bayyinaat

Published time: 10 ,September ,2018      02:06:51
Da wannan ne mu’ujiza ta wayi gari ana kallonta a matsayin yanayi na togaciya ga wannan salon na haxuwa ko bibiya ba tare da ta ci karo da wata larura ko ta kai mu ga abin da ba zai yiyu ba.
Lambar Labari: 228
Haqiqa, Tabbas ita mu’ujiza bisa yadda aka fahimce ta a addinance ta wayi gari a cikin hasken harshen ilimin zamani ana fahimtar ta da daraja (a mataki) mafi girma fiye da yadda take a qarqashin inuwar mahangar ta ta musamman irin ta mutanen da zuwa ga alaqa ta sababi.
Haqiqa tsohuwar fuskar mahanga na ganin (na qaddara) cewa ko wanne daga abubuwan nan guda biyu samuwar xayan su na tabbatar da samuwar na biyun don haka alaqar dake tsakaninsu alaqa ce ta larura (ba makawa), larura kuma tana nufin ba zai tava yiyuwa xayansu ya rabu da xayan ba, sai dai wannan alaqar ta juye ta canja zani a mahangar ilimin yanzu ta zamo dokar gwamuwa ko bibiya na ko da yaushe   tsakanin abubun biyu, ba tare da qaddara wannan larurar ta gaibu ba.
Da wannan ne mu’ujiza ta wayi gari ana kallonta a matsayin yanayi na togaciya ga wannan salon na haxuwa ko bibiya ba tare da ta ci karo da wata larura ko ta kai mu ga abin da ba zai yiyu ba.
Amma bisa mahangar (usasul manxiqiyya lil istiqra’i) tushen hankalin bibiya,   mu mun yi ittafiqi da sabuwar mahangar ilimi cewa shi bin diddgi, ba ya kafa hujja kan alaqar larura tsakanin bayyanannun abubuwa guda biyu, sai dai muna ganin hakan na yin nuni kan samuwar wata fassara mai tarayyaya ba da ma’anar ci gaban maimatuwar gwamayya ko bibiya tsakanin abubun biyu ba, kuma wannan fassarar ta gamayya kamar yadda tushen ta ke yin nuni kan yiyuwar tsayuwar ta kan asasin larura (ba makawa), haka ma zai iya xankar ma’anar tsayuwarsa bisa asasin kaddara wata hikima da ta sa wanda ya tsara Duniya ya alaqanta zahirin abubuwa kaza da na waxancen abubuwan kaza tare da ci gaban (maimatuwar hakan). Kuma ita kanta wannan hikimar a wani lokaci ana kiranta da togaciya, sai mu’ujiza   ta afku.
Da wannan ya bayyana a mahangar ilimin manxiq yana mai kafa hujja cewa rayuwa mai tsawo abu ne mai yiyuwa, kuma ba wani dalili na ilimi da yake kore yiyuwarsa haka ma ba wata hujja ta falsafa da take kore shi. Kuma da wannan ne marhalar bincike ta farko kan abin da ya shafi gaibu ta zo qarshe.

Ta biyu:- marahalar tabbatar da tabbatuwar hakan a aikace dangane da Imam Mahdi (a.s)
 
Kuma bincike a wannan marhalar zai kasance ta hanya biyu:
1-    Ta hanyar aqida. 2- Ta hanyar tarihi
Ta Xaya:- HANYAR AQIDA:  
Tabbatar da ita zai yiwu da bayanai guda uku:
(a)    Haqiqa wannan kevantar na suna daga cikin abubuwa na ba kamawa wajen fahimtar Mahdi (a.s) a wajen Ahlulbait, domin tabbatar wannan fahimtar - kamar yadda ya gabata - lamari ne da yake xauke da tabbatacen dalili, yankanke, kuma hakan na bayyana vacin waninsa, kuma a xabi’ance wannan yana kai mu zuwa ga qudurcewa da fakuwar limami na goma sha biyu. Kuma muddin limamai goma sha biyu ne kaxai, sannan ayyanannu ne a wajen Allah Maxaukaki, haka kuma - ya tabbata cewa - ba gudummawar mtuane a cikin zavinsu, to ba wani abu a kanmu face qudurce ci gaban rayuwar limami na sha biyu da tabbatar rayuwarsa sa a kamar sauran ‘yan’adam da kuma cewa zai bayyana bayan haka a zagaye na qarshe daga rayuwar mutane, sannan a xabi’ance baya yiwuwa ga mutumin da ake qaddara masa irin wannan hadafin, ake kuma qaddara masa wannan doguwar rayuwar, ya zamana ya yi ta a bayyane!, ba makawa sai dai ya yi ta a voye, yana mai vuya da fakuwa daga idanuwa, sai dai idan da za a qaddara rasuwar Imam Mahdi a tsawon lokaci na xabi’a kamar sauran mutane, sannan kuma ya dawo duniya ya sake wata sabuwar rayuwa a lokacin da zai bayyana, illa iyaka kuma haqiqa qaddara faruwar hakan na lazimta yankewar hujja a wani lokaci mai rabewa daga mutuwarsa zuwa bayyanarsa. Kuma wannan ya savawa Hadisin Saqlaini wanda ya yi nuni bisa lazimtar littafi da (Itra) Ahlulbaiti (a.s), da rashin rabuwarsu a cikin wani zamani daga zamuna har tashin qiyama da gangarawarsu zuwa tafkin - kausara -, kamar yadda hakan yake wajabta yin quduri da (raja’a) wato komen Imam Mahdi (a.s) zuwa rayuwa bayan mutuwarsa, alhali ba wanda ya faxi wannan daga cikin Musulmai.
(b)    Ruwayoyin da suka yi nuni bisa siffantuwar Imam Mahdi (a.s) da fakuwa, kuma haqiqa wasu daga cikin littattafan Sunan sun ambace su misalin: Yanabi’ul Mawadda da Fara’idus Simxain.
A cikin Yanabi’u daga littafin Fara’idus Sumxaini daga Baqir daga babansa daga kakansa daga Ali (AS) ya ce: Manzon Alalh (SAW) ya ce: " Mahdi daga ‘ya’yana yake, da sannu zai faku daga idanun mutane, idan kuma ya bayyana da sannu zai ciki qasa da daidaito da adalci kamar yadda aka cika ta da danniya da zalunci”.   
Kuma a cikinsa dai daga Fara’id an karvo daga Sa’idu xan Jubair daga xan Abbas Allah ya yarda da su ya ce: Manzon Allah (SAWW) ya ce: "Lallai Aliyu shi ne wanda na yi wa wasiyya, kuma daga ‘ya’yansa akwai tsayayye abin saurane Mahdi zai cika qasa da daidaito da adalci kamar yadda aka cika ta da qeta da zalunci, na rantse da wanda ya aiko ni da gaskiya ina mai bushara da gargaxi lallai waxanda suka tabbata kan imani da imamancinsa a lokacin fakuwarsa su suka fi xaukaka fiye da jar wuta”, ma’ana wuta mai ci ganga-ganga”. Sai Jabir xan Abdullahi ya tashi zuwa gare shi, sai ya ce: Ya Manzon Allah, tsayayye daga ‘ya’yanka zai vuya? Ya ce: "Qwarai na rantse da Allah domin Allah ya tsamar da masu imani ya shafe kafirai”. Sannan ya ce: "Ya Jabir, lallai wannan wani lamari ne daga Allah kuma sirri ne daga Allah ahir ka yi kokwanto domin kokwanto a cikin almarin Allah mai girma da buwaya kafirci ne”.


MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA    
Mail= munirsaid92@gmail.com
Whatsapp da telegram +2348038557822.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: