bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      16:09:10
Ubangiji madaukaki yana cewa: "Hakika mun ba wa Lukman hikima ka godewa Allah
Lambar Labari: 249
Wasiyyar Luk'man (a.s) ga D'ansa

Nasihohin Lukman Hakim (a.s) ga Dansa - 1
Zamu so kawo karashen wannan magana game da tarbiyyar yara da nasihohin Lukman (a.s) ga dansa wadanda suka tattaro dukkan hikimomi masu yawa da amfani a dukkan janibobin rayuwar mutum ta duniya da lahira.
Ubangiji madaukaki yana cewa: "Hakika mun ba wa Lukman hikima ka godewa Allah wanda ya gode yana godewa ne ga kansa kuma wanda ya butulce hakika Allah mawadaci ne abin yabo. Yayin da Lukman ya ce da dansa yana mai yi masa wa'azi Ya dana! Kada ka yi shirka da Allah (an ce dansa ya kasance mushriki, bai gushe ba yana yi masa wa'azi har sai da ya musulunta) hakika shirka zalunci ne mai girma ".
Wannan munin nata kuwa saboda ita shirka daidaita mafificin samammu ne da mafi kaskancinsu ce, da kuma daidaita mai ni'imtarwa mawadaci tsantsa da kuma mai ni'imtuwa (wanda ake ni'imtarwa) matalauci tsantsa. Don haka ne sai Lukman (a.s) ya fara gabatar da wa'azi game da hanin shirka domin tauhidi shi ne asalin wa'azi, kuma shirka zalunci ne wanda Allah ba ya yafe shi idan an mutu ba a tuba ba sabanin sauran zunubai. "Ya dana, ka sani cewa" wato; Dabi'a mummuna ko kyakkyawa "idan tana kwatankwacin kwayar Khardal"  wato nauyin aikin, shi Khardal wani tsiro ne na ciyayi da yake fitowa a gonaki da kuma gefen hanya, kwayarsa karama ce sosai kuma launinsa baki ne kuma ana buga misali da shi a kankanta ana cewa ba ni da koda kwayar khardal, kuma ana amfani da ita a magani da kuma kansasa abinci, "To zata kasance a sahara ne ko samammai ko kasa" wato wannan dabi'ar koda tana mafi boyuwar waje kuma mafi taskatuwar wuri kamar cikin duwatsu wacce tafi kowane dutse tsauri ko mafi nisan waje to "Allah zai zo da ita" ya yi hisabinta, "hakika Allah mai tausayi ne" a iliminsa da abin da ya boyu "kuma masani" da dukkan komai.
"Ya dana, ka tsayar da salla" wato domin kamalar kanka "ka yi umarni da kyakkyawa ka yi hani da barin mummuna" wannan kuma domin kamalar waninka "ka yi hakuri domin abin da ya same ka" na bala'ai da wahala da cutarwa a kan hanyar umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna "hakika wannan" hakurin "yana daga manyan al'amura" wanda ya kamata a dage a kansu. "kada ka karkatar da kanka ga mutane" ai ka karkatar da kanka kana barin mutane don wulakaci, an ce; Yana nufin kada ka karkato zuwa garesu don kwadayin abin hannunsu . Daga Imam Ja'afar Sadik (a.s) ayar tana nufin: Mutane su kasance daya ne a wajenka a sani .
 "Kada ka yi tafiya a bayan kasa kana mai jiji da kai, hakika Allah ba ya son mai takama mai alfahari". Daga Annabi (s.a.w) yace: Wanda ya yi tafiya a kan kasa yana mai takama kasa zata la'ance shi da abin da yake karkashinta da abin da yake kanta . "Ka tsakaita a tafiyarka" wato tsakanin takama da kuma kaskantar da kai, wato ba labo-labo ba, ba kuma gudu-gudu ba. Shi ya sa ya zo a cikin hadisi cewa saurin tafiya yana tafiyar da kwarjinin mumini . "Kuma ka kaskantar da sautinka, hakika mafi munin sauti shi ne muryar jaki". Wato kada sautinka ya yi kasa kuma kada ya yi sama domin mafi munin sauti sautin jaki, wannan kuma misali na shesshekarsa da daga sauti sama wannan kuma misali ne mai kyau da ake nufin irin jinsin abu ba wai daidaikunsa ba.
Daga Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Ita (mafi munin murya) atisshawa da murya mai muni, da mutumin da yake daga sautinsa da magana dagawa mai muni sai dai idan ya kasance mai kira ne ko yana karanta Kur'ani .
Ko kuma a gaban makiya saboda fadinsa madaukaki: "Masu tsanani ne a kan kafirai". kamar yadda ya kamata ko ma mustahabbi ne ladani ya kasance mai murya madaukakiya domin a samu isar da sakon sanarwa, a kan wannan kuwa hadisan Ahlul Baiti (a.s) sun zo game da hakan .
Ya kamata dalibi ya kasance mai sassauta muryarsa kasa-kasa daga muryar malaminsa da babansa da ladabi kuma ba kyau daga murya a kan muryarsu.
Lukman ya kasance ya ce da dansa: Ya dana! Yaya mutane ba sa tsroron abin da aka yi musu alkawari, kuma alhalin kullum suna rage rayuwarsu, yaya wanda yake da ajali ba ya tanadi saboda abin da ake yi masa alkawari, Ya dana!; Ka riki duniya guzuri kada ka shiga cikinta shiga da zai cutar da lahirarka, kuma kada ka ki ta sai ka kasance naunyi a kan mutane. Ka yi azumi da zai yanke sha'awarka, kada ka yi azumin da zai hana ka yin salla, ka sani salla ta fi azumi a wajen Allah.
Ya dana! Kada ka nemi ilimi domin ka yi wa malamai yanga da shi, ko jayyayya da wawaye, kada ka bar ilimi domin kin sa da son jahilci. Ya dana! Ka zabi mazauni, idan ka ga mutane suna ambaton Allah ka zauna tare da su, domin idan ka kasance malami ne sai ya amfane ka kuma su dada maka ilimi, idan kuwa ka kasance jahili sai su sanar da kai, ta yiwu Allah ya mamaye su da rahama sai ta mamaye ka tare da su.
Ya dana! Idan kana kokwanton mutuwa sai ka dauke wa kanka yin bacci, amma ba zaka iya ba. Idan kuwa kana kokwanton tashin kiyama to ka dauke wa kanka farkawa, wannan kuwa shi ma ba zaka iya shi ba, ka sani idan ka yi tunani zaka san cewa ranka ba a hannunka take ba, bacci kamar mutuwa ne kuma farkawa bayan bacci kamar tashi ne da ba mutuwa.

hfazah@yahoo.com
Haidar Center (HAIDARCIP)
Text Only or ; 1-WhatsApp 2-Tango 3-Viber 4- Telegram, etc: (+234 803 215 6884)
Web Site: www.haidarcenter.com

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: