bayyinaat

Published time: 10 ,September ,2018      02:25:28
haqiqa gajeriyar fakuwa ta kasance a matsayin mataki na farko a lokacin imamancin tsayayye abin sauraro amincin Allah Ta'ala ya tabbata a gare shi haqiqa an qaddarwa wannan imamamin tun lokacin da ya karvi imamanci al’umma
Lambar Labari: 232
haqiqa gajeriyar fakuwa ta kasance a matsayin mataki na farko a lokacin imamancin tsayayye abin sauraro amincin Allah Ta'ala ya tabbata a gare shi haqiqa an qaddarwa wannan imamamin tun lokacin da ya karvi imamanci al’umma da ya vuya daga idanuwan mutane ya wanzu yana mai nesantar da sunansa daga abubuwan da suke faruwa, ko da kuwa ya kasance yana kusa da abubuwan da zuciyarsa da hankalinsa, haqiqa an lura cewa lalle wannan fakuwar idan ta faru katsaham zata haifar da bugawar kwakwalwa kan tsarin zamantakewar a’imma a cikin al’ummara musulmi, saboda waxannan tsare-tsaren da aka saba tafiya a kansu na saduwa da Imam a ko wane lokaci, da kuma yin alaqa da shi da komawa zuwa gare shi don warware matsaloli mabanbanta, idan Imam ya faku daga shi‘arsa katsaham kuma suka yi tsammanin cewa shagabancinsa na ruhi da tunani ya yanke, wannan fakuwar   zata sabbaba babban  ba zato ba tsammani a inda ba ‘a tsammace shi ba kuma wannan zai iya tarwatsa samuwar shi’anci baki xayanta kuma ya xaixaita haxuwarsa, sai ya zama ba makawa da ayi wa wannan fakuwar shimfixa, don waxanna mutanen su saba da ita a hankali, kuma yanayin ya samar da kansa a hankali a hankali kan tushensa, kuma wannan shinfixar ta kasance ita ce: yin gajeriyar fakuwa wacce Imam Mahdi (a.s) ya vuya a cikinta daga idanun mutane, duk da cewa ya kasance a ko da yaushe yana da alaqa da jiga-jigan mabiyansa da shi’arsa da waqilansa da na’ibai da amintattunsa, daga sahabbansa Waxanda suka a matsayin igiyar sadarwa tsakaninsa da mutane muminan da suka yi imani da tafarkin imamamnci   Haqiqa tsanin da ke tsakanin mutane da imam a wannan lokacin ya kasance ta hanyar mutum huxu waxanda su waxannan wakilan sun haxu a kan tsoron Allah, kuma masu tsantseni ne kuma masu tsarki a lokacin rayuawrsu, ga su kamar haka:
1-    Usman xan Sa’idul Amri.
2-    Muhammad xan Usman xan Sa’idul Amri.
3-    Baban Qasim Husaini xan Ruh.
4-    Baban Hassan Aliyyu xan Muhammadus Samuri.
Haqiqa waxannan huxun   sun gudanar da mafi muhimmancin wakilci bisa jerantuwar da aka ambata, duk sanda xayansu ya rasu sai xayan ya maye shi a bayansa da ayyunawar Imam Mahdi (a.s).
Me mayewar ya kasance yana haxuwa da ‘yan Shi’a ya xauki tambayoyinsu zuwa Imam, ya bijiro da matsalolinsu gare shi ya karvo amsoshin tambayoyin da baki zuwa gare su wani lokacin kuma a rubuce   mafi yawan lokaci, kuma jam’ar da suka rasa ganin imamainsu su na samun damar yin alhini da rarrasar kawukansu ta hanyar waxannan wasiqoqon da ganawa ba ta kai tsaye ba. kuma na lura cewa dukkan sa hannu da wasiqun da suke zuwa daga Imam Mahdi (a.s) da rubutu iri xaya ne da tsari xaya   tsowon wakilcin wakilan nan guda huxu wanda ya kai kusan shekara saba’in, Samurri ya kasance wakili na qarshe, ya kuma bayyana qarewar lokacin qaramar fakuwa wacce ta kevantu da ayyanannun wakilai, daga nan ne babbar fakuwa ta fara wacce ba a samu wasu ayyanannun mutane da za su zamo tsani tsakanin Imam da Shi’a ba, haqiqa ya bayyana qarewar qaramar fakuwa da babbar fakuwa tare da tabbatar da qaramar fakuwar don burin riskar babbar da qarewawr cikin qaramar, domin ita - kamar yanda aka ambata a baya - ta kare ‘yan Shi’a ne ta hanyar bin matakai don gudun faxawa karo da jin rauni kewa saboda fakuwar Imam, ta samar da daidaita yanayin ‘yan Shi’a a kan tushen fakuwa, ta yi musu tanadi ta hanyar bin matakai don karvar tunanin wakilcin wasu daga Imam, da wannan ne wakilcin ya juya daga xaixaikun kevantattun mutane   zuwa tsari na gama-gari.   Shi ne tsarin Mujtahidi adili wanda ya san lamuran duniya da na addini, wanda ya dace da canjawar qaramar fakuwa zuwa babbar fakuwa.
To yanzu zai yiwu ka auna wannan matakin bisa sakamakaon abin da ya gabata, don ka fahimci cewar Mahdi wata haqiqa ce da wata al’umma ta rayu da ita, kuma jakadu da na’ibai suka yi bayanin ta tsawon shekara saba’in ta hanyar cuxanyarsu da sauran mutane, kuma ba wanda ya shinshini wata alama daga gare su a wannan lokacin mai tsayi cewar suna wasa da kalmomi ne kawai, ko ‘yan dabarbaru ne da naqalto wa mutane qarya. Shin za ka iya surantawa - dan Allah - da cewar wata qarya za ta iya rayuwar har shekara saba’in har mutum huxu majeranta su riqe ta kuma dukkansu sun rayu a kanta, su tabbata a kan tushenta, suna cuxanya da mtuane a matsayin abin da za su rayu da shi a kawukansu su riqa ganinsa a idanuwansu, ba tare da wani abu ya shige su na kokwanto ba, har ma ya zamana akwai wata kevantacciyar alaqa tsakanin waxannan mutum huxun ta yin imani da wannan qadiyyas da suke da’awar cewa suna tare da ita kuma suna rayuwa dai ta?!
Haqiqa tun da ana cewa; Igiyar qarya gajeriya ce, kuma zance na gaskiya na tabbatar da cewa ba zai tava yiyuwa a aikace a lissafin na hankali qarya ta rayu da irin wannan yanayin da kuma tsahon wannan lokacin, ba tare da waxannan alaqoqin ta hanyar karvar saqo da bayarwa sannan ta samar da amincewa ga dukkan waxanda ke kewaye da ita.
Haka nan za mu ga cewar zahirin qaramar fakuwa zai yiwu mu yi la’akari da ita a matsayinta na ilimi da aka sani kuma mai yiyuwa a aikice bisa gwaji don tabbatar da cewa aba ce mai afkuwa, don ganin an sallamawa Imami jagora (a.s) , ta hanyar haihuwarsa da rayuwarsa da fakuwarsa,   da kuma gamammiyar sanarwa da shelar da ya yi game da babbar fakuwa wacce ya vuya, ya tabbatar da ita ta fuskar rashin fitowa fili ya bayana kansa ga kowa ”.  
ZA MU CI GABA IN SHA’Allah Ta'ala:-

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA    
Mail= munirsaid92@gmail.com
Whatsapp da telegram +2348038557822.



comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: