bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      15:24:28
ya ba wa rundunar Sham damar su keta mutuncin musulmai, ya yanka iyaye da yaransu, har sai ka ga sojan Sham ya dauki mai shan nono daga hannun uwarsa ya buga kansa a kan bango har sai kwakwalwarsa ta yi tarwatsi a kan bango, sannan kuma ya
Lambar Labari: 242
A shekara ta biyu ya kashe musulmi dubu goma da makaranta Kur'ani dari bakwai daga sahabbai, sannan kuma ya halatta Madina kwana uku, ya ba wa rundunar Sham damar su keta mutuncin musulmai, ya yanka iyaye da yaransu, har sai ka ga sojan Sham ya dauki mai shan nono daga hannun uwarsa ya buga kansa a kan bango har sai kwakwalwarsa ta yi tarwatsi a kan bango, sannan kuma ya tilasta mutane yi wa Yazid bai’a a kan cewa su bayinsa ne, kuma ya tsorata Madina ya firgita mutane sannan kuma ya mayar da wannan gari na Annabi mai haske zuwa ga wata fadama da ta lalace da jini kaca-kaca.
A shekara ta uku kuwa ya sanya wa Ka’aba majaujawa kuma ya rusa ta kuma ya kona ta, sannan ya rusa rukunanta sannan ya yi yaki har cikin masallaci mai alfarma ya zubar da jini har sai da ya kwarara a Ka’aba, kuma mai litttafin "Tarihin Hamis" da "Diyarul Bakari" da "Dabari" da "Ibn Asir" da Mas’udi a "Murujuzzahab" da wasunsu na daga malaman tarihi sun kawo wannan dalla-dalla cikin bayain abubuwan da suka faru a shekarar sittin da daya har zuwa sittin da uku tahijira.
Amma duk da haka sai ka samu wasu da yawa daga malaman Sunna suna nuna kuskuren wanda ya fito domin yakar Yazid kuma suna ganin fitowa domin yakarsa fita ce daga addini, kai har wasu ma suna kai da nuna kuskuren Imam Husain (A.S) shugban samarin aljanna, kamar kai ka ce lokacin da Annabi (S.A.W) yake cewa: "Hasan da Husain (A.S) su ne shugabannin samarin ‘yan aljanna" bai san zai yaki Yazidu ba ne, kuma lokacin da Annabi (S.A.W) yake cewa: "Hakika Husain (A.S) da sahabbansa zasu shiga aljanna ba tare da wani hisabi ba " kai ka ce bai san cewa zasu yaki Yazidu ba. Kai Allah ka shiryi mutanenmu! kai ka ce Ibn Arabi Almali ya fi Annabi (S.A.W) sanin makomar lamura ne da yake nuna wa Husain (A.S) makomar lamura kuma ya na umartarsa da ya zartar da hakan!
Wai zuwa ga wane kaskanci da tabewa ne wannan duniya zata kai mutanen!
Sai mu ga Gazali a cikin abin da ya kawo irin wadannan abubuwan alhalin kuwa ga shi a gabansa akwai gomomin litattafai na tarihi da suke da karfafan hanyoyi amintattu kan lamarin Yazid da ayyukansa. Sai ga shi amma a littafinsa na Ihya’ul ulum ya na cewa game da la’antar Yazid:
Idan aka ce: Shin ya halatta a la’anci Yazid domin ya kashe Husain (A.S) ko kuma ya yi umarni da hakan? Sai mu ce: Wannan bai tabbata a bisa asali ba, don haka bai halatta ba a ce shi ne ya kashe shi ko kuma ya yi umarni da hakan matukar hakan bai tabbata ba, balle kuma a la’ance shi, domin bai halatta ba a danganta wa wani musulmi babban laifi ba tare da wani tabbaci ba, har dai yake cewa: Idan aka ce yaya fadin cewa "Allah ya la’anci makashin Husain (A.S), ko kuma wanda ya yi umarni da kashe shi" sai mu ce: Abin da yake daidai shi ne a ce: Wanda ya kashe Husain (A.S) idan ya mutu kafin ya tuba to Allah ya la’ance shi .
Don Allah mai karatu shin tunaninka zai iya jure wa jin wani ya na fadin irin wadannan kalamai da suke zowa daga irin wannan mutumim!? Shin litattafan tarihi da suke hannun musulmi wadanda suka zo da wadannan lamura da suka faru da umarnin Yazid kai tsaye dukkansu ba sa iya tabbatar da ayyukan Yazid ko kuma su hukunta shi su soke shi?! A wajensa ya na ganin Yazid da ire-irensa makasa annabawa da ‘ya’yan annabawa duk suna samun dacewar tuba?! Kuma duk wata hanya ba ta iya tabbatar da sukan Yazid gun Gazali, sai dai kawai abin da yake tabbata gunsa shi ne ya ga Yazidu ya hadu da Allah ya sanya hannunsa a kan hannunsa, kuma ya yi masa magana, kuma ya kwarara masa haskensa, da gafararsa . 
Mai littafin Miftahussa’adati ya na cewa: Abubakar Nassaj ya yi shisshigi kan lamarin Gazali a kabarinsa ya fito ya na mai jirkitaccen launi, sai suka tambaye shi me ya faru. Sai ya ce: Na ga wani hannun ne na dama ya fita ta bangaren alkibla, kuma na ji wani mai shela ya na kira cewa dora hannun Muhammad Gazali a kan hannun shugaban manzanni . Sai ga irin wannan ya isa ya tabbatar da hujja a irin wannan, amma dukkan litattafan tarihi dukkansu ba sa iya tabbatar da wata hanya guda daya da zata soki Yazid!.. 
Kai lamari ya kai ga jifan alayen Annabi da fita daga kan hanya, balle kuma share fagen zaginsu. Sai ga Ibn khaldon a mukaddimarsa ya na cewa: Ahlul-baiti (A.S) sun fita daga hanya da kirkiro wata mazhaba da suka kago ta, suka kuma kadaita da ita a kan sukan wasu daga sahabbai, da kuma fadinsu na ismar imamai da kuma kawar da sabani daga zantuntukansu, kuma dukkan wannan asasi ne maras tushe.
Yana fadin haka alhalin ga hadisan Annabi (S.A.W) a game da Ahlul-baiti (A.S) a gabansa da Ibn hajar ya ruwaito a littafinsa na Sawa’ikul Muhrika  cewa: "A cikin kowane zamani akwai masu adalci daga adalai daga Ahlin gidana da suke kore wa wannan addini karkatar batattu da hanyar mabarnata da kuma tawilin jahilai, ku saurara hakika jagororinku su ne masu zuwa ga Allah, sai ku duba wanda zaku zo tare da shi (A matsayin shugaba a ranar lahira".
Haka nan ya na ganin abin da Hakim ya ruwaito a littafinsa na Mustadrak mai cewa: "Wanda ya so ya rayu irin rayuta kuma ya mutu irin mutuwata ya shiga aljanna da Ubangijina ya yi mini alkawarinta, ita ce aljannar dawwama to ya jibanci Ali da zuriyarsa bayana, hakika su ba zasu fitar da ku daga shiriya ba, kuma ba zasu shigar da ku kofar bata ba .
Amma duk da haka sai ya kira Ahlul-baiti (A.S) masu fandarewa masu bidi’a a nazarin ra’ayin Ibn khaldon, Allah ya sani, da zan zo da irin wadannan misalai da zan sanya hannu ne kawai a kan mikin da ya halakar da mu ya na kunkuna ga zukata shekaru masu yawa. Kuma irin wadannan matakai na sukan juna ba komai suke zurfafawa ba sai sabani, don haka ne ma ambatonsu wani lokaci yake zama ba daidai ba.
Marubutan musulmi suna da nauyi a kansu na tsayawa kan wannan lamuran da wadanda suka rubuta su suka mutu suka bar abin da yake bala'i a kan musulmi. Kuma wani abin mamaki a nan shi ne: shirun malamai da marubutan musulmi a kan irin wadannan maganganu na Ibn Khaldon da waninsa tare da samun dalilai masu karfi a kan cewa alayen Muhammad (S.A.W) su ne ci gaban wannan sako da ya zo da shi. Hada da cewa dukkan wannan ya zo a cikin sunnoni da aka ruwaito a tafarkin Ahlul-baiti (A.S) da ba a aiki da su alhalin ana aiki da bidi’o’in da istihsan ya zo su a tafarkin wasunsu, ka riki misali mas’alar kiran salla da aka cire wata fakara a cikinsa ta "Hayya ala khairil amal" tare da tabbatarta da cewa ya tabbata cewa ita wani yanki ne na kiran salla ta hanyoyi masu yawa.
Mai littafin Maba’di’ul Fikihu game da hakan ya na cewa: Ga yadda ake kiran salla: Allahu akbar, allahu akbar, allahu akbar, allahu akbar, ash’hadu an la’ilaha illal-Lah, ash’hadu an la’ilaha illal-Lah, ash’hadu anna muhammadar rasulul-Lah, ash’hadu anna muhammadar rasulul-Lah, hayya alassalat, hayya alassalat, hayya alal falah, hayya alal falah, allahu akbar, la’aila illal-Lah. Wannan shi ne kiran sallar da mutanen Basara da na Kufa suka hadu a kansa, kuma mutanen Sham da Misira suka bi su a kai, kuma shi ne mazhabar mutane Hijaz da Zaidiyya da Malikiyya, sai dai su a wajensu kalmar Allahu akbar sau biyu ce a kiran salla ba sau hudu ba, kuma a kan wannan ne mutanen Madina suke. Amma kalmar "Assalatu khairun minan naum" ba kiran salla ba ce na shari’a tun asali: A cikin littafin ‘Taisirul wusul"Ya zo daga Maliku cewa: Labari ya zo mini cewa mai kiran salla ya zo wajen Umar dan Khaddabi, ya na yi masa kiran sallar asuba, sai ya samu ya na bacci, sai ya ce: Assalatu khairum minan nau. Sai Umar ya umarce shi da ya sanya ta a cikin kiran sallar asuba! Don haka ne ma Abuhanifa ya ce: Wannan jumlar ana dada ta ne bayan kammala kiran salla, domin ita ba ta daga Sunna.
Amma kalmar "Hayya ala khairul amal"A mazhabar Ahlul-baiti (A.S) tana tsakanin "Hayya alal falah" da "Allahu akbar" ne. Dalilinsu kan hakan daga Sunna shi ne: Baihaki ya ruwaito a cikin Sunan dinsa cewa Aliyyu bn Husain -Zainul-abidin- (A.S) ya kasance idan ya ce: "Hayya alal falah" to ya na cewa kuma "Hayya ala khairul amal", ya na cewa haka kiran sallar farko yake.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: