bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      15:54:50
sun kasance suna Azumin Ashura a lokacin Jahiliya, Manzon Allah (s.a.w) ya kasance
Lambar Labari: 245
Kashi na biyu cigaba daga kashi na farko Magana akan azumin Ashura.
SHIN DAGA INA AZUMIN ASHURA YA ZO? KUMA ZA A IYA BARINSHI?
Ga abinda ya zo daga Sahihu Muslim, a cikin babin azimin ashura: Zuhair  dan Harb ya bamu labari, Harir ya bamu labari, daga Hashim dan Urwa, daga Babanshi, daga A’isha ta ce: Kuraishawa sun kasance suna Azumin Ashura a lokacin Jahiliya, Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana yin shi shima, yayin da ya yi Hijira zuwa Madina sai ya yi azumin kuma ya yi Umarni da ayi azumin, ya yin da aka wajabta Azumin watan Ramalana sai ya ce: Wanda yaso ya yi wanda kuma baya so ya barshi(1) .
{  حدّثنا زهير بن حرب, حدّثنا جرير عن هشام بن عروة عن أبيه عن عائشة (ر) قالت كانت قريش تصوم عاشوراء فى الجاهليّة وكان رسول الله (ص) يصومه فلّما هاجر الى المدينة صامه وأمر بصيامه فلّما فرض شهر رمضان قال: من شاء صومه ومن شاء تركه .             
Shin yanzu dan Allah hankali zai yadda cewa Annabin Allah wanda Allah madaukakin sarki yake yi wahayi a ce wai shine zai kwaikwayi mutanen Jahiliya akan wani aiki ba tareda an saukar masa wannan aikin ba, wanda ya zo domin shiryar da mutane sai kuma gashi ya buge mutanen ne ke shiryar da shi, shin wannan shine wanda Allah ya fada mana cewa baya yin ko wace irin Magana sai anyi masa wahayi ya ku ma’abota hankali?
YAHUDAWA NE SUKA SANAR DA ANNABI  ( S.A.W ) AZUMIN ASHURA:
SHIMA AKAN WANNAN GA HADISI DAGA DAI SAHIHU MUSLIM DIN:
Ibn Abu Umar ya bani labari, Sufyan dan Ayyuba ya bamu labari, daga Abdullahi dan Sa’id dan Jubair, daga Babansa, daga dan Abbas (r.a) Tabbas Manzon Allah (s.a.w) ya shiga Madina sai ya samu Yahudawa suna azumin ranar Ashura sai Manzon Allah (s.a.w)  ya ce musu: wannan kuma wace rana ce kuke azumi cikinta? Sai suka ce ai wannan ranace mai girma acikinta ne Allah ya tseratar da Musa ( wato Annabi Musa ) da mutanensa kuma ya hallaka Fir’auna da mutanensa sai musa ya yi azumi saboda godiya ga Allah muma sai muke yin azumin wannan rana. Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: mune mukafi ku cancanta da Musa sai Manzon Allah (s.a.w) ya yi azumin kuma ya yi umarni da yin azumin(2) .
وحدّثنى ابن عمر حدّثنا ابن سفيان عن أيّوب عن عبد الله ابن سعيد بن جبير عن أبيه عن ابن عبّاس (ر) أنّ رسول الله (ص) قدم المدينة فوجد اليهود صياما يوم عاشوراء فقال لهم رسول الله (ص) ما هذا اليوم الذى تصومونه؟ فقالوا هذا يوم عظيم أنجى الله فيه موسى  وقومه وغرّق فرعون وقومه فصامه موسى شكرا فنحن نصومه. فقال ر سو ل الله (ص) فنحن أحق وأولى بموسى منكم . فصامه رسول الله (ص) وأمر بصيامه.                  
Dan Allah ba’abota hankukla ku duba wannan Magana ku gani mana, Manzon Allah (s.a.w) wanda yake da alaka da sama wanda Allah madaukakin sarki ke saukarma da wahayi wanda mala’iko ke kaiwa da komuwa a gidansa shine wai zai tafi wajen Yahudawa domin neman sanin wani abu, shin hankali zai yadda da wannan? Manzon Allah ya tsaya jiran Yahudawa su sanar dashi, wai ya shiga Madina sai ya gansu suna Azumin wannan ranar sai ya tambaye su meyasa suke yin wannan azumin, sai suka bashi labari saboda Allah ya tseratar da Annabi Musa ne, kawai sai ya ce ai munfi ku cancanta da Musa saboda haka kawai sai ya fara yin azumin wannan rana kuma harma ya umarci sahabbansa da yin wannan azumin dan Allah wannnan wace irin kwaba ce? Shin daman Manzon Allah (s.a.w) daga hannun Yahudawa yake karbar shiri’arsa? Shin daman Annabi (s.a.w) yana yin hukunci batareda umarnin Allah madaukakin sarki ba? Miyasa sai ya saurari Yahudawa domin su bashi labari sannan wai har ya umarci mutane da yin wannan azumin, shi ashe wannan ba wata kiyana bace ga Manzon Allah (s.a.w) da kuma rage kimarsa daga wajen Ubanjigi mai girma ba?
SAI KUMA HADISIN DA YAKE NUNI DA CEWA MANZON ALLAH (S.A.W) BAIMA SANI MUSULMAI NE KUKA SANAR DA SHI AKAN AZUMIN.
Shima dai gashi daga hadisin daga Sahihu Muslim din dai: Hasan dan Aliyul Hulwani ya bamu labari, Baban Maryan ya bamu labari, Yahaya dan Ayyuba ya bamu labari, Isma’il dan Amayya ya bani labari, tabbas yaji Aba  Gadafan dan Darifil Murri, yana cewa: naji Abdullahi dan Abbas (r.a) yana cewa: lokacin da azumin Ashura ya wuce Manzon Allah (s.a.w) bai yi azumin ba kuma bai umarci ayi azumin ba, sai Sahabbai sukace masa ya Manzon Allah (s.a.w) Tabbas ranace da Yahudawa da Nasara suke girmamata. Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: idan Allah ya kaimu shekara mai zuwa in Allah yaso zamu azimci ranar tara 9. Sai ya ce kafin shekarar ta zagayo Manzon Allah (s.a.w) ya yi wafati(3) .
وحدثنا الحسن بن عليّ  الحلوانى , حدّثنا ابن أبى مريم حدّثنا يحيى بن أيوب حدثنى اسمائيل بن أمنيّة أنه سمع أبا غطفان بن طريف المريّ يقول سمعت عبدالله بن عبّاس (ر) يقول حين صام رسول الله (ص) يوم عاشوراء وأمر بصيامه قالوا يا رسول الله (ص) انّه يوم تعظّمه اليهود والنّصارى فقال رسول الله (ص) فا ذا  كان العام المقبل ان شاء الله صمنا اليوم التّاسع. قال فلم يأت العام المقبل حتّى توفى رسول الله (ص).           ّ
Dafarko dai Manzon Allah (s.a.w) wanda  shine shugaban halittun Allah baki daya kuma shine mafi sanin kuma acikin dukkanin halittun Ubanjigi madaukakin sarki shine wai musulmai zasu taro sai su bashi labarin azumin Ashura shi bata tareda yasani ba kawai sai ya umarci al’umma da yin wannan azumin alhali ma shi bai ma san me yasa ake yin azumin ba, saida musulmai suka zo wajensa suna cewa ya Rasulullah shin Ubanjigi mai shiryar da kai yin azumin Ashura ba da kuma Muhimmancin wannan ranar, ranace fa da Yahudawa da Nasara ke matukar girmamata, wai sannan sai Manzon Allah (s.a.w) ya fadaka sannan ya ce: oh yanzu kunsanar dani abinda bansani ba, insha Allah idan shekara ta zagayo zamuyi azumin. Dan Allah  wannan wane irin cin mutuncine ga shugaban halitta wanda shine aka saukarma da Risala daga sama wanda iliminsa yake kai tsaye daga Maliccin bayi wanda ake yiwa wahayi wanda baya wata Magana face wayice daga Ubangijinsa shine kuma zai tsaya sauraron Yahudawa ko kuma mutane daga cikin Musulmai su zo su bashi labarin wata ibada wacce Allah madaukakin sarki bai snar dashi ba, shin yanzu wannnan shine Annabinku ya ku al’ummar musulmai?
Zamuci gaba insha Allah a kasha na uku duk dai akan wannan Magana ta azumi a ranar Ashura.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: