bayyinaat

Published time: 10 ,September ,2018      02:11:35
A cikinsa dai, daga Ahmad xan Ziyad daga Da’abil xan Aliyyu Bakhuza’e a cikin labarin zuwansa wajen Imam Ridha (a.s) da kuma qasidarsa da ya rera mai (qafiayr) ta,
Lambar Labari: 229
Ya kuma zuwa a cikinsa a shafin da aka ambata daga Hasan xan Khalid ya ce: Aliyu xan Musa Rida ya ce: Haqiqa na huxu daga ‘ya’yana xan shugabar mata ne,  da shi Allah zai tsarkake qasa daga dukkan qeta da zalunci shi ne wanda mutane za su yi shakka a cikin haihuwarsa kuma shi ne ma’abocin fakuwa, to kuma idan ya bayyana qasa za ta haskaka da hasken Ubangijinta”.      
A cikinsa dai, daga Ahmad xan Ziyad daga Da’abil xan Aliyyu Bakhuza’e a cikin labarin zuwansa wajen Imam Ridha (a.s) da kuma qasidarsa da ya rera mai (qafiayr) ta, zuwa inda ya ce: "Imami a bayana (shi ne) xa na Muhammad bayansa xansa Aliyyu bayan Aliyyu sai xansa Hassan bayan Hasan sai xansa Hujja tsayayye kuma shi ne abin sauraro a cikin fakuwarsa kuma abin yi wa bayayya a lokacin bayyanarsa, zai cika qasa da adalci bayan ta cika da zalunci, amma yaushe zai tsaya? Wannan labari ne na lokaci, haqiqa babana ya bani labari daga iyayensa daga Manzon Allah (SAWW) ya ce: "Misalinsa kamar misalin alqiyama ce ba za ta zo muku ba sai katsahan”.   
An samo daga cikinsa dai daga littafin Gayatul Maram daga Jabir xan Abdullahi ya xaukaka shi: "Mahdi daga ‘ya’yana yake sunansa suna na alkunyarsa alkunyata, mafi kamar mutane da ni a halitta da xabi’a, fakuwa za ta kasance gare shi da ximuwar da al’umm za su vata a  cikin ta yana gabatowa kamar tuararo mai haske zai cika qasa da adalci kamar yadda aka cikata da zalunci”.
A cikinsa, daga fara’idul simxaini a shafin da aka ambata a cikin fara’idul simxaini a cikin sahifar da aka mabata daga Baqir (a.s) daga iyayensa daga Ali (a.s) ya yi rafa’in hadisin cewa: "Mahadi (a.s) daga cikin ‘ya’yana yake fakuwa zata kasance a gare shi da ximuwar da al’ummu zasu vace a cikinta - har zuwa inda ya ce - kuma zai cika duniya da adalci kamar yadda ta cika da danniya da zalunci”   
A cikin sa daga manaqib daga Abi Ja'afar Muhammad  xan Baqir (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w)  ya ce farin ciki ya tabbaata ga wanda ya riski tsayeyyen alayen gida na kuma yana mai yin koyi da shi a lokacin fakuwarsa kafin tsayawarsa kuma yana yin biyayya ga waliyensa kuma yana qin maqiyansa waxannan su ne abokai na ma’abota soyayya ta mafi karamcin al’umma ta ranar alqaiyama.
A cikinsa an karvo daga abi basir daga Sadiq Ja'afar xan Muhammad  daga iyayensa daga shugaban muminai ya ce Manzon Allah (s.a.w)  ya ce: "Mahdi (a.s) daga cikin ‘ya’yana yake sunansa irin nawa alkunyarsa ma irin tawa kuma shi ne mafi kamanceceniyar mutane da ni a halitta da halayya zai faku kuma mutane zasu shiga ruxani har sai mutane sun vata sun bar addininsu a wannan lokacin sai tauraro mai haske zai gabato ya cika duniya da adalci kamar yadda ta cika da zalunci da danniya”. A cikin littafin akwai irin wannan Hadisin, sai dai shi ya ce: "A sannan ne zai gabato kamar tauraro mai haske ya zo da ajiye-ajiyen Annabawa (AS)... ka karanta Hadisin.    
A cikinsa a shafi na 494 daga gare shi daga Jabir xan Yazid Baju’ufe ya ce: Na ji Jabir xan Abdullahil Ansari yana cewa: Manzon Allah ya ce da ni: "Ya Jabir lallai wasiyyaina kuma shugabannin Musulmi a bayana na farkonsu Aliyu ne sai Hassan, sai Husaini sai xansa Aliyu sannan Muhammad xan Ali wanda aka sani da Baqir da za ka riske shi kai Jabir, idan ka haxu da shi ka gaishe min da shi, sannan Ja’afar xan Muhammad sannan Musa xan Ja’afar sannan Aliyyu xan Musa sannan Muhammad xan Ali, sannan Aliyu xan Muhammad sannan Hasan xan Ali, sai tsayayye, sunansa sunana, alkunyarsa alkunyata xan Hasan xan Ali wanda Allah Maxaukaki zai buxe gabashi da yammacin qasa a hannunsa, shi ne wanda zai vuya ga barin masoyansa vuyan da ba mai tabbata a kan faxi da imamancinsa sai wanda Allah ya cika zuciyarsa da imani”.
(a)    Idan Mahdi (a.s) bai kasance Imami ma’asumi ba, ya kasance gamagarin mutum daga gamagarin Musulmi, to zai zama ba wata alaqa tsakaninsa da bayyanar Masihu (a.s) tare da shi, domin shi yana daga Ulul Azmi, balle ya qarfafa Mahdi (a.s) ya kira Kiristoci zuwa ga yin imani ga Annabcin Annabi (s.a.w). To ba makawa Imam Mahdi ya zamo ma’asumi, tun da shi Imamanci ba abu ne da yake karvar da’awa ba, abu ne da yake buqatar ayyanawa daga sama da nassin Annabi da zai bayyanata, kuma wannan bai gudana ga wasun imamai sha biyu ba, haqiqa wafatin Imaman da suka gabata tare da bunne jukkunansu a sanannun gurare abu ne da ya tabata, kuma imami na sha biyu ya yi saura ba a san mutuwarsa ba har yanzu. To ke nan ba makawa da yin quduri da ci gaban rayuwar wannan imamin daga haihuwarsa zuwa lokacin bayyanarsa a qarshe zamani, domin ya cancanci qarfafawar Annabi Isah gare shi.
Sharifi mai girma Sayyid sami Albadari yana faxa game da haka:
"Haqiqa bayyanar Isah za ta kasance tana da buqatuwa zuwa ga faffaxar masaniya da ilimi da jagoranci qarqashin Mahdi (a.s) bisa la’akari da cewa shi Annabi Isa (a.s) mai yin shaida ne gare shi kuma mai temakawa ne wajen isar da saqon da zai daga muryarsa da shi da littafinsa kuma mai yin biyayya ne a gare shi. Shi Mahdi (a.s) a bisa surantawar ‘yan Sunna ba shi da damar da zai iya mamaye Isa (a.s), (ma’ana ya zama a qarqashinsa) kai ba ma shi da damar da zai iya mamaye wasu daga qungiyoyin Musulmi.
Su - suna ganin - sam ba shi da ikon mamaye Isah, domin shi Isa Annabi ne Ma’asumi abin qarfafawa da Mu’ujizozi, misalinsa kuwa ba zai yiwa wani mutum ya xoru a kansa ba alhali ba a qarfafa shi da mu’ujizozi da isma da cikakken ilimi ba.
Ba zai kasance mai iko bisa xoruwa a kan dukkan Musulmi ba ba tare da qarfafawarw Ubangiji da mu’ujizozi da isma da kuma cikakken ilimi ba.      


MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA    
Mail= munirsaid92@gmail.com
Whatsapp da telegram +2348038557822.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: