bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      15:23:06
waxanda suka gabatar da Imam Ali game da halifanci. Abul’aswad Addu’uli ya na cewa
Lambar Labari: 241
Bayan dukkan waxannan bayanai ina son in xan karkato da hankulanmu cewa yayin da nake karanta litattafan tarihi ban ga wani lokaci ba duk da yake ya na da tsawo a duk faxin rayuwar halifofi da na samu wani ya yi zagi daga sahabban Imam Ali (A.S), kuma sai dai kawai akwai wanda ya yabi halifofi akwai kuma wanda ya yabi Imam Ali (A.S) hatta da masu tsananin riqo da wilayar Ali ba mu samu wanda ya zagi wani ba daga waxanda suka gabatar da Imam Ali game da halifanci. Abul’aswad Addu’uli ya na cewa: 
Ina son Muhammad so mai tsanani
Da Abbas da Hamza da wasiyyi
Qasqantattu Banu Qushair suna cewa
Tsawon zamani kada ka manta da Ali
Ina son su saboda son Allah har sai
na zo, idan aka tashe ni a kan sona
‘Ya’yan ammin Annabi makusantansa
Mafi soyuwar mutane dukkansu gurina
Idan son su ya kasance shiriya na dace
Ni ba mai kuskure ba ne idan halaka ne (Alkamil, Mubarridu, hamishi ragbatil amal, j: 7.)
Haxa da cewa har ma zamani na biyu na lokacin Umayyawa mafi yawancin Shi'a suna kau da kai daga zagin Sahabbai, ko Tabi’ai: Ibn Khalikkan ya na faxa game da Yahaya bn Ya’amur: Ya kasance xan Shi'a ne daga masu yabon Ahlul-baiti (A.S) babu wani suka da yake yi ga waninsu(Wafyatul a’ayan, j 2, shafi: 269).


 

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: