bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      14:54:26
Idan kuma baiwa ta kasance mallakar wani ce, to bai hallata a qulla mutu'a da ita ba, ba tare da izinin mamallakinta ba.
Lambar Labari: 235
2. Ma'aurata (Mijin Da Matar) 
Namiji na iya qulla mutu'a ne kawai da musulma ko ma’abota littafi. Bai halatta a qulla mutu'a da mushirika ko maqiyin/maqiyiyar iyalan gidan Manzo (s.a.w) ba, kamar khawrijawa d.s.s, kuma bai halatta musulma ta auri wanda ba musulmi ba. 
Idan mutum ya yi auren da’imi da mace `ya, to bai halatta ya yi auren mutu'a da baiwa ba, har sai ya nemi izinin matarsa. (wacce ta ke `ya ba baiwa ba). 
Da zai aikata hakan to aure bai qullu ba, ko kuma wajibi ne a dakatar da shi, har sai ta amice. 
Idan kuma baiwa ta kasance mallakar wani ce, to bai hallata a qulla mutu'a da ita ba, ba tare da izinin mamallakinta ba. Hadisai  da dama sun zo da  wannan bayanin-  misali, Imam jafar (a.s) ya ce: 'Babu   laifi yin  auren  mutu’a  da baiwa matuqar an nemi izanin me ita’ (Ibid, 463).
Bai halatta namiji ya auri, `yar `yar’uwar matarsa ko `yar xau uwan matarsa ba, ba tare da iznin matar ta sa ba. Da zai aikata hakan to auren bai qullu ba, sai dai a dakatar da auren har sai ta yarda. (Sheikh Mohd Hassan (d. 1266/1850), Jawahirul Kamal (littafi ne dake Magana kan shari'a), Tehran, 1325/1907, 5, 165)  Bayan waxannan biyun da aka keve, sauran waxanda aka haramta a aure su aure na din-din-din, an haramta a aure su auren mutu'a. 
An so (mustahabbi ne) mutum ya yi auren mutu'a da mace musulma kamammiya ba fajira ba, wacce ake kira da 'Afifa' wato mai kamun kai ita ce wacce ba ta tava yin zina ba,  kuma wacce take bin shari’a a cikin al'amuranta,  waxannan kalmomi biyu da aka dangantata da su 'musulma   kuma  nutsatstsiya' an  samo su ne daga faxin Imamai biyu; an tambayi  Imam al- Rida: (a.s) 'mutum  na iya auren mace bayahudiya ko banasariya'? sai ya ce 'na fi yi masa zabin ya auri `ya kuma musulma'. (Wasa'il x4 452) Amma game da mutu'a, da aka tambayi Imam jafar (a.s) cewa ya yi: domin Allah ya ce: {Da kuma waxanda da suke kare   tsiraicinsu} (23”5) don haka ka da ka yi amfani da kuxinka wajen sanya tsiraicinka a inda ba ka da kwanciyar hankali (Ibid). 
Idan  mutun yana zargin wata mace, to ya fi kyau kafin ya qulla mutu'a da ita ya tambaye  ta game da halin da take ciki, ma’ana; game da ko tana da miji ko a’a, kuma ko kamammiya ce ko a’a. Amma tambayar ba ta daga cikin sharuxin qulla aure. (Jawahir, 5, 165). A qarqashin dokokin fiq'hu (Usulul Fiqhu, Dakuma littafin da aka yi kan kimiyya dana zamantakewar rayuwa da tsare-tsare da kuma dokoki) bisa tsarin dokokin (na bincike) da musulmai suke rayuwa a kansu, (Usulusshi'a)  idan mace ta so ko ta yi nufin yin mutu'a, ba aikin wanda zata aura ba ne, yin bincike kan cewa tana da aure ko ba ta da shi, ko da kuwa yana zarginta, amma bai tabbatar ba, musali, Idan muna kokwanto a kan halaccin (ingancin) auren wasu ma’aurata to sai mu xauka cewa auren ingantacce ne. idan ba haka ba, sai kuma mu shiga shakku a kan halaccin ‘ya’yansu, shin akwai gado tsakaninsu ko baba?. kamar dai misalin salla. Idan mutun ya shiga kokwanton ko kuma ya yi kokwanton adadin raka’o'in sun cika ko sun gaza bayan ya idar da salla, to sai ya xauka cewa sun cika cif. Idan ba haka ba sai ya xauki lokaci yana maimaita abin da tuni ya riga ya aiwatar, don xan qanqanin kokwaton zai iya kai shi ga maimaita aiki. 
A kan wannan ka’ida ta shari’a dole mutun ya nisanta kansa da tunani a kan cewa matar da zai aura ba ta da kamewa ko hali ko nagarta. Don haka babu buqatar ya tambaye ta. Hadisai da dama sun kausasa magana dangane da hakan bayan an xaura aure. Misali, wani ya tambayi Imam Jafar (a.s); 'na auri wata mata auren wucin gadi. Sai kuma daga baya na fuskanci kamar tana da miji , sai na bincika har na gano haka ne'  sai Imam ya ce: 'to me ya sa ka bincika'? (Al-Wasa'il x4, 458 Hadiss 3). 
An karhantawa mutun yin auren mutu'a da mazinaciya, kamar yadda alqur’ani ya bayyana yana mai kafa hujja da cewa: mazinaci ba ya aure sai mazinaciya ko mushrika. Kuma mazinaciya ba me aurenta sai mazinaci ko mushriki. Wannan kuma haramun ne ga mumunanai (24:3). Idan mutun ya xaura auren mutu'a da mazinaciya, to lalle ne ya tabbatar ya umarce ta da kar ta aikata zina, amma wannan ba sharaxin qulla aure ba ne kamar yadda yake a dokar fiqihun musulunci. (Jawahir, 5, 166) 
Haka nan an karhanta yin auren mutu’a - da dukkanin kashe-kashwn sa da nau’o’insa - da budurwa, kamar yadda ya zo daga faxin Imam Ja’afar: 'ba a so haka ba (an karhanta hakan) saboda zai haifar da wani tanbari a kan danginta (Wasa'il x4 459, Hadiss 10) idan auren ya zama babu makawa sai an yi, to ba a yarda mutum ya yi jima’i a auren ba sai idan har an sami amincewar iyayenta …..' imam al-rida (a.s) ya ce: budurwa ba zata yi auren mutu'a ba, sai da amincewar iyayenta” (Ibid, 458, Hadiss, 5).


Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: