bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      14:58:11
Wannan sura ta sauka ne lokacin da kafirai ke qoqarin nunawa Manzo (SAW) cewa ya zo su haxu wajan bauta tare, abin nufi su haxu yau a bautawa Allah (SW)
Lambar Labari: 236


سورة الكافرون

SURATUL KAFIRUN (SURA TA 109)

Sratul kafirun ko surar kafirai, kafirai a nan wajan anan nufin masu bautar gumaka, domin kafirci mataki – mataki ne, wannan sura na tabbatar mana da cewa ba yadda mutum zai iya xauke hannun sa daga tauhidi, duk da cewa mutum na iya ganin zai iya janye na zahiri amma ba a haqiqa ba.

DALILIN SAUKA

Wannan sura ta sauka ne lokacin da kafirai ke qoqarin nunawa Manzo (SAW) cewa ya zo su haxu wajan bauta tare, abin nufi su haxu yau a bautawa Allah (SW) gobe kuma a bautawa gumaka, haka zai baiwa kowa mafita, a qarshe zai zama cewa idan yadda ya faxa ne gaskiya cewa akwai lahira, kowa zai samu rahama, idan kuma kamar yadda su ke faxa cewa ba tashin lahira ne ba abinda kowa zai cutu da shi, ba kamar yadda Manzo (SAW) ke faxa ba, sun yadda akwai Allah amma basu yadda akwai lahira ba, su na bautawa gumaka don su kare su daga musibun duniya ne kawai, amma ba na lahira ba don babu ita a wajan su, wannan shine tunanin mutanen Makka lokacin Manzo (SAW).

Al'halin su ya kamata a gayawa hakan su da ke bautar gumaka, tunda a wajan su ba hisabi ya kamata su bi wanda ya ce akwai hisabi, ta yadda idan akwai sun kuvuta idan kuma babu an yi daidai da abinda su ka faxa, su na son shirya makirci ne kawai ga Manzo (SAW), sun manta cewa ba dole sai musulmai sun bautawa gumaka ba ko kuma su su bautawa Allah ba tare da Imani da Manzon sa (SAW) ba wajan a zauna tare, kawai dai wani wayo su ke son wai su yi wa Manzo (SAW) don su samu damar gurvata abinda ya zo da shi.

Shixan ba ta inda baya zuwa yakan zo wa mutum ta inda ya sani da inda ma bai sani ba, domin ya kan zo maka ta dama, in bai samu nasara ba sai ya zo ta haxu, gaba, baya, sama da qasa duk sai ya gwada ko zai samu nasara, kamar yadda mu ka yi baya ni a fassarar ta'awizi (TAFSEER 1), sabida kafirai sun bi duk hanyoyin da su ke ganin ya kamata su bi wajan hana Manzon Allah kira zuwa ga taihidi, sun zo masa ta sama (ta wajan baffansa) sun zo ta qasa (takura shi ta dukkan hanyoyin rayuwa wajan cutar da iyalin sa) sun zo ta hagu (sa qarfi wajan cutar da mabiyan sa) shi ne yanzu su ka zo ta dama (wai a bautawa gumaka tare a yi salla tare).

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (1)

Da sunan Allah mai rahama (mai faxin da take ko ina) mai jin qai(rahama ce kevantacciya wadda bata haxe komai ba kamar yadda rahmaniyya ba).

قُلْ يَا أَيُّهَا الْكَافِرُونَ (1)

Ka gaya musu ya ku kafirai.

لَا أَعْبُدُ مَا تَعْبُدُونَ (2)

Ba zan bautawa abinda ku ke bautawa ba.

وَلَا أَنْتُمْ عَابِدُونَ مَا أَعْبُدُ (3)

(Kuma) ba za ku bautawa abinda na ke bautawa ba.

وَلَا أَنَا عَابِدٌ مَا عَبَدْتُمْ (4)

A nan gaba ma ba zan bautawa abinda ku ke bautawa ba.

وَلَا أَنْتُمْ عَابِدُونَ مَا أَعْبُدُ (5)

(Ku ma) a nan gaba ba zaku bautawa abinda na ke bautawa ba.

لَكُمْ دِينُكُمْ وَلِيَ دِينِ (6)

Addinin ku na gare ku, ni ma addini na na gare ni.

Domin faɗaɗa bayani a bincika tafsirin Qur'anin Al-mizan na Allama Ɗaba-Ɗaba'i.

Ibrahim Muhammad Sa'id

+989368244976, +2348068985568

Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: