bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      15:57:19
tsakanin Annabinmu Annabin tsira Muhammad dan Abdullahi (s.a.w) wane ne ahakku muyiwa biyayya?
Lambar Labari: 246

Kashi na uku magana akan Azumin Ashura.
Kamar yanda muka kawo hadisai daban-daban akan wannan maudu’i na Azumi a ranar ashura wanda tundaga farfo ma irin su Nasiruddin Albani ya karyata irin wadannan hadisai inda mukaga yana cewa makiyan Husaini sun kirkiro irin wadannan hadisanne ba don komai ba sai dan kishiyantar Yan shi’a wadanda suke raya wannan rana ta Ashura kuma suke yin kuka a cikinta saboda musafar data sami Husaini (a.s).
Sannan kamar yadda bayani ya gabata a cikin tambayo yin da akiyi shine: shin hankali zai yanda cewa Manzon Allah (s.a.w) wanda shine Allah ke saukarwa wahayi daga samu wanda baya magana saida Umarnin Ubagijinsa shine yau kuma zai yi koyi da Hahudu da Nasara akan Azumin Ashura?
Sannan koda dama hakan ya faru cewa a ranar Ashura ne aka tseratar da Annabi Musa (a.s) da Jama’arsa kuma aka halakar da Fir’auna shima da Jama’arsa, shin tsakanin Annabinmu Annabin tsira Muhammad dan Abdullahi (s.a.w) wane ne ahakku muyiwa biyayya? Shin taya Annabi Musa (a.s) murnar tseratar dashi da Allah da kuma halakar da Fir’auna da akayi ko kuwa taya Manzon Allah (s.a.w) bakin cikin kashe masa Dad a akayi? 
  Yanzu a ce a yanka Dan Manzon Allah (s.a.w) sannan a sa Dawaki suyi sukuwa akan jikinsa mai tsarki sannan a yanke kanshi a tsere kansa a jikin mashi a daga ana yawu dashi Gari-Gari sannan a kashe Ahlin gidansa da mataimakansa da Sahabbansa sannan a kama matan Gidan wahyi da sunan bursunonin yaki ana tafiya dasu ana duka aje dasu har wajen Yazidu fasiki mashayin giya, sannan duk da wannan sai Musulmi ya rufe idonsa wai ya ce yana Azumi a irin wannan ranar, saboda me yake azumin a irin wannan ranar wai dalilinsa shine a irin wannan ranar Yahuduwa suna azumin wannan ranar saboda a irin ranar ne Allah ya tseratar da Annabi Musa daga hannun Fir’auna. Shin dan Allah ta yaya za a yi farincikin tseratar da Annabi Musa alhali an kashe Imam Husaini (a.s).
Wai ko kuma dalilin shine saboda kiristoci suna azumi a irin wannan ranar saboda wai a ranar ne aka Haifi Annabi Isa (a.s) kuma wai dalilin shine haihuwar Annabi Isa (a.s) kuma tana daya daga cikin mafi girman Mu’ujiza wacce Tarihi ya taba gani kuma hakan shin ashe ba mune ahakku da Isa (a.s) akan kiristoci ba kamar yadda Ahlussunnah suke fada.
Shin yanzu wannan ya isa ace dalili ne da zaisaayi murna ranar da aka kashe Dan Manzon Allah (s.a.w) wwato a bar bakin kicin abinda ya sami Annabi a ko kuma farincikin haihuwar Annabi Isa (a.s). ko kuma kamar yadda muka yi mayani a baya idan Hijirar Manzon Allah (s.a.w) ta kasance ranar Litinin 8 ga watan Rabi’u Auwal shekarar farko ta hijira, wacce tayi dai dai 20 ga watan satumba,  shekara ta 622 Miladiyya, haka kuma ya yi dai dai da 10 ga watan Tashri, shekara ta 4383 Ibriyya, wacce itace  ranar da Yahudawa ke azumin Ashura din, to tambaya ta yaya zai yi dai dai da 10 ga watan Muharam na ko wace shekara? Wannan kawai karyace da aka kirkiro kamar yadda aka saba kirkirowa Annabi karya a wurare daban-daban, sannan kuma idanma gaskiya shin wane abune mafi girma a tsakanin ababe duga biyu ga al’ummar musulmai, shin murana da tseratar da Annabi Musa daga Hannun fir’auna da kuma murnar ranar da aka haifi Annabi Isa (a.s) ko kuwa musibar da ta samu Annabin mu Manzon Allah (s.a.w) ta kashe masa da akayi mafi munin kisa a ranar Ashura?
 Shin yanzu ya kyautu ace musulmi ya iya mantawa da irin wannan ranar da akayiwa ya yan gidan Manzon Allah (s.a.w) kisan gilla a sahara babu mataimaki? Babu shakka duk wanda ya yi irin wannan tunanin ma ya kamata ya binkici imaninsa da kuma soyayyarsa ga Manzon Allah (s.a.w) shin ashe ba Manzon Allah (s.a.w) ne yake cewa ba: { Husaini daga gareni yake kuma Nima da Husaini nake} { Alhasani wal Husaini sayyida shababi ahlil janna} shin yanzu wace amsa zamu bawa Annabi kenan a ranar kiyama a lokacin da zai tambaye mu cewa: ya kuka kula da ya yan gidana wace amsa zamu bawa Manzon Allah (s.a.w)?
Magana ta gaskiya ya kamata mutsaya mu kula kuma mu karanta tarihi mubishi da kyau idan bamu sani ba saboda gudon fadawa cikin halaka. Domin kuwa anyi sake-sake cikin tarihi da kirkiro tatsuniyoyi domin kawo rudani cikin tarihin musulunci matukar bamuyi taka tsan-tsan ba tofa za a kaimu a baro a cikin tarihin wannan addinin namu na musulunci. Karmu  mudauka cewa wai munyi imani da abinda muke yi baza mu nemi ilimi ba, wannan shine babban kuskure a rayuwa. 
Saboda haka Magana ta gaskiya shine Yahudawa basa wani azumin Ashura saboda tarihinma ya sabawa abinda wadancan ruwayoyin suka dogara dasu. Hakama Nasara ba wani azumin Ashura da suke yi suma lissafin baiyi dai dai da lokacin da aka ambata ba wanda aka ce wai a lokacin sukeyin Azumin Ashura, kamar dai yadda bayani ya gabata a baya.
       AZUMIN ASHURA A WAJEN YAN SHI’A.
An tambayi Imam Sadik (a.s) akan azumin ashura sai ya ce: duk wanda ya yi azumin makomarsa irin makomar ibnu marjana ce da kuma ali Ziyad, sai aka ce: wata ce.
Mafiya yawancin shi’a sun tafi akan cewa yin azumin Ashura ba wai mustahabi bane, kamar yadda ake dangana mafi yawan ruwayoyi da hanin yin azumin Ashura kuma mu ya abinda Imam Ridah (a.s) ya fada ya isar mana dan gane da azumin wannan ranar. An tambayi Imam Ridah (a.s) dan gane da azumin ranar Ashura sai ya ce: Shin dan gane da azumin Ibnu Marjana kuke tambayata? Wannan ranar azumi ce ga iyalen Ali Ziyad saboda kashe Husaini (a.s)(1) .
A wani hadisin na daban kuma dan gane dai da azumin Ashura din  Imam (a.s) yana cewa: Bah aka bane na rantse da Ubangijin Baitul Harami, ba ranar azumi bace, ba wata rana bace sai ranar bakinciki da musiba wacce ta shiga wajen ahlin sama da ahlin kasa da kuma gaba daya muminai, sannan kuma rana ce ta farin ciki da walwala ga Ibnu Marjana da kuma ali Ziyad da kuma mutanen Sham(2) .
Saboda haka Magana akan Azumin Ashura zamu iya cewa abune wanda aka kirkire shi bayan kisan gilla da aka yiwa ya yan gidan Manzon Allah (s.a.w). walhamdu lillahi rabbil alamin. Amincin Allah ya kara tabbata ga wanda suka ga shiriya kuma suka bita.

Aliyu Abdullahi Yusuf: What’sapp, Telgram, Istgram, da sauran Media Number: +2348037493872. Ko kuma email address: y.aliyuabdullahi@yahoo.com.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: