bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      15:07:22
Risalar Humawiyya shafi na 429 a ciki “Rasa’ilil kubra”sannan abumai burgewa a cikin wannan al’amari na Ibn tai miyya ya yi amfani da ayar nan da Fir’ana yake cewa
Lambar Labari: 238
Gazakhan wanda yake daya daga cikin shahararrun sarakunan Ilkhani (Magul) wanda yake har ya musulunta amma duk da haka nan bai bar tunanin kai wa Misra da Sham hari ba. Sakamakon haka ne tsakanin shekara ta 699-702 garuruwan Sham suka hadu da yaki mai tsanani wanda ya auku tsakanin sarakunan Magul da sarakunan Musulmi na misra, sannan mafi yawancin nasarar da sarakunan Magul da suka yi a kan musulmi ya kasance matsayin taya murna da Karin karfi ga kiristocin da suma suke yakin musulmi. (  Domin samun Karin bayani a kan Sarakunan Magul da alakarsu da kiristoci a kan yakin musulmi ana iya tuntubar littafin Abbas Ikbal Ashtiyani mai suna Tarihin Magul a shafuka na 191, 197;202, 204, 204, 216, 237, 245, 266. 
  Risalar Humawiyya shafi na 429 a ciki "Rasa’ilil kubra”sannan abumai burgewa a cikin wannan al’amari na Ibn tai miyya ya yi amfani da ayar nan da Fir’ana yake cewa a gina masa gini zuwa sama domin ya je ya ga Allah da Annabi musa yake cewa akwai, wato yana kafa dalili a ksan samuwar Allah a sama da wannan aya)  
A wannan matsanancin hali ne Ibn Taimiyya ya fara yada wadannan munanen akidu nasa, sakamakon haka ne manyan malaman musulunci (Sunna da Shi’a) na wannan lokaci suka tashi tsaye domin kalu balantar wannan akidu wadanda suka haifar da babbar baraka tsakanin al’ummar musulmi. 
A daidai wannan lokaci duniyar musulmi tana cike da bukatar wani mai karfin zuciya wanda zai tashi ya kara kiran musulmi a kan hadin kai da tsayuwa a sahu guda daya domin yakin mushirikai da kiristocin da suke yakar musulmi da musulunci, amma abin bakin ciki a wannan lokaci sai Ibn Taimiyya sabanin wannan abin da duniyar muslmi suke bukata wato hadin kai, sai kawai ya zo da abin da ya kara raba kan al’ummar musulmi. 
An haifi Ibn Taimiyya a shekara ta (661BH) a garin Harran, wato bayan faduwar daular Bagdad da shekara biyar, Harran daya daga cikin garuruwan sham ne, sannan Ibn Taimiyya ya fara karatunsa na farko har zuwa lokacin da ya kai shekara 17 a wannan gari nasu. Hare-haren Magul zuwa wasu daga cikin garuruwan Sham, ya kasance abu mai ban tsoro ga zukatan al’umma a wannan lokaci, sakamakon haka ne Abdul Halim wato mahaifin Ibn Taimiyya tare da wasu daga cikin na kusa da shi suka bar wannan gari nasu zuwa Damaskas kuma suka ci gaba da zama a wannan gari, har zuwa shekara ta 698 ba a ji wani abu ba daga Ahmad Ibn Taimiyya, amma daga farkon karni na takwas aka fara jin wasu akidu masu ban tsoro daga Ibn Taimiyya, musamman a lokacin da mutanen Hammat suka bukace shi da ya fassara musu ayar nan wacce take cewa "Arrahaman alal arshis tawa” yayin fassara wannan aya ya hadu da matsaloli ta yadda ya baiwa Allah wuri a sama yana zaune a kan wata karagar mulki (Risalar Humawiyya shafi na 429 a ciki "Rasa’ilil kubra”sannan abumai burgewa a cikin wannan al’amari na Ibn tai miyya ya yi amfani da ayar nan da Fir’ana yake cewa a gina masa gini zuwa sama domin ya je ya ga Allah da Annabi musa yake cewa akwai, wato yana kafa dalili a ksan samuwar Allah a sama da wannan aya).  
Mafi yawan musulmi daga cikinsu akwai ‘yan Shi’a wadanda suka yi imani da cewa Allah madaukaki ya tsarkaka daga jiki da duk wani abu na jiki, sun yi Imani da cewa Allah madaukaki ya wuce ya kasance a wani wuri na musamman domin hakan zai kasantar da Ubangiji wanda ya takaita a wani wuri sabanin wani wurin, domin kuwa kamar irin ayoyin da suke cewa” Allah ba ya kama da wani abu, ko kuma wacce take cewa; "Ba shi da wani mai kama ko daidai da shi”. Dukkanin wadannan ayoyi suna tabbatar mana da cewa Allah madaukaki ba ya kama da wani abu daga cikin siffofin bayinsa. 
Amma Ibn Taimiyya kamar yadda ya fassrara ayar da muka ambata a sama ya siffanta Allah da mutum ta yadda yana zaune a kan al’arshi kamar yadda mutum zai zauna a kan karagar mulki. 
Yaduwar wannan amsa ta Ibn Taimiyya a garin Damashka da gefenta ya sanya malamai suka yi wa Ibn Taimiyya ca a kan wannan magana, Sannan malaman wannan zamani suka bukaci alkali Jalaluddini Hanafi wanda yake shi ne alkali a wannan lokaci da ya gurfanar da shi a gaban kotu sannan ya hukunta shi, sakamakon haka ne alkali ya kira shi domin ya amsa karar da ake yi masa amma Ibn Taimiyya sai ya ki halartar wannan kotu. 
Ibn Taimiyya ya ci gaba da yada akidunsa wadanda suka sabawa na musulmi a wannan lokaci, sakamakon haka ne duk ya rikita al'amura a tsakanin al’ummar musulmi. Yana cikin haka ne a shekara ta 705 aka gurfanar da shi a gaban kotu yayin da kotu ta yanke hukunci korar sa daga kasar Sham zuwa kasar Misra. Ibn Taimiyya ya kasance a cikin Kurkuku har zuwa shekara ta 707 in da ya fito daga kurkuku kuma a shekara ta 712 ne ya dawo zuwa Sham in da ya ci gaba da yada akidunsa, sakamakon haka ne a shekara ta 721 aka sake hukunta shi a kotu inda aka aika shi zuwa gidan jarun, a shekara ta 728 ne kuma ya riga mu gidan gaskiya a cikin gidan kurkuku. (Albidaya wannuhatyana Ibn kathir:14/52). 
Wannan littafi ba zai ba da damar yin bayani ba a kan abin da malaman Sham da Misra suka sanar a kan Ibn Taimiyya a wannan lokaci, sai dai kawai a nan zamu wadatu da yin bayani a kan abin da ya sauwaka ta yadda kawai zamu iya fahimtar yadda Ibn Taimiyya ya kawo rudani a tsakanin al’umma da malam wannan zamani, sannan mu fahimci irin yadda ya shuka itaciyar munafunci a tsakanin al’umma.
Shahararren dan yawon shakatawar nan mai suna Ibn Batuta ya yi bayani a cikin littafinsa mai suna tafiye-tafiyen Ibn Batuta, yana cewa: A Damaskas na ga wani babban Fakihi na Hambaliyya mai suna Takiyyudin Ibn Taimiyya, ya ci gaba da cewa wannan malami ya kasance yana magana a fannoni daban-daban na ilimi sai dai ya kasance tunanisa taikaitacce ne, sai ya ci gaba da bayani, ya ce a wata jummu’a Ibn Taimiyya ya kasance yana wa’azi a wani masallaci sai ni ma na halarci wannan wa’azi nasa, daga cikin maganganunsa ga abin da yake cewa: Allah madauki ya kasance yana sakkowa daga Al’arshi zuwa sama ta daya kamar yadda nake sakkowa haka daga bisa mimbari, yayin da ya fadi wannan magana sai ya sakko daga bisa matakalar mimbari daya wato haka Allah yake sakkowa daga al’arshi zuwa sama ta daya, a wannan lokaci sai wani malami fakihi dan malikiyya mai suna Ibn Zahra ya kalubalance shi a kan wannan ra’ayi nasa, amma mutane sai duk suka tashi domin nuna goyon bayansu ga Ibn Taimiyya sannan suka ci gaba da dukan wannan malami dan malikiyya. (Littafin ibn baituta.) 

Wahabiyya na Ayatullahi Ja'afar Subhani.
Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: