bayyinaat

Published time: 10 ,September ,2018      03:07:42
kamar yadda Allah ya faxa game da manzon sa (SAW) {baya faxin son zuciya ba abinda yake faxa sai wahayin da aka yi masa} suratun Najm aya ta 3-4.
Lambar Labari: 233
HAKIKANIN SHIA DA FARKON TA.
Kalmar  "SHIA"
Ita wannan kalmar "shi'a" tana da ma'anar nabiya da mataimaka kamar yadda ya zo a littafin kalmomi "qamus" na kusan dukkan "qamus' xin larabci, Fairuz abady a cikin qamus ya ce kalmar "shi'a" ... "shi'aturrajul" na nufin mabiyansa ko mataimakan sa, haka nan ma'anar su xaya da firqa, tana xoruwa  kan mutum xaya, biyu, jam'in maza da jam'in mata, Wanannan Kalma ta Shia amman daga baya sai ya zama a na gayawa wanda ya jivinci Imam Ali da mutanen gidan sa, har ma sunan ya zama kamar na su ne su kaxai, jam'in kalmar shi ne "ashya'u" da "shiya'u". wannan ce ma'anar kalmar shi'a, ina fatan wannan ma'anar ba zata rikitar da ku ba daga yau.
Kalmar "shi'a" a magana: suna ne da ake gayawa mabiya Imam Ali bin Abi Xalib (AS) da mataimakan sa tun daga zamanin Manzon Rahama (SAW) ba wanda ya sa musu wannan sunan sai Manzon Rahama (SAW), daga litattafan Ahlus sunna kamar yadda zamu kawo inda su ka zo a nan gaba.
kamar yadda Allah ya faxa game da manzon sa (SAW) {baya faxin son zuciya ba abinda yake faxa sai wahayin da aka yi masa} suratun Najm aya ta 3-4.
Haka ma Manzon Rahama (SAW) ya ce : "shi'ar Aliyyu sune rabautattu" malaman sunna sun rawaito wannan hadisin da ire-iren sa a litattafan su da tafsirsn su a tafsirin ayar da ta gabata Kamar Haka:
1-    Hafiz Abu Nu'aim ya rawaito a littafin sa "hilyatul auliya'u " da sanadin sa daga ibni Abbas ya ce : lokacin da wannan maxaukakiyar ayar ta sauka {haqiqa waxanda suka yi imani da ayyuka na gari sune fiyayyun halitta} suratul Bayyina aya ta 7. sai Manzo (SAW) ya yiwa Imam Ali bin Abi Xalib (AS) magana ya ce masa : "ya Aliyyu! kai da mutanen ka zaku zo ranar alqiyama kun yarda da Allah shima ya yarda da ku".Abu Mu'ayyad Muwaqqaf Ahmad al kuwarizmi ya rawaito a fasali na 17 cikin klittafin manaqib littafin "tazkiratul kuwwasul ulama'u"  na sibx ibnil jauzi. (al-manaqib, hadisi na biyu daga hadisi na 18 cikin bayanin abinda ya sauka game da Ali (AS).
2-    Babban malamin tafsirin Sunna da aka sani da Hakimu Ubaidullahi Al'haskani ya rawaito cikin littafin sa "shawahiduttanzil" daga Hakima abi Abdullahil Hafiiz da sanadin sa zuwa Yazid bin sharahital ansary, ya ce : na ji Aliyyu (KW) na cewa : Manzon Rahama (SAW) ya bani labari cewa : "ya Aliyyu baka ji Allah na cewa : {haqiqa waxanda suka yi imani suka yi kyakykyawan ayyuka sune fiyayyun halitta} ba? (ai kai da maqiyan ka ne, mahaxa ta da ku tafkin alkausara, idan al'uImam Ali bin Abi Xalib (AS)a suka zo wajan hisabi za'a kira ku a karrama ku kuma jikin ku na ta haske".
3-    Abu Mu'ayyad Muwaqqaf Ahmad al kuwarizmi ya rawaito a "manaqib " cikin fasali na tara daga jabir bin Ab dullahil ansari, ya ce : muna zaune wajan Manzon Rahama (SAW), sai Imam Ali bin Abi Xalib (AS) ya fuskanto sai Manzon Rahama (SAW), ya ce : "haqiqa xan uwana ya zo muku" sai ya waiwaya wajan ka'aba ya dake ta da hannun sa sannan ya ce : "na rantse da mariqin raina haqiqa wannan da mabiyan sa sune ma rabauta a ranar qiyama, kuma shine farko a imaniu kuma ya fiku cika al'amarin Allah, kuma ya fiku dagewa da lamari Allah, ya fiku adalci a cikin mutane, ya fi ku raba abu daidai, sannan ya fi ku daraja a wajan Allah". Sai ayar : {haqiqa waxanda suka yi imani kuma suka yi aiki na gari sune mafiya alkhairin mutane} Suratul Bayyina aya ta 8, ta sauka.
Mai ruwaya ya ce : sahabban Manzon (SAW) sun kasance idan sun ga Imam Ali bin Abi Xalib (AS) ya fuskanto su sai su ce : fiyayyan mutanen Annabi (SAW) ya zo. (manaqibi Aliyyin (AS) fasali na 9, hadisi na 10).
4-    Jalaluddin assuyuxy babban shahararren malamin sunna ma haka ya faxa game da wannan aya da ta gabata, har ma ana ce masa mujaddadin ahlussunnah wal'jama'a a qarni na tara kamar yadda aka faxa  a "fat'hul maqal" ya rawaito a tafsirin sa "addurrul mansur" daga ibni askar addimashqy, ya rawaito daga Jabir xan Abdullahil ansary ya ce : wata rana muna zaune a wajan Manzon Rahama (SAW) katsam sai ga Aliyyu bin Abi Xalib ya shigo, sai Manzo (SAW) ya ce : "na rantse da mariqin raina, haqiqa wannan da mabiyan sa sune masu rabauta ranar al'qiyama", sai aya ta sauka : {haqiqa waxanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka masu kyau waxannan sune fiyayyun halitta}.
Haka nan ma ya kuma zuwa cikin durrul "mansur" a tafsirin ayar da ta gabata, daga bin Addi, daga bin Abbas ya rawaito cewa : lokacin da wannan ayar ta sauka Manzon Rahama (SAW) ya ce da Imam Ali bin Abi Xalib (AS) cewa : "kai da mabiyan ka zaku zo ranar al'qiyama kun yadda da Allah, shi ma ya yarda da ku".
5-    Ibni Sabbag al'maliki ya rawaito a littafin sa "fusulul himma Babi na 122, daga xan Abbas ya ce : lokacin da ayar : {haqiqa waxanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka masu kyau waxannan sune fiyayyun halitta} Suratul Bayyina, aya ta 8, ta sauka.  sai Manzon Rahama (SAW) ya ce da Imam Ali bin Abi Xalib (AS) : "ai kai ne da mabiyan ka, kun yadda da hukuncin Allah, Allah kuma ya yarda da ku, maqiyan ka zasu zo cikin fushi an banqare su".
6-    Ibni Hajar a cikin sawa'iqul muhriqa babi na 11, ya rawaito daga Hafiz Jamaluddin, Muhammad bin yusuf azzarandy almadani, har ma ya qara a ciki : sai Imam Ali bin Abi Xalib (AS)  ya ce : su waye maqiya na? Sai Manzo (SAW) ya ce: "duk wanda ya yi maka bara'a ya tsine maka!".
7-    Allama Shamhudy a cikin littafin sa "jawahirul iqxaini ya rawai to shi daga Hafiz jalaluddin azzarandy, ya yadda abinda aka kawo a sama (6).
8-    Shahararren Malamin sunna Mair Saiyyid ya rawaito a littafin sa "mawaddatul qurba" daga Ummu Salama uwar muminai matar Manzon (SAW) ta ce : Manzon Rahama (SAW) ya ce : "Aliyyu kai da tawagar ka yan Al'jannah ne, kuma kai da tawagar ka yan Al'jannah ne".
9-    Hafiz ibnul magazili shaf'iy  al-wasixy ya rawaito a
litttafin sa "Manaqib Aliyyu bin Abi Xalib (AS)" da sanadin sa daga Jabir bin Abdullahi ya ce : lokacin da Ali (AS) ya dawo daga yaqin khaibara sai Manzon Rahama (SAW) ya ce masa : "Ya Aliyyu ba don kada mutane cikin al'umma ta su faxi irin abinda nasara suka faxa a kan Annabi Isa (AS) ba, da na faxi wata maganar da idan ka wuce ta kusa da musulmai, za sun dinga xiban qasar qafarka da ragowwar ruwan alwalar ka, don su yi magani da su, saidai ya isheka cewa matsayin ka wajena kamar matsayin Haruna ne a wajan Musa, sai dai ba annabi bayana, kaine zaka sauke nauyin da ke wuyana ka suturta addini na, kuma zaka yaqi mutane kan sunna ta, gobe qiyama ka fi kowa kusanci da ni, kuma kaine halifana a tafkin al'kausara, kuma mabiyan ka suna kan membarin haske, fuskokin su sun yi haske a gefe na, sannan sune maqota na a gidan al'janna, wanda ya yaqeka ni ya yaqa haka ma wanda ya yi zaman lafiya da kai to da ni ya yi".
Mun karanta a muwaddatul qurba da abinda muka naqalto wannan maganar ga ta : an rawaito daga Manzon Rahama (SAW) ya ce ya Aliyyu , : "kai da mabiyan ka zaku zo ranar al'qiyama kun yadda da hukuncin Allah, Allah kuma ya yarda da ku,  maqiyan ku na cikin vacin rai an banqare su".
Mun karanta a "mawaddatul qurba" kan abinda muka faxa hadisin da ya gabata cewa : an rawaito cewa ; Manzo (SAW) ya ce : "ya Aliyyu, kai da mabiyan ka zaku zo ranar al'qiyama kun yadda da hukuncin Allah, Allah kuma ya yarda da ku,  maqiyan ku na cikin vacin rai an banqare su".

'YAN SHIA DAGA CIKIN SAHABBAI
Ya zo a kitabuzzeena na ibni Hatim arrazy malamin snna ya ce : "Shia" shine sunan farko a musulunci na wasu jama'a a lokacin Manzon Rahama (SAW), har sahabbai huxu sun shahara da wannan suna, su ne :
1-    Abu Zarril gifari.
2-    Salmanul farisi.
3-    Miqdad bin Aswad.
4-    Ammar bin Yasir.
Tambayar da zata zo z nan itace: ta yaya sahabban Manzon (SAW) guda huxu na kusa da shi waxanda ya ke ji da su za'a dinga kiran su da shi'a alhalin ya na ji yana gani kuma bai hana wannan ba!
Amsa itace: Manzo (SAW) shine wanda ya sanya Ali (AS) a matsayin Halifansa a bayan sa, domin ya shiryar da mutane musuluncin gaskiya a bayan sa.
Waxannan dalilai masu inganci da suka fito daga wajan mashahuran malaman sunna kan qarfafa zancen Allah ta hanyar hadisai masu inganci a daga malaman sunna, wannan kuma kaxan ne daga cikin dubunnan da su ka zo daga vangaren sunna, Ina fatan mai karatu zai bincika sannan ya fahimci Hujjar shia na fifita Ali (AS) a kan kowa bayan Manzo (SAW), da fatan bayan haka ba wanda zai sake tuhumar Shia kan fifita Ali (AS) domin ba su ne su ka fifta shi ba, Allah ne da Manzon sa (SAW) su ka fifita shi.
 Abin baqin ciki da yawa daga masu kiran kansu malaman sunna, da fatan yan uwa yanzu sun gane cewar duk musulmin kirki ya wajaba ya yi riqo da wannan fifkon Allah da Manzon sa su ka yi, domin allah da Manzon sa sun fi kowane xayan mu cancatar a kan sa,
Idan mu ka waiwaya a manyan litattafai zamu samu hadisai da yawa da suka zo daga waxanda ke da tsananin ikhlasi daga sahabban Manzo (SAW) cewa : sun ji Manzon Rahama (SAW) ya na cewa : "mabiya Aliyyu sune fiyayyun talikai, sune masu rabauta don hakane ma suka yi alfahari da hakan har ma suka shahara a cikin sahabbai da sunan "shi'ar Aliyyu".


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: