bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      16:20:56
Haqiqa ya sa su bacci na shekara xari uku da tara a wannan kogon, sannan ya tashe su daga baccinsu ya dawo da su fagen dagar rayuwa, bayan tuni wancan tsarin da suke jin tsoro
Lambar Labari: 251
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

Kuma shin ka karanta game da waxannan samarin da suka yi imani da Ubangijinsu ya qara musu shirya   ? Suka fuskanci wani mugun gwamna me bautar gunki, mara tausayi, baya kaikawo cikin tsige dukkan wani tsiro daga ire-iren nau’o’in tsiron bishiyar tauhidi, ko kaxan baya xaga kafa idan mutum ya bar shirka, wannan ya sa rayuwa ta yi musu qunci, kuma xebe tsammani ya kutsa cikin qofofin zukatansu, har ya toshe tagogin fata da buri a gaban idanuwansu, sannan suka fake a kogo suna neman warwarar matsalarsu daga Allah bayan da suka gaza samarwa kansu warwara da mafita, kuma lamarin ya yi musu nauyi a zuciya a ce varna ita ce ke yin mulki, tana zalunci, kuma ga shi ta fi qarfin gaskiya, sannan duk wani sauti da ya yinquro yana kishiyantarta ba ta barin sa har sai ta ga bayansa.  
Shin ka san abin da Allah Maxaukaki ya yi da su?
Haqiqa ya sa su bacci na shekara xari uku da tara   a wannan kogon, sannan ya tashe su daga baccinsu ya dawo da su fagen dagar rayuwa, bayan tuni wancan tsarin da suke jin tsoro wanda ya rinjaye su da qarfinsa da zaluncinsa ya riga ya faxi, ya wayi gari a cikin kundin Tarihi ba ya iya tsoratar da kowa baya iya motsa abin da ke ajiye, duk wannan don waxannan samarin su ga mutuwar wannan vataccen mutumin wanda faxin ikonsa da qarfinsa da kuma zartarwarsa ta girmama gare su, kuma su ga qarshen lamarinsa da idanuwansu kuma suga yadda vata ya kwashi qasqanci a lokacin da suke raye. 
Idan har wannan ganayya mabayyaniya ya tabbata ga ashabul kahfi a sarari, tare da dukkanin abin da take xauke da shi na girma da buyawa masu matuqar qima ta hanyar wannan tilon abin da ya faru, wanda ya tsawaita rayuwarsu har shekara xari uku, haqiqa wannan shi ne ainihin abin da zai faru da jagora sha sauraro Imam Mahdi (a.s) ta hanyar rayuwarsa mai tsawo, da zata ba shi damar ya ga gagarau alhali a lokacin yana xan’qarami kuma ya shedi bishiya kangaran alhali a lokacin tana kwarar iri wadda ake shukawa, sannan kuma ya ga zamanoni tun suna lokacin asubarsu ta fari   (tun farkon faruwar su), qara kan haka cewa, lalle ilimin gwajin wanda ya yi wa tafiyar wannan wayewa rakiya, kuma ya rako ci gabanta na nan gaba, ya kuma fuskance ta kai tsaye domin motsota da ci gabantar da ita, lalle yana da tasiri babba wajen kintsa tunani da zurfafa kwarewa a jagoranci domin yinquri a ranar da aka yi alqawari, domin - waxannan gogayyar zasu sa wanda aka tanada ya samu kansa a gaban gogayyar mutane da dama da dukkanin abin da ke cikinta na vangaren rauni da qarfi, da ma nau’o’in kuskure da daidai, kuma zata sa wannan mutumin ya sami iko mafi girma wajen kimanta zahirin marayar xan’adam ya kuma xorata kan wayewa cikakkiya bisa sababinta, da ma dukkanin abin da ya cakuxa da ita na Tarihi. 
Sannan wannan aikin na kawo canji wanda aka tanadi jagora don ya tsaya da shi ya tsaya ne kan asasin sako ayyananne wanda shi ne sakon musulunci, kuma abu ne na xabi’a cewa tsayuwa da wannan aikin a irin wannan yanayi zai zama yana buqaci jagora na daban, wanda ya rayu a kusa da masdarin musulunci na farko, wanda an riga an gina mutumtakarsa wato (shakhsiyyarsa) cikakkiyar ginawa, da yanayi na daban wanda ya nisanta daga tasirin wayewar zamanin da aka hukuntawa kawo qarshensa wanda shi ne zamanin da aka yi alaqawarin idan Imam (a.s) ya zo zai yaqe shi. (Ma’ana be tasirantu da wayewar zamanin da aka umarce shi ya yaqe ba). 
Sabanin wancenenka, mutumin da aka haifa kuma ya tashi a zanin goyon wannan zamanin kuma ya zama  a nan tunaninsa da shu’irinsa suka buxe, haqiqa wannan bisa  mafi rinjaye ba zai iya kuvuta daga kura-kuran wannan zamanin da ma abin da zamanin yake xamfare da shi ba, ko da kuwa ya jagorancin motsin kawo canja yana mai kisiyantarsa. ..
Domin  a tabbatar da rashin tasirantuwar jagoran da aka tanada da wayewar da aka xora masa aikin canja ta, ya zama ba makawa ga mutumtakarsa ta zama an gina ta  cikakken gini a lokacin wayewar zamanin da ya gabata wacce ta fi kusa da ginuwa kan gamammiyar qauna, ta vangare tushe kuma ta zama ta fi kusa da wayewar da aka umarci wanda aka yi alqawari zuwansa ya canja ta” .   
ZA MU CI GABA IN SHA’Allah Ta'ala:-

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA
Mail= munirsaid92@gmail.com 
Whatsapp da telegram +2348038557822.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: