bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      16:05:22
Kur’ani zancen Allah ne kuma mabubbugar hikimarsa da iliminsa, kuma ayoyinsa masu girma suna nuna mana girman Ubangiji madaukaki. Kur'ani wata taska ce mai girma da kima
Lambar Labari: 247
Gaskiya Da Rikon Amana
Koya wa yara gaskiya da rikon amana yana daga cikin ayyukan da suka hau kan iyaye, domin wannan yana daga mafi muhimmancin ayyukan da suka doru a kansu na tarbiyyantarwa tun suna kanana. Don haka ne ya hau kan iyaye su kiyaye wannan al’amari mai muhimmanci domin samar da zuriya da al’umma mai addini mai tsarki, mai tausayi da tunani, mai hangen nesa.
Dukkan al’ummar da ba ta samu irin wannan tarbiyya ba to ma’aikatanta da jagororinta zasu kasance maha’inta, kuma wannan zai sanya ba zasu taba cin nasarar rayuwar duniya ba, domin ci gaba da yalwata da ‘yancin al’umma ya doru ne bisa samar da al’umma mai rikon amana da gaskiya.
  
Koyar Da Kur’ani
Kur’ani zancen Allah ne kuma mabubbugar hikimarsa da iliminsa, kuma ayoyinsa masu girma suna nuna mana girman Ubangiji madaukaki. Kur'ani wata taska ce mai girma da kima maras iyaka ga dukkan musulmi da ma al’ummar duniya baki daya.
Wani abu muhimmi a nan shi ne; Kur'ani wani alkawari ne tsakanin Ubangiji da mutane, don haka ne ya hau kan iyaye su koyar da ‘ya’yansu ilimomi masu kima da suke cikin wannan littafi mai girma wadanda suke raya al’umma, ta yadda dukkan ma’anoninsa da abubuwan da ya kunsa a dunkule zasu kasance a cikin kwakwalensu a matsayin wani tunani da sani da ilimi mai daraja .

Soyayyar Alayen Annabi (s.a.w)
Tarbiyyantar da soyayyar Ahlul Baiti (a.s) ga yara yana daga cikin mafi muhimmancin nauyin da ya hau kan iyaye, da akwai hanyoyi masu yawa da na koyar da soyayya ga Ahlul Baiti (a.s) a cikin tarihinsu da koyarwarsu da zantuttukansu da ayyukansu wadanda suke masu yawa a cikin littattafai. Sannan a rika sanya wa ‘ya’ya sunayen Ahlul Baiti (a.s) da kai su wajen ziyararsu da majalisosin da ake yin a ranakun haihuwarsu ko shahadarsu, hada da kula da abincin halal ga yaro, da ambaton falalolin Ahlul Baiti da sanar da su matsayinsu (a.s).
Sannan da yin salati yayin samun wani abu na farin ciki ta yadda zamu rika tunasu, da yi musu salati yayin faruwar wani abu domin tunawa da su ya dawwama a kwakwalensu, kuma harsunansu su nuna da ambatonsu, rayuwarsu ta cakuda da tunaninsu.
A wata ruwaya ya zo cewa: "Ku ladabtar da ‘ya’yanku a kan abubuwa uku; son annabinku, da son ahlin gidansa, da karanta Kur'ani .
Soyayya da kauna ga Ahlul Baiti (a.s) soyayya ce da kauna ga Allah madaukaki da manzonsa (s.a.w) , kuma damfaruwa ne da abubuwa masu kima na Ubangiji da koyarwar addini mai girma, kuma kaiwa ga mafi daukakar matsayi ne na kamala da cikar mutumtakar dan Adam, kuma idan babu wannan soyayyar to kaiwa ga wannan kamala ba zai yiwu ba har abada, kuma idan babu ita ayyukan da mutum musulmi yake yi na alheri ba zasu karbu ba a wajen mai girma Ubangijin talikai kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyin . Don haka ne ma kusanci zuwa ga Allah madaukaki da isa zuwa ga sa’adar duniya da lahira ba zai yiwu ba sai da soyayya ga Annabi Muhammad da alayen Muhammad (s.a.w) domin soyayyarsu an hada ta tare ne.


hfazah@yahoo.com
Haidar Center (HAIDARCIP)
Text Only or ; 1-WhatsApp 2-Tango 3-Viber 4- Telegram, etc: (+234 803 215 6884)
Web Site: www.haidarcenter.com

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: