bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      14:48:02
A littattafan fiqihu kuwa, ana amfani da waxannan kalmomin masu zuwa da ma’anar mutu'a:- 'Nikahul munkaxi’i' (aure me iyaka), da 'Nikahul muwaqqati' (auren wucin gadi), Muhaqqiqul Hilliy. (Ja'afar dan Mohammad dan Sa'id, (602 – 76/1205 – 77)
Lambar Labari: 234
BANGARE NA BIYU

GINSHIQAN AUREN MUTU'A GUDA HUXU 
A cikin littafin bayanin kalmomin Larabci (qamus xin larafci) An ambaci ma’anar kalmar mutu'a da’jin daxi, nishaxi, farin ciki: Tushen kalmar ya zo ne daga m-t-; wanda ke nufin 'xaukewa', 'kawarwa', Auren mutu'a aure ne da ake qulla shi zuwa wani qayyadadden lokaci. Wannan aure na mutu'a an yi bayaninsa a hadisan Manzo (s.a.w.), kuma an yi bayani a kansa dalla-dalla a cikin litattafan fiqihu. A cikin hadisi da zantuttukan musulman farko, an yi amfani da wannan kalmar 'mutu'a' da ma’anar 'auren wucin gadi'. Shi’a sun tafi a kan cewa kalmar 'mutu'a' tana nufin  'auran wucin gadi' saboda Alqur’ani kansa ya danganta wannan auren da asalin wannan kalmar ta 'mutu'a' a yayin da ya zo da kalmar 'istimta`i' a cikin ayar da ma’anar jin daxi: 'Don haka abin da kuka ji daxi da su daga cikin su (mata) ku ba su haqqoqinsu' (4:24).  
Abin nufi dai, kalmar mutu'a an fi amfani da ita – da ma’anar auren wani lokaci - fiye da sauran kalmomin da suke nufin auren wuci gadi a lokcin rayuwar Manzon (s.a.w.) da ma bayan nan, haka ma a lokacin halifancin imaman Shi’a da sauran shuwagabannin musulmi. A cikin wasa’ilushshi’a, cikakken littafin hadisi wanda Shi’a ke komawa gare shi dangane da hukunce hukuncen fiqihu, an yi amfani da kalmar 'mutu`a' a duk inda ake magana kan auren wucin gadi. 
A littattafan fiqihu kuwa, ana amfani da waxannan kalmomin masu zuwa da ma’anar mutu'a:- 'Nikahul munkaxi’i' (aure me iyaka), da 'Nikahul muwaqqati' (auren wucin gadi), Muhaqqiqul Hilliy. (Ja'afar dan Mohammad dan Sa'id, (602 – 76/1205 – 77) shine marubucin littafin shara'i'i Islam, wanda ya tsayu a kan Fiqhun shi'a wanda ya tattara bayanai masu yawa).
A rubuce-rubucen sa yana amfani da kalmar ‘aure me iyaka’ (Shara'i'i, Baurut, 1930, 11, 23). don haka masu sharhin littafin sa ma suka yi amfani da ita, duk da cewa a wasu lokuta a ire-iren rubutunsa, wanda da ya shafi wannan auren yakan yi amfani da kalmar istimta’i da kalmar tamattu’i. Shahidus Sani (Zainuddin Mohammad dan Ali al-Amuli (911 - 65./1505 – 58). Marubucin littafin Bahiyya fi sharhul Lum'a tudumashqiyya). Wanda shahidul auwal ya rubuta) ya yi amfani da kalmomin Muhaqqiqul Hilli,( Sharhul Lum'a 5, 245) amma wasun su kamar Shahidul Auwal, (Abi Abdullahi Moh'd dan Makki al Amuli (d. 782/1380)) Allama Hilli (Jamuluddin Hassan dan Yusuf dan Zainab Dini Ali dan MUttahar Alhilli (648 – 726/1250 – 1326), Marubucin Littafin Irshadul Azanul Ahkamul Imam) da Shaikhul Ansari, (Murtadha dan Moh'd Amin Aldisfuli, (1214 – 81/18000 – 64). Ayyukansa sun hada da irin su al-matajir, Fiqhu, Arrisa'il, da kuma Fiqhu Tare da sauran ilmomin kimiyya da fasaha) duk sun zavi kalmar mutu'a. (Sharhul Lum'a, 5, 245 Almatajir, Tehran (1352/1993). Littafi ne a kan mutu'a, wanda Allama (Irshad) ya rubuta).
A cikin litattafan fiqihun sunna akwai tattaunawa kan ko auren mutu'a dai-dai yake da 'auren wuci gadi' ko ba dai-dai yake da shi ba. Mafi yawansu sun tafi a kan cewa dukkaninsu abu xaya ne. (Fiqhu 4, 90). 
A wasu rubuce-rubucen ana amfani da muhimmiyar kalmar nan ta 'musta’ajara' wato 'matar haya' ga matan da suke yin mutu'a. Ana xaukar kalmar mutu'a a matsayin 'haya' saboda babban burin namiji a auren mutu'a shi ne kawar da sha’awa ta hanyar jima’i tare da biya ko bada lada ko sakawa matar da kuxi ko makamancinsa. Ma’anar 'haya' a sharia: 'it ace amfanuwa da wani abin buqata ta hanyar biyan wani adadi na kuxi'. (Shara'i I, 233). Wannan ma’ana dai-dai take da ma’anar auren wucin gadi. Hadisai da yawa sun zo da kalmar musta’ajara. (Mohammad Dan Hassan Al-Hur, Al-amuli (1033 – 1104/1624 – 93). Cikin wasa'ilus shi'a, Tehran 1385/1965 – 66 – xic, 446). 
Malaman fiqihun Shi’a suna kallon auren wuci gadi da idon da suke kallon auren din-din-din, (dukkanin su aure ne cikakku, illa iyaka sun sava ne a wasu sharaxai). Auren mutu'a yana da ginshiqai da tsare-tsare, kamar yadda auren da’imi yake da ginshiqai biyu, wato, siga da kuma su ma’auratan, haka ma auren mutu'a yake da su, qari a kan lokaci iyakantacce da kuma sadaki.  

1.    Siga 
Tun da auren mutu'a kulla shi ake, yana buqatar 'nema', 'bayarwa' da 'karva' kamar yadda yake a auren da’imi, abin da ake nema a wajen mace da farko shi ne bayarwa, dole bayarwar ta xauki xayan sigogi uku na larabci irin waxanda Shi’a suke amfani da su a auren da'imi (na din-din-din). Sayyid Murtada (Ali dan Hussain Al-Musawi (355 – 465 – 1044) Ali dan Hussain Shararen malami ne, kuma ya tattara abubuwa masu yawa, wanda yake dan'uwa mai suna: Sharifur-Radi (d. 406/1015), shima shahararren malami ne, duba Nahjul Balagha din sa) ya qara da cewa: Baiwa zata iya yin amfani da sigar 'Na ba ka dama' (abahtu- ka) ko 'Na halattamaka 'hallaltuka' (Riyad, 11, 113, Mukhtasarin Nafi, wanda akai a karni na 18/14. Da akwai wadansu Karin bayanai da aka yi ta harshen Farisa wato (Iran) wanda allama Muhaqqin ahilli ya fitar, akwai ma na wani marubuci wanda bai bayyana sunan sa ba; sai dai ya zo kamar haka: (ed. M.T DHANESH PHAZUN TEHRAN, 1343/1964, 231)), amma wannan maganar ta sa, ba ta samu karvuwa ba a wajen wasu malaman. Shahidus Sani ya ce: 'Ni a waje na ina ganin zai fi kyau mu taqaitu da kalmomin ukun farko'.(Asshahidussani, masalikil afham, (wanda yake magangane akan shari'a Tehran, 1273/1856 – 57, 1536)) A haqiqa babu savani a kan cewa mace ba zata iya amfani da lafazozi kamar: 'Na ba ka damar mallaka', 'Na ba ka kaina a matsayin kyauta', Na baka kaina ko 'na baka aron kaina' ba. 
Bayyana 'Amincewa' ko 'karva' na kasancewa gada vangaren namiji bayan mace ta bayyana nema da bayarwarta; misali, zai ce: 'zan karvi wannan auren', ko 'Na karvi wannan mutu'a', idan da zai ce kawai: 'Na karva' ko 'Na gamsu', to auren ya qullu. 
Ba a sharxanta bayyana nema - daga mace - ya rigayi karva ba, don saboda qulla aure ya haxa da nema da karva, ana iya farawa da kowanne. Wannan an sami haxuwar malamai a kansa.(Sharhul Lum'a 5, 110). Muhaqqiq Hilli ya bayyana qarara cewa idan namiji ya ce: 'Na aure ki', sannan matar ta furta abin da ya furta to aure ya qullu.(Shara'i 11, 24). 
A fatawar Allama Hilli, dole sigar qulla auren ta kasance cikakkiyar jimla (perfect tense).(Al-Matajir 11, 298) Amma mafi yawan malamai sun tafi a kan cewa ba dole ne sai qullawar ko furtawar ta zamo da cikakkiyar jumla ba, (perfect tense), matuqar a kwai niyyar qulla auren.(Riyad 11, 113) Hadisai da dama sun hakaito cewa ba sai da cikakiyar jumla ba. Misali, an tambayi Imam Ja'afarus Sadiq (a.s) cewa: wace siga ake furtawa yayin xaura auren mutu'a?. sai ya ce: 'Na aure ki auren mutu'a bisa tafarkin littafin Allah da sunnar Manzo (s.a.w), ba tare da cin gadona ba ko gadonki na wasu kwanaki, bisa wani adadi na kuxi --- (Al-wasa'il x4, 466). 
Dokokin da suka yi magana kan qulla auren sun nuna dole me bayyana neman da me karva su cika sharuxxan wannan auren. (ahlul aqdi). (su cika sharaxai waxanda suke hallata a qulla musu wannan auren). Dangane da lamarin auren mutu'a kuwa dole ne ma’auratan da za a qullawa auren su kasance namiji ne da mace, su da kansu su xauki nauyin qullawar ko kuma wakilansu ko iyayansu. Misali, uba na da damar ya ce: 'Na bada ‘yata auren mutu'a bisa yardar ta'. Idan wanin waxannan mutane ya qulla auren to bai qullu ba (vatacce ne).


Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: