bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      16:17:02
Lambar Labari: 250
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
Kimar Aqida Ga Sanin Mahdi A Makarantar Alulbait (a.s)
Aqidoji duk xaya ne shin sun kasance na qasa ne waxanda xan’adam ya fare su, ko na sama waxanda faruwarsu ke komawa ga Allah Maxaukaki, ba makawa suna da alaqa da dalili na mutuntaka, idan sun kasance na qasa to suna faruwa ne daga yanayin xan’adam kuma an fassarasu ne da tsinkayensa da kwaxayinsa zuwa ga saduwa da mafificiyar rayuwa, in ko sun kasance na sama to suna samar da jin qan Allah (SWT) ga mutum da sonsa gare shi da kwaxayinsa bisa sadar da shi zuwa ga farfajiyar arziqi, kuma wannan na daga cikin abin da mumini ke yinsa take a cikin asalin aqidar Musulunci, duk xaya ne wanann manufar ta bayyana ga mutum a warware ne ko kuma warwarata ta wanzu a dunqule a voye a cikin gaibu. (a gare shi).
Shi mutum wani lokacin yana mu’amala tare da aqidoji ne a hankalce ta fuskancin dalilai da hujjoji, wani lokacin kuma (yana mu’amala da aqida) da jiki ta fuskancin manufofi da amfanunnukan da yake samu daga waxannan aqidojin a rayuwarsa ta yau da gobe. Kuma duk yadda waxannan aqidojin suka kasance bayyanannu masu qarfafa ta fuskancin dalilai da hjujjoji, to murxiyar da ke cikinsu da voyuwarsu ta fuskancin mutumtaka na sa ta zama lamarin da ake kokwanto a kansa, ko dai - a taqaice - su zamo marasa muhimmanci waxanda ba su da tasiri a zuci.
Sannan ita aqidar Musulunci a matsayin ta na aqidar sama ba zai yiwu gare mu mu bayyana manufofinta ga mutum a warware ba, domin warwararren bayani zai kai mu zuwa komawa ga vangare jikin xan’adam wannan kuma ya sava da lamarin da yake shi ne ginshiqi kuma tushe na asali a aqida wanda yake wakiltar vangaren hankali a sarari, (wato bangare hankali shi ne asasi a cikin aqida) da dogaro ta vangaren ruhi a mutuntakar mutum, don haka a xabi’ance za mu isu da wannan aqida da bayanin mataki mafi kusa a taqaice ga buqatun mutum.
Misalin faxin Allah (Ba mu aiko ka ba face jin qai ga talikai).  
Sai dai ita a wannan lokacin tana kwaxaitar da mutum mumini da fuskantar da shi zuwa ga hankaltuwa da tuntuntuni wanda ke bada sakamako zuwa yin amfani da hikimomi waxanda ake kyautata tsammanin cin musu da buqatun xan’adam na fili waxanda ake zato a mabanbantar fuskoki na aqida da na shari’a daga Musulunci.
Haqiqa mun karanci mas’alar Mahdi (a.s) ta fuskancin dalili da hujja, (a.s) kuma ya bayyana cewar fahimtar makarantar Ahlulbait game da mas’alar Mahdi (a.s), in ka kwatanta ta zuwa fahimtar makarantar mazhabobi huxu ta fuskancin dalili da hujja, za ka ga makarantar Ahlulbaiti  (a.s) sun fahimci wannan mas’alas a aikace a cikin mafi kammala sura da cika.  
Kuma cikarta ta fuskancin aqida da dalili yana hukunta kuma yana kai mu zuwa ga quduri da cikarta a cikin abin da ya gabace shi na hidimtawa da tamakawa ga xan’adam, sannan mararrabar da ke kai da yawan mutane su riqa yin kokwanto suna motsa shubuhohi dangane da fahimtar Mahdi (a.s) a wajen Ahlulbait (a.s), suna nuna cewa waxannan mutanen ba sa yin duba ta fuskacin fagen kafa dalili da hujja, gwargwadon yadda suke yin duba ta fuskancin mutuntaka wanda hakan kan sa su yin tambayoyi:
Wane amfani ake samu ta hanyar yin quduri da fahimtar Mahdin da ya siffantu da ma’anonin fakuwa ba irin fakuwar da aka saba ba, ga shekaru masu yawa, ga imamanci sabo? A lokacin da ba sa saduwa da gamsasshen jawabi, sai vangaren mutuntakar wannan fahimtar ya wanzu yana kewaye da shakka da ruxewa, wanda jahilci zai riqa tura su zuwa gare su, kuma gazawae masu wannan  fahimtar ga barin iya suranta lamarin kamar yadda yake na sa masu ita su riqa tuhumar cewa an wuce iyaka kuma qarya ake, sai su musanya ta da wata fahimtar wacce ta sha bamban da wannan mahangar, wacce wofinta daga waxannan shubuhohin da tambayoyin, wanda ba ya buqatar kawo wani voyayyen lamari mai girman gaske, ba tare da sun gane cewa wannan aikin nasu da suka yi - na cire abin da ba su sani ba daga fahimtar mahdawiyyanci - ya sa sun ciratu daga kamala zuwa tawaya, kuma haqiqa wannan bujeriwar ta su daga wannan vangaren na mahangar fakuwa kawai bujerew ga wani ginshiqi mai girma ga mafahimtar Mahdi (a.s) a Musulunci ne, balle ma lalle hakan ya sava da mahangar hankali wanda shi ne yake yin hukunci a babin aqida da qudiri kan miqa wuya ga dalili da hujja duk inda suka fuskanta, ba a canja su a juya su ta fuskancin son rai da soye-soyen zuciya da buqatar xan’adam ba.
Da ace za su yi tunani, kan mahanga da fahimtar Ahlulbait (a.s) kan Mahdawyyanci  (a.s), da sun samu fahimta mafi cika a kan haka fiye da fahimtar makarantar khalifofi ta vangaren mutuntaka, haqiqa Sayyid Shahid Muhammad Baqid Sadar ya yi bayanin wannan nahiyar bayani mai qaye a inda ya rubuta yana cewa:  
"Za mu xauki tambaya ta biyu, yana cewa: Don me duk wannan kwaxayin na musamman daga Allah Maxaukaki a kan wannan xan’adam xin, ya zamana an kautar da dokoki ne xabi’a ta hanyar tsawaita rayuwarsa? Kuma don me ba za a bar jagorancin ranar alqawarin ga wani mutum a nan gaba ba da zamani yake jiransa, sai abubuwan mamakin ranar alqawari su nuna a hannunsa sai ya fito a lokacin ya aiwatar da aikinsa wanda ake jira sa ya gabatar.
Da wata kalmar za mu iya cewa: Mecece fa’idar wannan doguwar fakuwa kuma meye manufarta? 
ZA MU CI GABA IN SHA’Allah Ta'ala:-

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA
Mail= munirsaid92@gmail.com 
Whatsapp da telegram +2348038557822. 

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: