bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      15:45:16
A wanan karon zamuyi Magana ne akan wasu shibuhuhi da tambayoyi Da kuma amsar su insha Allah akan abinda ya shafi azumi a ranar 10 a watan Muharram
Lambar Labari: 244
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai tsira da amincin Allah su kara tabbata ga shugaban halitta Annabinmu Annabi Muhammad (s.a.w) da iyalen gidansa tsarkaka wadanda Allah ya tsarkake daga dukkanin wani datti.
A wanan karon zamuyi Magana ne akan wasu shibuhuhi da tambayoyi Da kuma amsar su insha Allah akan abinda ya shafi azumi a ranar 10 a watan Muharram wanda aka faro shi hijarar Manzon Allah (s.a.w) tana da shekaru 61 wato tun bayan abinda ya faro na waki’ar Ashura wanda aka yiwa ‘yaya mafi kima da daraja a wurin mahaliccin sammai da kassai wato Husaini bn Aliyu bn Abi Dalib jikan Manzon Allah (s.a.w) da iyalinsa a filin karbala.
Shin Manzon Allah (s.a.w) yana karbar shari’a ne daga hannun Yahudu da Nasara ko kuma daga wajen Kafiran kuraishawa?
Shin daga ina ne Azimin Ashura ya samo Asali, daga wajen Allah ne ko kuwa Yahudu da Nasara ko kuma daga wajen Kafiran Kuraishawa?
Ta yaya Manzon Allah (s.a.w) wanda ya kasance yanada alaka da mala’ikun dake sama daban-daban wanda kuma ake saukar masa da wahayi; zai tafi wajen Yahudu da Nasara ko kuma Kafiran Kuraishawa domin su sanar dashi shari’a??
Shin dama Manzon Allah (s.a.w) yana karbar hukunci daga hannun wani banda Allah madaukakin sarki? Me yasa sai jira Yahudu da Nasara sun bashi labarin wata shari’a ta yadda har zasu bashi umarni akan yin Azumin Ashura? Shin ashe wannan baici karo da Ismar Manzon Allah (s.a.w) da iliminsa yake daga wurin Ubangiji madaukakin sarki ba?
Shin hankali zai hukunta cewa Manzon Allah (s.a.w) zai takalidi da Yahudu da Nasara sannan kuma ya umarce sahabbansa suma suyi koyi dasu bayan kuma ya hane su da bin sunnar Ahlil-kitab?
Manzon Allah (s.a.w) ya kasance wanda yake da sako daga sama kuma yake da ilimi daga wajen Ubangiji wanda baya furta komai sai anyi masa wahayi; to ta yaya zai saurari Yahudu da Nasara harma da Kafiran Kuraishawa domin su zo su koyar dashi ibada? Ko kuma hadisan da suka zo akan batun ashura suna kore ismar Annabi ne kawai ba wani abu ba?
Yanzu a ce a yanka dan Annabi a raba kansa da jikinsa mai tsarki sannan a tsire kansa a sanda ana daga shi sama ana yawo dashi gari-gari, sannan a kashe iyalansa da mataimakansa  da Sahabbansa a kama matansa a matsayin ganimar yaki ayi kaca-kaca da gidan wahayi kai harma jakin gidan wahayi bai tsiraba a ranar 10 ga watan Muharam; sai kuma a samu wani musulmi wai dai dai irin wannan ranar ya rufe idonsa wai yace yau yana Azumi domin Yahudawa suna yin Azumi a irin wannan ranar domin murnar tseratar da Annabi Musa (a.s) daga hannun fir’auna da Allah yayi a irin wannan ranar, shin yanzu hankali zai hukunta haka? Shin yanzu farincikin tseratar da musu har zai sa ka manta da musibar da ta sami Husain ranar Ashura??
Ko kuma kuna azumin ashura ne saboda haihuwar Annabi Isa (a.s)? sannannen abune cewa haihuwar Annabi Isa (a.s)  tana daga cikin manyan mu’ujizozi a tarihi shin ashe ba mune mafi cancanta da Isa akan kiristoci ba ku Ahlussunna kamar yadda kuke fada?
Shin wai ba ance dalilin yin azumin ashura ba shine saboda yahudawa suna yin azumin ranar ba? To me yasa yanzu kuma yahudawan basa yin wannan azumin?
Idan hijirar zababbeen Allah Muhammad dan Abdullahi (s.a.w) ta kasance ranar litinin 8 ga watan rabi’u auwal, shekarar farko ta hijira, wacce tayi dai-dai da 20 ga watan September, shekara ta 622 miladiyya, haka kuma ya yi dai-dai da 10 ga watan Tashri, shekara ta 4383 Ibriyya, wacce itace ranar da yahudawa suke azumin; to ta ya ya zai zama ya yi dai-dai da 10 ga muharram din ko wace shekara???
Shin akwai wata alama akan wannan azumin na ashura wanda aka nakalto daga al’adon jahiliyya? Me yasa malaman lugga sukayi ittifaki kan cewa tabbas ashura sunane da aka samar dashi cikin musulunci babu shi kafin musulunci shin maganar su abin jefarwa ce kuwa??
Shin abinda yafi bai kamata muce azumin ashura da falalarsa da ake fada wata bidi’a bace da aka kaga bat un lokacin da aka kashe Husain (a.s) ba???
AZUMIN ASHURA TSAKANIN HANKALI DA SHARI’A.
Ga abinda Al-bani yake cewa:
{ و قد نقل المناوى عن المجد اللغوى أنّه قال: ما يروى فى فضل صوم عاشوراء والصلاة فيه والانفاق والخضاب والادهان والا كتحال بدعة ابتداعها قتلة الحسين ري الله عنه        
Hakika dukkanin abinda aka ruwaito (wato hadisai) akan falalar yin azumi, da sallah, cika-ciki…  a ranar ashura bidi’ace da kasan Husaini  ( R.A ) suka kirkira.
Al – Bani yaci gaba da cewa:
{و من الممكن  أن يكونوا من أعداء الحسين رضي الله عنه الذين وضعوا الأحاديث فى فضل الاطعام والاكتحال وغير ذالك يوم عاشوراء معارضة منهم للشيعة الذين جعلوا هذااليوم يوم حزن على الحسين رضي الله عنه لأن قتله كان فيه ولذالك جزم شيخ الاسلام ابن تيمية رحمة الله بأن هذاالحديث كذب وذكر أنّه سئل الامام أحمد عنه فلم يره شيئا وأيد ذالك بأن أحدا من السلف لم يستحب التوسعة يوم عاشوراء وأنّه لا يعرف شئ من هذه الأحاديث على عهدالقرون الفاضلة وقد فصل القول فى هذافى الفتا وى"    فراجعه.       Gaskiyar Magana shine zai iya yuwa makiyan Husaini (r.a) ne suka kirkiro hadisan da suke Magana akan falalar  cika-ciki da ado dama wanin wannan a ranar Ashura, don kishiyantar yan shi’a wadanda suka maida wannan rana ranar bakin ciki akan Husaini (r.a), saboda an kashe shi ne a irin wannan ranar, saboda hakane ma sheikul Islam ibnu Taimiyya Allah ya yi mashi rahama ya karyata wadannan hadisan kuma an tambayi Imamu Ahmad akai baiga wani hadisi da ya inganta  akan haka ba sannan kuma magabata basa ganin cika-ciki a ranar ashura ba, ba wanda yasan da wannan hadisin ba hakika Ibni Taimiyya ya yi cikakken bayani a fatawa a koma mashi(1) .
(Gaba daya ta’alikin da akayi a Fikhussunna: Muhammad Nasiruddin Al-bani: maktabatul islamiyya, darur raya wajen yadawa kenan: bugu na uku.
Zamuci gaba da amsa tambayoyin da suka zo a sama a kashi na biyu insha Allah, aminci ya tabbata ga wanda sukabi shiriya.
Aliyu Abdullahi Yusuf: What’sapp, Telegram, Istgram, da sauran Social Media Number: +2348037493872. Ko kuma Email address: y.aliyuabdullahi@yahoo.com.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: