bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      16:08:20
Al'ummar da take mai lafiya mai annashuwa ita ce wacce take da daidaikun mutane da suke da nishadi da karfin himma
Lambar Labari: 248

Motsa Jiki Da Yawon Shakatawa
Samar da yanayin farin ciki da annashuwa da motsa jiki ga yara da wajen wasanni yana daga abubuwa masu muhimmanci matukar gaske, kuma daya ne daga bukatun yara masu matukar amfani. Don haka ya hau kan iyaye su karfafi ruhi da jikin yara da bayar da muhimmanci kan wannan mas'ala ta motsa jiki, annabin rahama (s.a.w) a cikin maganarsa madaukakiya ya bayar da muhimmanci kan wannan mas'ala ta yara a a cikin abubuwan da ya lissafa da suka hada da; koyar da littafin Allah, da koyar da harbi da iyo a ruwa, da kuma barin gadon dukiya ta halal .
Al'ummar da take mai lafiya mai annashuwa ita ce wacce take da daidaikun mutane da suke da nishadi da karfin himma, kuma ya zo a cikin dabi'un imamai (a.s) game da wasanni da motsa jiki cewa suna daga hanyoyin watayawa da karfafa ruhi da jiki wadanda suke kawo habaka da ci gaba, don haka ne a fili yake cewa; muna iya gani shari'a ba ta gafala daga wannan al'amari mai muhimmanci ba.


Zabar Aiki Mai Dacewa
Rashin aikin yi bayan lalata karfin da Allah ya ba wa samari da yake yi, haka nan yana sanya su jin kaskanci da lalaci, sannan ya mayar da shi cima-zaune dan kashe wando, wannan al’amari ne mai taba tunani da rayuwar samari matuka, sannan kuma wani bala’i ne na al’umma. Muna iya gani sau da yawa wannan yakan kai ga nau’o’in fasadi iri-iri na kyawawan halaye ne ko na zamantakewa.
Saurayi matashi dole ne ya kasance mai sadaukarwa da karfinsa ga al’umma, don haka ne saurayi mai kishin al’umma sai ya yi kokarin zabar aikin da zai yi domin ya bayar da gudummuwa cikin al’ummarsa, kuma ya taimaka wa kansa da danginsa, da al’ummarsa da kasarsa. Kuma iyaye suna da rawar da zasu taka mai girma wajen ganin sun taimaka masa samun aikin da yake na halal a shari’ance.

Taimakawa Don Yin Aure
Aure wani abu ne mai daraja a cikin al’umma wanda musulunci ya shar’anta shi, ya dauke shi a matsayin ibada mai girma, da yin aure ne saurayi zai taka matakin farko na rabuwa da son kansa da komawa zuwa ga son waninsa, domin idan ya yi aure a lokacin ne zai yaye kansa daga son kansa da kebantar komai nasa da kansa domin ya sanya shi a hannun waninsa wanda yake ita ce matarsa. Kuma ta hanyar shiga wannan sabuwar marhalar ne zai cike tawayar da take tattare da shi yayin zaman gwauranci.
Sannan kuma ta hanyar aure ne za a kiyaye samuwar manyan gobe masu albarka, da samun nutsuwar ruhi da zama waje daya, da kammaluwa da kuma biyan bukatun sha’awa ta hanyar halal, da samun lafiya cikakkiya, da amincin al’umma, da kuma biyan bukatun nan da suke damun tunanin rayinsa.
Manzon rahama mai tsira da aminci yana cewa: "Duk wanda ya yi wa ‘ya aure, kuma ya aika ta gidan mijinta, to Allah zai sanya masa hular sarauta a kansa ranar kiyama .

Yin Wa’azi D a Shiryarwa
Yin wa’azi da nasiha da shiryarwa suna daga mafi muhimmnacin al’amuran tarbiyya ga yara, kuma iyaye suna da babbar rawar da zasu taka a nan domin shiryar da saurayi ga zabi nagari. Muna iya gani da farko rayuwar samari da ‘yan mata cike take da matsalolin rayuwa, kuma akwai masu rashin halaye nagari domin bata su. Don haka ne ya zama wajibi kan iyaye su shiryar da su ga tafarkin kwarai da hanyar shiriya, kuma su yi amfani da tajribar rayuwa da suke da ita domin ganin sun koyar da ‘ya’yansu ita.
Su sani da yin nasiha da shiryarwa da gargadi da tsoratarwa ga Allah suna iya sanya ‘ya’yansu tashi cikin shiriyar da ake bukata garesu da al’ummarsu.
kuma ta hakan suna iya kautar da ‘ya’yansu daga fadawa tafarkin kauce hanya da barna, don haka ne ma Allah ya kawo mana misalin nasiha ta uban nan mai tausayi ga dansa a cikin Kur’ani mai girma a surar nan ta Lukman, kuma ya sanya mana wannan a matsayin kyakkyawan abin koyi ga iyaye da ‘ya’yansu .

hfazah@yahoo.com
Haidar Center (HAIDARCIP)
Text Only or ; 1-WhatsApp 2-Tango 3-Viber 4- Telegram, etc: (+234 803 215 6884)
Web Site: www.haidarcenter.com

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: