bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      15:24:28
saba na jifan Shi'a da rawafidanci da kuma kiran su da wannan suna ya faru ne daga bayansaboda wasu dalilai da zamu kawo wasu a nan: Wannan
Lambar Labari: 243
Shi'awa Ba Su ake kira Rawafidawa Ba
Daga dukkan abin da aka ambata zai bayyana cewa abin da masu rubuce-rubuce suka saba na jifan Shi'a da rawafidanci da kuma kiran su da wannan suna ya faru ne daga bayansaboda wasu dalilai da zamu kawo wasu a nan:
Wannan zamani da aka fara kiran Shi'a da rawafidawa a lokacin Umayyawa ne, shi ya sa wasu litattafai suka zo suna siffanta rawafidawa da cewa wasu bangare ne su na Shi'a, ba wai Shi'a ba kamar yadda wasu suke son kawowa a wasu nassosi:
1- Muhamamd Murtada Zubaidi a Tajul Arus ya ce:
Rawafidawa dukkan wata runduna da suka bar jagoransu, kuma ana gaya wa wasu jama’a daga Shi'a Sunan rawafidawa. Asma’i ya ce: An kira su da wannan suna ne saboda sun yi bai’a ga Zaid dan Ali sannan sai suka ce ya barranta daga shaikhaini sai ya ki ya ce: Ba zai yi ba domin sun kasance wazirai ne na kakansa, sai suka bar shi suka ki shi sannan suka waste suka bar shi .
2- Isma’il dan Hammad Al’jawahiri ya fada a cikin Sihah: 
Gun kalmar nan ta Rafadha, sai ya fadi abin Zubaidi ya fada kamar ya kwafa daga asali ne .
3- Al’kali Iyad:
Al’kali Iyad ya bambanta a littafinsa na "Tartibul Madarik fi a’alami mazhabi Malik" tsakanin Shi'a da rawafidhawa, yayin da ya kwatanta mazhabar Maliku da watanta ya ce: Ba mu ga wata mazhaba da tafi rashinsu kamar malikiyya ba, domin a cikin watanta akwai jahamiyya da rawafidhawa da khawarijawa da mur’ji’a da Shi'a, sai dai kawai mazhabar Maliku, domin ba mu ji wani ya cirato irin wadannan bidi’o’i ba a cikinta .
A fili yake cewa wannan jumla ta nuna cewa Rawafidhawa ba su ne Shi'a ba, domin samun bambanci a jerin da ya kawo. Irin wannan ne muke samu a cikin maganganun waninsa na daga ma’abota sani da ilimin addinai da mazhabobi suka cirato da wannan ma’anar ta lugga, kuma dukkan mutane da suka nisanci jagoransu ana kiran su da rawafidhawa. Kuma siffanta sahabban Zaid da wannan suna ya na daga siffantasu ne da ma'anar kalmar don haka ne aka kira su da wannan suna bisa dogaro da bairn sa da suka yi yayin da suka nemi ya barranta da shaikhaini kamar yadda aka fada.
1- Wadannan da suka nemi barranta daga Zaid da sun kasance Shi'a ne to da babu makawa suna kwadayin taimaka wa Zaid ne, da kuma neman Shi'a ga shiga sahun dauki-ba-dadi da azzalumai ne domin matsayinsu ya na da alaka da matsayi irin na Zaid, kuma idan ya samu rushewa to wannan ya na nfin su ma sun rusu ke nan, musamman da yake cewa: Abokan gabarsu Umayyawa suna kashe duk wani wanda yake karkata ga alayen Abudalib hatta da a kan zato da tuhuma, to mene ne ya kai su ga kirkiro wannan bala’ai da zai kai karewar rundunar Zaid da kuma hasararsa a fagen yaki, da mutuwarsa shahidi a hannun Umayyawa. Don haka ba makawa wadannan mutane ba Shi'a ba, sai dai su wata jama’a ce da aka yi dasisarsu domin su kawo bala'i da fitina don gamawa da Zaidu da kawo masa rushewa a fagen daga.
2- Idan mun kaddara cewa akwai jama’a guda daya kebantacciya da take da ra’ayin kin shaihaini to mene ne ma’anar sanya wannan suna ga dukkan mai son Ahlul-baiti (A.S) har lamarin ya kasance an sallama shi a matsayin suna ne da ya kebanta da su kawai, don haka ne sai ga Shafi'i ya na fada a cikin baitinsa da ya shahara ya na cewa: 
Ya kai mahayin muhassabi a filin mina
Ka shelanta ga na zaune da na tsaye a taronta
A sahur idan mahajjata suka kwarara zuwa mina
Kwarara kamar tunkudar kogin Furat mai kwarara
Shin kun sani cewa Shi’anci ne mazhabata
Ni ina fadin haka kuma ban warware ba
Idan son alayen Muhammad shi ne rawafidanci
To al’ummu biyu  su shaida ni barawafide ne
Baiti na karshe na wannan baitoti da Zubaid ya fada a littafin tajul'arus a kalmar rawafidhawa da sauranta a bayanin tarihin Shafi'i ya zo a cikin litattafai masu yawa .
Kuma bayanin Imam Shafi'i da yake cewa: Idan dai son alayen Muhammad shi ne rawafidanci ya na nuna cewa ana amfani da wannan kalma a kan dukkawan wani dan Shi'a har ma wannan kalma ta rawafidhanci ta shahara gare su kuma an yi amfani da shi don kinsu, kuma a cikin wannan akwai misali masu yawa, kuma daga cikin abin da yake nuna akwai wani kaidi da ake yi wajen amfani da wannan kalma shi ne yadda aka dora wa Shi'a wannan suna kuma har suka shahara da shi, shin an yi amfani ne ta hanya mai kyau ko maras kyau.
3- Tayiwu a ce babu makawa akwai wasu mutane masu zagin sahabbai amma me ya sa suka kasance hakan, yayin da Shi'a su ba su yarda da zagi ba haka ma imamansu ba su yarda da shi ba? Amsa ita ce ba makawa mu koma zuwa ga wasu dalilai da suke tasowa sakamakon wani abu na takurawa da ya haifar da wannan lamari, kuma daya daga cikinsu shi ne:
Dalilan Zagi
a- Korewa da azabtarwa mai ban tsoro ga Shi'a da kuma abin da suka wahala sakamakon kisa ko kawarwa da batarwa bisa zato da tuhuma, mafi kyawun halin da suka samu kansu a kansa shi ne bin su da kuma yakar su da aka yi bisa lamarin tatattalin arziki da hana su Baitul Mali, da kuma dora musu haraji mai tsanani, da kuma kawar da su a siyasance. Kuma mai karatu ya na iya komawa zuwa ga tarihin Umayyawa a Kufa da wasunsu na daga garuruwan Shi'a domin ya san abin da halin ya kai su zuwa gare shi da abin da suka tuke zuwa gare shi a hannun Umayyawa na kekasar zuciya da kuma take hakkin ‘yan’adamtaka da cin mutuncin da hatta da dabbobi suna barranta daga wannan lamari da ya faru a lokuta biyu: na Umayyawa da Abbasawa .
Irin misalin wannan cusgunawa tana bukatar a samu wata hanyar lumfasawa daga wannan matsi mai tsanani kuma wannan lumfasawa domin samun sauki tana iya kasancewa ta hanya mai kyau, wani lokaci kuma tana iya kasancewa ta hanya maras kyau kamar zagi. Sai dai mu ba muna cewa yin zagin daidai ba ne a kowane hali kuwa kamar yadda ya gabata.
b- Kuma wanda ya assasa wannan lamari su ne Umayyawa su da kansu domin sun zagi Ali (A.S) a kan mimbari suka kuma zagi Ahlul-baiti (A.S) tsawon shekaru tamanin, kuma wannan yanayi ya ci gaba duk da kuwa kokarin da wannan mutum mai kirki Umar dan Abdul’aziz ya yi na ganin ya kawar da wannan zagi amma bai ci nasara ba, kuma maganganun Banu Umayya musamman Mu’awiya sun riga sun karfafa cewa sun assasa wannan zagin ne domin yaro ya girma a kansa kuma babba ya tsufa a kansa, sai aka samu wannan zagi da ake tuhumar Shi'a da shi domin su yi ramuwar gayya. Kuma idan mutum ya zurfafa sosai zai ga cewa an samukarkatar hanyar warware wannan matsala wajen wasu malaman Sunna. Muna iya ganin misalin dan Taimiyya ya na wallafa littafin nan na "Takobi zararre a kan kafirta duk wanda ya zagi Annabi (S.A.W) ko daya daga cikin sahabbai", ya na kuma kawo dalilai a kan kafirta wannan zage-zage da ake yi sai dai duk da ya san Mu’awiya ne ya assasa wannan zagin da Umayyawa da zagin da suka yi wa Imam Ali da Ahalin gidansa da la'antar su, amma bai kafrita su ba. Aliyyu dan Abidalib (A.S) dan’uwan Annabi (S.A.W) ne kuma ya bayar da komai nasa wajen yin hidima ga musulunci da musulmi amma saboda me wanda yake zaginsa ba ya kafirta? A nan ne zaka ji wani jawabi mai ban mamaki ai ya tuba kuma Allah ya gafarta masa shi ke nan wai an warware wannan matsalar!!
Duba wani misalin: Yayin da Yazid dan Mu’awiya ya hau kan hukunci na shekaru uku kawai a shekarar farko ya kashe Imam Husain (A.S) da ahlin gidan Annabi (S.A.W) kuma ya ribace iyalinsu ya kuma yanka ‘ya’yansu kuma ya yi musu abin da ko kisra da kaisar ba zasu yi musu ba.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: