu don kare rayuwar wasu mutane daga Annabawa da Hujjujin Allah Ta'ala a bayan qasa, an tsaga tafki ga Annabi musa (a.s),  kuma an kamantawa rumawa cewa Annabi isa (a.s)  suka kama alhali ba shi suka kama ba, kuma Annabi Muhammadu (s.a.w), ya fita daga gidansa alhali yana kewaye da dakarun quraishawa waxanda suka shafe awannai suna dakonsa don su kai masa farmaki, sai Allah Ta'ala ya suturta shi daga idanuwansu a lokacin da yake tafiya tsakatsakinsu .    dukkanin waxannan yanayoyin misali ne na dokokin xabi’ar da aka karya domiin kare rayuwar mutum, hikimar Allah Ta'ala ta zartar da a kare ruyuwarsa, kenan me zai hana dokar tsufa ita ma ta kasance daga cikin waxannan dokokin.
Kuma ta yiyu mu iya fita daga wannan da gamammiyar fahimta, shi ne cewa duk lokacin da kiyaye rayuwar hujjar Allah Ta'ala a bayan kasa ta dogara kan karya dokar xabi’a kuma ci gaban rayuwarsa ya zama larura domin zartar da abin da aka sa shi, sai ikon Ubangiji ya yi aikinsa wajen karya dokar xabi’a domin ya sami damar isar da abin da aka xora masa, haka ma akasin haka, idan bawan Allah Ta'ala ya gama aikin da ya hau kansa, wanda Ubangiji ya xora masa, tabbas da sannu zai gamu da ajalinsa ya rasu ko ya yi shahada, daidai da yadda dokoki xabi’a suke.
Kuma a al’adance dangane da wannan fahimtar da ta game zamu iya fuskanta tambaya mai zuwa: ta yaya za a iya karya dokar xabi’a?   kuma ta yaya za iya raba alaqar larura wacce xabi’a ta tsayu a akai? Shin wannan ba kishiyantar ilimi ba ne wanda ya gano Wannan dokar ta xabi’a kuma ya iyakance waxannan alakokin na ba makawa bisa asasin gwaji da bin diddigi?
Amsa: Tabbas shi kansa ilimi ya bada amasar wannan tambayar ta hanyar sassautowa da yin qasa-qasa da ya yi daga mahangar tilasaci a dokar xabi’a, bayanin haka:- haqiqa ilimi ne ya ke gano dokokin xabi’a bisa asasin gwaji da bin diddigi, a yayin da ya kore faruwar wani abu na xabi’a a daidai faruwar wani abu to wannan abin da ya faru yana yin nuni kan doka ta xani’a, wacce ita ce duk lokacin da abu kaza na farko ya faru to abu kaza na biyu ma zai faru bayansa, duk da cewa shi ilimi a irin wannan doka ta xabi’a ba ya qaddara samuwar alaqa ta xabi’a tsakanin abubuwan guda biyu irin alaqar da ta samo asali daga ainihin abu na farko da ainihin na biyun, domin ba makawar da ke tsakaninsu ko a ce domin (larurur da ke tsakaninsu) yanayi ne na gaibu wanda ba za a iya gano ta ta hanyar gwaji da bin diddigin ilimi ba, don haka ma haqiqa yaren ilimin zamani, yana qarfafa cewa haqiqa dokar xabi’a - kamar yanda ilimi ya bayyana ta - ba ta magana kan doka ta larura (ta ba makawa), balle ma yana magana ne kan qaddarawa mai ci gaba, tsakanin abubuwa biyu,   dan haka idan mu’ujiza ta zo ta shiga tsakanin waxannan abubuwan guda biyu ta rava su da juna hakan ba raba alaqa ta ba kamawa tsakanin abubuwa biyu ba ne.


MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA    
Mail= munirsaid92@gmail.com
Whatsapp da telegram +2348038557822.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: