bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      15:09:40
sannan suka yi bayani a kan kura-kurarensa. wasu daga cikin manyan malaman da
Lambar Labari: 239
Wannan wasu daga cikin akidunsa kenan wanda Ibn Batuta da kansa ya ji ya gani, sakamakon haka ne duk wani mutum wanda yake mai hankali da masaniya a kan Allah madaukaki idan ya ji irin wannan bayani a kan Allah madaukaki dole ne ya nemi tsari daga Allah a kan hakan. 
Duk da cewa Ibn Taimiyya ya kawo rudani a cikin al’umma amma gefe guda kuma ya taka rawa a addini, amma bai kamata ba mabiyansa su runtse idanunsu a kan abubuwan da ya yi na kirki su manta da abubuwan da ya yi wadanda ba na kirki ba ta yadda zasu yabe shi ko ta halin kaka ba tare da la’akari da hakan ba. 
Amma masu neman hakikanin al’amura fiye da Aflaton wato masu ‘yantaccen tunani sun yi nazari ne a kan dukkan wadannan sassa guda biyu wato abubuwansa na kirki da na banza, sannan suka yi bayani a kan kura-kurarensa. wasu daga cikin manyan malaman da suka tashi da irin wadannan ayyuka kuwa, sun kasance daya daga cikin manyan malaman da ake ji da su a wannan zamani a garuruwan Sham da Misra, yayin da suka fitar da sakamakon cewa lallai akidun Ibn Taimiyya sun sha bamban da koyawar annabawa da waliyyan Allah. A kan haka ne suka rubuta littattafai daban-daban don kalu balantar wadannan akidu da koyawar Ibn Taimiyya, daga cikin wadannan malamai kuwa su ne kamar haka: 
1-Sheikh Safiyuddin Hindi Amuri (644-715Bh) 
2-Sheikh Shahabuddin Bn Jahbak kilabi Halbi ya yi wafati a (733BH) 
3-Alkalin alkalai Kamaluddin zamalkani (667-733) 
4-Sadaruddin murahhil ya rasu a (750) 
5-Shamsuddin Muhammad Bn Ahamad Zahbi ya rasu (748) 
6-Ali Bn Abdulkafi subki ya rasu (756) 
7-Muhammad Bn shakir kutbi ya rasu (764) 
8-Abu Muhammad Abdullahi Bn As’ad yafi (698-768) 
9-Abubakar Hasani Damashki ya rasu (829) 
10-Shabuddin Ahmad Bn Hajar Askalani (852) 
11-Shahabuddin Bn hajar Haitami ya rasu (973) 
12-Jamaluddin Yusuf Bn tagarriAtabaki (812-874) 
13-Mulla Ali Kari Hanafi ya rasu (1016) 
14-Abul Ais Ahmad Bn Muhammad Maknasi wanda ya shahara da Abuk kadhi
15-Yusuf Bn Isma’il Bn Yusuf Nabhani (1265-1350) 
16-Shaihkh Muhammad Kauthari Misri ya rasu (1371) 
17-Shaikh Salama Kadha’I Izami ya rasu 1379Bh
18-Shaikh Muhammad Abuz Zahra (1316-1396) 
Wasu daga cikin wadannan manyan malamai sun rubuta littafai musaman a kan raddin akidun Ibn Taimiyya kamar Takiyyuddin Subki wanda ya rubuta littafai guda biyu a kan haka masu suna (Shafa’us sikam fi ziyarati khairil anami da Addurral madhiyya fi raddi ala Ibn Taimiyya. 
Domin mai karatu ya san yadda malaman ahlussuna suka yi wa Ibn Taimiyya hukunci yana da kyau mu yi nuni zuwa wusu daga cikin maganganunsu kamar haka: 
Shamsuddin Zahbi wanda yake daya daga cikin manyan malaman AhlusSunna kuma wanda yake ya yi fice wajen ilimin hadisi da ruwaya a lokacinsa, sannan kuma kamar Ibn Taimiyya yana bin mazhabar Hambaliyya ne, a cikin wasikarsa wacce take cike da nasihohi zuwa ga Ibn Taimiyya yana cewa:
Shin yanzu lokaci bai zo ba wanda zaka bar wannan duhun jahilci ka bar abin da kake yi ka tuba zuwa ga Allah? duk da cewa kana fuskantantar shekara saba’in na rayuwarka kuma kana yin kusa zuwa ga mutuwa, ina rantsuwa da Allah ba ni tsammani cewa kana yin tunanin mutuwa, ba ma kawai haka ba, kana wulakanta wadanda suke yin tunanin mutuwar, duk da cewa ba ni tsammanin zaka yarda da Maganata kuma ka amshi nasihata, kawai na san dangane da wannan ‘yar gajeruwar maganar tawa zaka yi dogowar magana wacce zata sanya in yanke maganata, kodayaushe kana tunani a kan daukaka a gareni amma kawai na zabi in yi shiru ne. Duk da cewa kasan kai abokina ne amma kake yi mini haka, to ya zaka yi wa makiyyanka? ina rantsuwa da Allah daga cikin wadannan abokan gabar naka akwai masu dimbin ilimi, kamar yadda yake akwai daga cikin masoyanka wadanda jahilci da karya da rashin mutunci suka baibayesu. Zan yi matukar farin ciki idan zaka aibanta ni a zahiri, amma a boye ka amshi nasihata zuwa gareka, Allah ya jikan wanda ya gaya mini aibuna a matsayin kyauta zuwa gareni. (Takmu llatus saifu sakil :109-192)  
Masanin nan mai bincike wanda yake ya yi zamani da Ibn Taimiyya ya yi Imani da cewa: Ibn Taimiyya a cikin rigar bin kur’ani da Sunna da yin da’awar kiran mutane zuwa ga gaskiya da shiryar da su zuwa ga aljanna, ya sanya bidi’a a cikin akidun musulunci, sannan ya karya shika-shika musulunci. Ibn Taimiyya ya tashi tsaye domin fito na fito da dukkan al’ummmar musulmi, sannan ya yi wata magana wacce take nuni da cewa Allah madaukaki yana da jiki da gabobi, sannan ya yi Imani da cewa duniya ta kasance akwaita fil azal, sakamakon wannan maganganun ne nasa ya fita daga kungiyoyi guda 73 da ake fada na musulmi.(Adduratul Madhiyya fi raddi ala Ibn Taimai yya Subki:50)  
Sannan Asakiri a cikin tarihin rayuwar Ibn Taimiyya ya ambaci wata risala ta Ibn Taimiyya wacce yake yabon Mu’awiyya a ciki, sannan yake nuni da rashin halarcin la’antar Yazid. (fawatul wafayat Subki:1:77)  Sannan Ibn Hajar Haitami wanda duk masana sun tafi a kan girma da falalarsa a kan Ibn Taimiyya ga abin da yake cewa: 
Allah madaukaki ya batar da shi sannan ya hallakar da shi kuma manyan malaman Ahlussunna sun tabbatar da rashin ingancin akidunsa. Don haka duk wanda yake so ya samu masaniya a kan akidunsa ya koma zuwa ga littafin Abul Hasan Subki da dansa Tajuddin da shugaban Ahlussunna Izzuddin Bn Jama’a. 
Maganganun Ibn Taimiyya ba su da wani matsayi, sannan shi mutum ne wanda ya kawo bidi’a, sannan mai batar da mutane wanda ba shi da birki. Allah madaukaki ya yi masa abin da ya kamata da adalcinsa sannan mu kuma ya tsare mu daga sharrin akidunsa. (Alfatawa haditha 86 tathirul fu’ad bugun misra wanda sheikh Muhammad bukhait ya rubuta.)  
Sakamakon kalu balantar da Ibn Taimiyya ya fuskanta daga malaman lokacinsa da na bayansa ya sanya akidunsa suka yi sanyi kuma suka yi ma gab da a manta da su, ta yadda da wahala ka ji wani yana magana a kan wadannan akidu nasa, ta yadda kamar ba a taba yin wannan mutum ba a bayan kasa, kuma kamar ba a taba zuwa da irin wadannan akidu nasa ba. Wadannan manyan masana da muka ambata a sama sun yi iya kokarinsu domin yin fito na fito da wadannan akidu marasa tushe, sannan sun yi riko da sunnar Ma’aiki (s.a.w) inda yake cewa: "idan bidi’a ta bayyana a cikin al’ummata to ya wajaba a kan malami ya bayyanar da ilminsa domin fito na fito da wannan bidi’a, idan kuwa bai yi haka ba to la’ana ta tabbata a kansa” (Alkafi:1:54 babin bidia da ra’ai hadisi na 1). 
Kuma sakamakon wannnan fito na fito ne ya sanya ba zaka ga wani abu ba dangane da Ibn Taimiyya sai kawai a cikin littafin almajirinsa wato Ibn kayyum Jauzi (691-751) sannan shi kan shi wannan almajiri nasa wato Ibn Kayyum a cikin littafisa (Arruh) ya kalubalanci wadannan akidu na malaminsa. 
A yanzu dole mu yi nazari a kan ta yadda wannan akida wacce ta bace ta kuma zama tarihi amma a cikin karni na sha biyu tauraruwarta ta sake bullowa kuma aka ci gaba da yada wannan akida ta hanyar wasu mutane da zamu yi maganar su. Saboda haka makalarmu ta gaba zata yi magana ne a kan haka. 

Wahabiyya na Ayatullahi Ja'afar Subhani.
Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: