bayyinaat

Published time: 10 ,September ,2018      02:23:39
Daga nan ne wasu daga manyan masana na sunna Imani da rayuwarsa da wanzuwarsa har ma ya dauwama a zantuttukansa. Haqiqa Sayyid Sadruddin ya ambaci wasunsu, ya ce: Daga cikinsu akakwai Sheikh Muhyiddin ibnul Arabi
Lambar Labari: 231
QISSA TA BIYU:  
Assayidul Baqi xan Udwa Al’alawi Alhasani ya hakaito min cewa; babansu Uxwahu bai yadda da samuwar Imam Muhammadul Mahdi ba, yana cewa; Idan ya zo ya warkar da ni daga wannan rashin lafiyar na gaskata zancen su? Yana maimaita wannan zancen to a wani lokaci mun taru a lokacin isha na qarshe, sai baban mu ya yi kururuwa sai muka zo masa cikin gaggawa sai ya ce: Ku riski Mahdi a yanzu ya fita daga wajena, sai muka fita ba mu ga kowa ba, sai muka dawo masa ya ce: Wani mutum ne ya shigo min ya ce: Ya Uxwa sai na ce: Labbaika, ya ce: Ni ne Mahdi (a.s) na zo gare ka ne don in warkar da cutarka, sannan ya miqa hannunsa mai albarka ya matsa saman cinyata ya tafi, sai ya fita sannan ya vace vat kai ka ce barewa, Aliyyu xan Isah ya ce: Na tambayi wani kan wannan qissar ba a wajen xansa ba, sai ya tabbatar min da ita.  
Daga nan ne wasu daga manyan masana na sunna Imani da rayuwarsa da wanzuwarsa har ma ya dauwama a zantuttukansa. Haqiqa Sayyid Sadruddin ya ambaci wasunsu, ya ce: Daga cikinsu akakwai Sheikh Muhyiddin ibnul Arabi a cikin Futuhat bisa riwayar sheikh Abdulwahhab Ash’arani a littafinsa Alyawaqit wal Jawahir wanda ya watsu sosai ya ciro shi daga littafin (Is’afur Ragibin), ba kuma na zaton zai yadda a jingina masa zaton wasu mtuane ba tare da ya tababtar ba.
Daga cikinsu akwai shi Shehu Abdulwahhab Assha’arani a littafinsa (Alyawaqit fil Jawahir) bisa abin da ke cikin Is’afur Ragibin a in da ya ce: Mahdi (a.s) da Imam Askari haihwuarsa ranar tsakiyar daga Sha’aban shekara ta 255 kuma yana nan a raye har sai ya haxu da Isa xan Maryam, haka Shehu Hasanun Iraqi ya ba ni labari dangane da Imam Mahdi (a.s) yayin da ya haxu da shi kuma Sayyid Aliyyul Khauwas ya dace da shi bisa haka.  
Daga cikin su akwai Shehu Abdullahi Muhammad xan Yusuf xan Muhammadul Kanji a littafinsa (Albayan fi Akhbari Sahibiz Zaman) bisa abin da Is’afur Ragibin ya naqalto, ya ce: Daga dalilai a kan cewar Mahdi na raye wanzajje bayan gaibarsa har zuwa yanzu, da kuma cewar ba abin da zai hana wanzuwarsa; wanzuwar isa xan Maryam, da Khidr, da Ilyas daga waliyyan Allah Maxaukaki, da kuma wanzuwawr Dujal mai ido xaya da Iblis la’ananne daga maqiyan Allah, waxannan wanzuwarsu ta tabbata a littafi da Sunnah.  
Daga cikinsu dai akwai: AL Shaikhul Ariful Fadilul Khojihu Muhammad Barisa a littafinsa (Faslul Khixab) bisa abin da ke cikin Yanabi’l Mawadda bayan ya ambaci haihuwar Mahdi da kuma cewar Allah Maxaukaki ya ba shi hikma da rarrabe zance tun yana qarami, kamar yadda ya yi baiwa ga Yahya da Isa ga wannan, ya ce: Kuma Allah Maxaukaki ya tsawaita rayuwarsa kamar yadda ya tsawaira rayuwar Khidir (a.s).   
Daga cikinsu akwai Sheikh Sadruddin Alkaunawi a cikin sashen wasiyyoyinsa ga xalibansa yayin rasuwarsa bisa abin da ke cikin Yanabi’ul Mawadda, a inda ya ce: Haqiqa littattafan da ke wajena daga littafan xibbu da littafan masu hikima da na falsafa, to ku sayar da su ku yi sadaka da kuxinsu ga mabuqata, amma littafan tafsiri da hadisu da na sufanci to ku kula da su a xakin littattafai, ku karanta kalmar tauhidi (La’ilaha Illallahu) dubu saba’in a wannan daren ku isar da gaisuwa daga gare ni zuwa ga Mahdi (a.s)   
Na ce: Zai yiwu a ce wannan faxin na sa baya nuni bisa samuwar Mahdi da rayuwarsa domin ta yiwu ya faxi haka ne, da qaunar ya riski bayyanarsa, sai dai na farkon ya fi bayyana.
Daga cikin su akwai Sheikh Sa’aduddini Alhamwi bisa abin da ke cikin Yanabi’ul Mawadda, yana cirowa daga littafin Sheikh Aziz xan Muhammadun Nafsi, yayin zancen sa a cikin jeranta waliyyai: Haqiqa Allah Maxaukaki ya zavi waliyyai sha biyu a cikin wnanan al’ummar daga Ahlulbaiti ya sanya su halifofin Annabinsa mai girma, har ya ce: Amma qarshen waliyyan wanda shi ne qarshen halifofin Annabi kuma majivincin lamari na ga sha biyu cikamakin waliyyan, shi ne Mahdi ma’abocin zamani.  
Daga cikinsu: Sheikh Shihabuddini Alhindi wanda aka sani da Sarkin Malamai a littafin (Hidayatus Su’ada ala ma fiddurarul Musawiyya) ya faxa yayin ambatonsa ga Imamai sha biyu, shi ya faku yana da rayuwa mai tsayi kamar yadda yake ga waxannan muminan, Isa da Ilyas da Khidir da kuma waxannan kafiran Dujal da Samiri.
Daga cikinsu akwai ba xaya daga masu falala da masana, domin abin nan da yake bayyana daga waqoqinsu na Arabiyya da Farisanci waxanda aka ambata a Yanabi’ul Mawadda da waninsa daga sashen littafan manaqib (darajoji), cewa suna ganin rayuwar imam Mahdi (a.s) abin sauraro kuma shi rayayyae ne ana azurta shi saboda siffata shi da ya yi da wulaya da imamanci da halifanci da wakilcin Annabi Muhammadu (s.a.w) kuma lalle shi ne wasixan kwararo baiwar Ubangiji”.   
c- A tabbatar da bayani na uku mun dogara da abin da sayyid shahid Muhammad  Baqir ya rubuta a inda yake cewa: "haqiqa fakuwa gwaji ne da al’ummu suka rayu da ita da ta kai nisan kusan shekar saba’in wacce ita ce fatarar fakuwa ta farko, domin mu bayyana hakan, zamu yi shimfixa don gabatar da fikira taqaitacciya kan gajeriyar fakuwa”.  

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA    
Mail= munirsaid92@gmail.com
Whatsapp da telegram +2348038557822.



comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: