bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      16:22:55
Amsa: haqiqa dukkanin wani aikin kawo canji cikin al’umma lamarin sa na xamfare da wasu sharuxxa da wasu yanayoyi na waje da ba zai iya yiyuwa canjin ya kai ga hadafinsa ko ya sami mazauni ba sai in har waxannan sharxan da yanayoyin sun cika.
Lambar Labari: 252
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
CI GABA:-
Sannan mai girman daraja ya qara jefo wata tambaya wacce ke da alaqa da vangaren mutumtaka daga aqidar mahdawiyyanci, saboda me wannan jagora na duniya be tava bayyana ba tsawon wannan lokacin? Kuma idan har ya kintsa kansa don yin aikin jama’a, me ya hana shi ya bayyana a fagen fama a tsawon lokacin da ya yi qaramar fakewa ko kuma a qarshe-qarshenta a maimaikon ya mayar da ita babbar fakuwa, a lokacin da yanayin da sharuxxan zamantakewa suka fi sauqi, kuma a lokacin alaqarsa da mutane ta hanyar gungun mutane a gajeriyar fakuwarsa zata ba shi dama ya tsara mabiyansa ya fara aikinsa farawa mai qarfi, kuma hukumar lokacinsa ba ta kasance tana da qarfin da ya kai girman qarfin ikon da mutumtaka ta kai zuwa gare shi bayan wancen lokacin ta hanyar ci gaban ilimi da na masana’anta ba?    
Amsa: haqiqa dukkanin wani aikin kawo canji cikin al’umma lamarin sa na xamfare da wasu sharuxxa da wasu yanayoyi na waje da ba zai iya yiyuwa canjin ya kai ga hadafinsa ko ya sami mazauni ba sai in har waxannan sharxan da yanayoyin sun cika. 
Kuma wannan aiki na kawo canji wanda sama zata tsarge shi a bayan qasa ya fifitu da cewa ba ya da wata alaqa da yanayin   lokacin kawo canjin, domin ayyukan da qoqarin kawa canji ya doru a kansu ta vangare sa na isar da sako, domin sakon da kawo canji da aka xaro masa  sako ne na ubangij, kuma sama ce ta samar da shi, ba yanayin da ake ciki ne ya samar da shi ba, amma ta vanagren zartarwa sakon ya dogara da yanayin da ake ciki kuma nasararsa da lokacin zartar da shi ya dogara bisa gwamata da lokacin wannan yanayin. Saboda haka ne ma, sama ta saurari wucewar qarni biyar na jiahiliyya har lokacin da ta saukar da saqonta na qarshe a hannun Annabi Muhammadu (s.a.w) domin alaqar da ke tsakanin yanayin don zartar da abin da ya kamata a jinkirta shi duk da tsananin buqatuwar duniya zuwa gare ta tun lokaci da dama da ya shuxe kafin wannan lokacin.  
Kuma yanayi na da tasiri ta vangaren zarta da aikin kawo gyara, daga ciki akwai abin da yake shimfixa gamemmen yanayin da ya dace domin samun canjin da ake buri, daga ciki kuma akwai abin da yake fayyace abubuwan da wannan motsi ke buqata ta hanayar bin lamarin loko loko.
Dangane da juyin juya halin da Linin ya  jagoranta a qasar rasha - bisa misali - har ya kai ga nasara, motshin na sa ya kasance yana xamfare da sababi na daga tsayuwar motsin kawo canji na farko a duniya da raunanar sarautar kaisaranci (tsarin masarauta), wannan na daga cikin abin da zai temaka wajen kawo cnaji na juyin juya hali, kuma matsin ya kasance yana xanfare da wani sababai na biyu na gefe iyakantancce, na daga kasancewar Linin cikin qoshin lafiya a cikin tafiyar sa da ya yi da ya samu ya kutsa cikin qasar Rasha ya jagoranci jujin juya hali, domin da wani abu ya faru da shi da zai hana shi shiga rasha da akwai yiyuwar jiyun ya rasa qarfinsa saboda wannan abin sai ya zama ya kasa bayyana a sarira cikin sauri. 
Kuma haqiqa haka sunnar Allah Ta'ala ta gudana wancce ba ta canjawa a wajen motsin kawo canjin da yake daga ubangiji, wanda yake iyakantacce ta vangaren zartarwa daidai da yanayin da ake ciki wanda hakan ke samar da gammamen yanayin da ya dace domin tabbatar da wannan aikin, wannan ne ma ya sa musulunci be zo ba sai bayan wani lokaci na rashin manzanni da tazara mai xaci da ta xore tsawon qarnoni. 
Duk da ikon da Allah Ta'ala yake da shi kan qaranta wahalhalu wajen isar da saqon ubangijintaka, da iya halittar yanayin da ya dace bisa mu’ujiza, sai dai be so ya yi amfani da wannan yanayin ba, domin ita jarrabawa da da musiba da wahalar da mutum ke sha kan hanyarsu ne mutum yake samun kamala, ta wannan nahiyar hakan ya hukunta motsin kawo canjin ubungiji shi ma ya zama bisa xabi’a, kuma wannan ba zai hana Allah Ta'ala ya sa hannu - a wani lokaci ba - kan abin da ya shafi fayyace wasu lamura da yanayi bai zama ya dace da su ba, kaxai dai wani lokaci a kan buqaci, yin motsi daidai da yanayin da ya dace ne, daga nan ne ake samun temako da miqa hannun ubangiji a voye wanda Allah Ta'ala yake yi wa waliyyansa a lokacin da suke cikin qunci sai ya kare manzanci da shi, sai ga wutar Namarudu ta wayi gari mai sanyi da aminci ga Annabi Ibrahim (a.s)  sai ga hannun mugun bayahuden da ya xaga takobinsa a kan Annabi Muhammadu (s.a.w) ya shanye ya rasa ikon da yake da shi na motsa shi,   sai ga iska mai qarfi ta xaxxage hemomin kafirai da msuhrikan da suka kewaye madina a ranar handaq tana jefa tsoru cikin zukatansu,   sai dai gaba xayan wannan be wace fayyacewa da bada gudun mawa a lokacin da ake buqata ba bayan yanayin ya kasance ya dace da ayi kokarin kawo canji a dunqule da zai iya zama bisa yanayi na yau-da-gobe, daidai da yanayin da ake ciki. 
Bisa wannan haskakawar zamu karanta matsayar Imam Mahdi (a.s), don mu ga cewa lalle motsin yin jujin juya hali da aka zave shi don ya gabatar ta bangaren zartarwa -kamr dai ko wane motsi ne na kawo canji - yana da alaqa ta vangaren zartarwa da yanayin da ake ciki wanda zai temaka wajen lamarin ya yi daidadi da aikin, daga nan ne ya zama a xabi’ance ya zama ya tsaya a kan haka. 
Sanannen abu ne cewa Imam Mahdi (a.s) be riga ya kintsa kansa kan wani iyakantaccen lamarin na jama’a na musamman ba ko kuma wani aikin kawo sauyi a wani yanki ko wancen ba, domin sakon da aka tanade shi don ya isar ta vangaren ubangiji maxaukaki sarki shi ne ya canja duniya canjawa na baki xaya, kuma ya fitar da xan’adama daga dukkanin xan’adam daga duhun zalunci zuwa hasken adalci,   kuma wannan babbana aikin na kawo canji wajen gudanar sa shi be isar ace kawai akwai saqo tare da jagora na gari ba, in ba haka ba da tuni sharaxan yin hakan sun cika tun a zamanin annabta kanta (zamanin da Annabi Muhammadu (s.a.w) yake raye), lalle kaxai lamarin na buqatar yanayin da duniya ta dace da hakan, da gamammen yanayin da zai temaka. Ta vangaren mutumtaka ana ganin yadda mutumin wayewa yake jin cewa narkewa dalili ne na asasi wajen halittar wannan yanayin da zai sa a karvi wannan sabon sakon na adalci, kuma wannan jin narkewar yana samuwa ne kuma yana kafuwa a jikin mutum ta hanyar gogayyar zamani kala-kala, wacce mutumin wayewa ya fito daga cikinta yana mai nauyaya da tufafin da aka gina yana mai riskar buqatarsa zuwa temako yana mai waiwayar fixirarsa zuwa gaibu ko zuwa abin da be sani ba.
ZAMU CI GABA:- 

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA
Mail= munirsaid92@gmail.com 
Whatsapp da telegram +2348038557822.


DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
CI GABA:-
Ta bangaren buqatun jiki kuma ta yiyu sharaxin sabuwar rayuwar buqatun jiki su zama sun fi iko fiya da sharaxin rayuwa a da, a lokaci irin lokacin fakuwa, wajen isar da saqon a matakin duniya baki xayanta, wannan kuwa saboda abin da zamanin ya tabbatar da shi na kusanto da nesa da iko mai mai qirman gaske kan kai-kawo tsakanin al’ummun duniya, da yalwatar hanyoyi da kayan aikin da hedkwata ke da buqatuwa zuwa gare su don gudanar da ayyukan wayar da kan mutanen duniya, da cigabantar da su kan asasin sabon manzanci (saqo).  
Amma abin da aka yi nuni kan sa a cikin tambaya na qaruwar karfin soji da makaminsu wanda jagora zai fuskanta a ranar da aka yi alqawari, duk lokacin da aka qara jinkirta bayyanarsa, wannan abu ne ingantacce, sai dai da me qara ci gaban qarfin soji zai amfanar tare da faxuwar ruhi da zukata warwas daga cikin jiki. Tare da zubewar ginin ruhin xan’adam din da ya mallaki waxannan makaman qasa-qasa makami ba shi da wani tasiri? Sau nawa ya faru a tarihi, sai kaga ginin ci gaba mai girma a zube sakamakon xan qaramin kai hari na farko, saboda dama a zube yake kafin nan, kuma ya riga ya rasa qwarin guiwa kan samuwarsa da gamsuwa kan kasancewarsa, da samun nutsuwa kan haqiqaninsa”  . A nan ne abin da - Sayyid Shahid Sadar - ya fa’idantar ya qare, Allah Ta'ala ya tsarkake ruhinsa.  
Kuma zamu iya yin bayanin abin da mutumtaka zata samu daga mahdawiyyanci a mahangar Ahlulbaiti (a.s) ta wani vangaren. 
Sai mu ce: 
Haqiqa qudurcewa da mahdawiyyanci (Imam Mahdi (a.s),  wanda ya faku daga idanuwa duk da yana raye kuma yana yin tasiri wajen gudanar lamura, haqiqa al’ummar muminai tana cin ribar hakan, kuma Imam na xauke da dukkanin khususiyyar Imamanci na daga Isma da nassin Annabci da kamala ta ilimi da aiki, kuma yana daga cikin sha’aninsa  yaxa wannan jawwin (wato yanayin da lamarin) na imamanci da Qanshinta na ma’anawiyya (na ma’ana wato mai tasiri a voye) da na ruhi maxaukai, kuma mutum yana jin ya qoshi da kyakkyawan shu’uri mai daxi saboda samuwar xorewar alaqa tsakanin  sama da qasa da ci gaban samun kulawar sama ga doron qasa, da canja haka zuwa ma’ana da ake xosana sosai da tafi tasiri a zuciya, bayan hakan ya kasance abu karvavve a tushenta na aqida, kuma za a tafiyar da hukumar tauhidi a fagen rayuwar zamantakewar mutane da siyasa, kuma zai sanya ta ta zama tana da tasirin da yake kusa da riskar xan’adam, la’akari da cewa lalle mahdin nan (a.s) da ya faku ba mutum ne game gari ba, lalle shi ne Imami na goma sha biyu wanda aka ayyana daga sama wanda ya hau kujerar imamanci har zuwa qarshin tarihi, da gaske ne cewa mutane ba su saduwa da shi a sarari, sai dai aqidantuwa da kasancewar sa haqiqa wacce ake riska, wacce riskar mu ta tawaya daga ganota, hakan na sa ruhi ya zama cikin yanayin jin alaqa ta ruhi mai kyau da tafarkin imamamanci ma’asumi na ubangiji a matsayinsa na cewa shi cigaban hukumar tauhidi ne a doron  qasa. 
Kuma wannan alaqa na bayyana sosai a lokacin fakakkiyar mahdawiyya ma’asuma wacce zata yi bayanin kanta bayani na siyasa a sarari, ta hanyar farkon fara gamemmen wakilci na musamman na (na wakilia huxu) a lokacin gajeriyar fakuwa. Da kuma fara gamemmen wakilci na musamman na faqihai a lokacin doguwar fakuwa a matsayunsu na jagorori na siyasa ta shari’a da al’uammar musulmai, ta yadda matsayin nan mai girma na imamanci zai wanzu, tamkar mai sa ido yana bibiyar gogayyar siyasa da ta zamantakewa yana temaka musu, kuma tamkar wata mashaya da take temaka musu a shari’ance idan ya ga ta dace da musulunci. ..
Daga cikin tarin waxannan bayanan ma’anar kamala a cikin abin da Imam Mahdi (a.s) zai gabatar za ta bayyana a sarari, na daga abin da mutumtaka zata bayar, kuma abu ne da ya dace xari bisa xari da tsaftatacciyar mahangar mahdawiyyanci, domin haqiqa mahdawiyyanacin da yake ma’asumi wanda da ya faqu mahdawiyyanci ne mai motsi mai tasiri mai amfani ga xan’adam, kuma ba ta wuce bada labarin abin da zai zo nan gaba ba. Kai ka ce mahdin Ahlulbaiti (a.s) ya xauki nauyin abin da aka xora masa ta hanyar motsa ainihin yadda xan’adam yake da kuma yin alaqa mai kyau da shi. 
Kuma wannan a kan kansa shi ne mafi kyau abin da za a iya bayyana ma’anar sauraro da shi domin sauraron yayewa ba shi ne yin shiru da nuna gazawa ba, kaxai da shi ruhi ne mai amfani mai motsi zuwa tafarkin kawo canjin da ake buqata a mahdawiyyance. 
Sakamakon Bincike  
A qarshen wannan zagayen, zamu iya rairayo abin da sakamakon wannan bahasin ke xauke da shi, da waxannan ‘yan kalmomi kamar haka: 
1- Haqiqa addini shi ne mafi kamalar bayani kan haqiqar xan’adam kuma musulunci ne bayani mafi cika kan haqiqanin addini, kuma shi’anci shi ne bayani mafi kamala kan haqiqanin musulunci, baya ga haka mahdawiyyancin Ahlulbaiti (a.s), shi ne mafi kamalar bayani kan asalin mahdawiyyanci, wanda dukkanin musulmai suka haxu kan aqidantuwa da shi. 
2- Haqiqa zinaren banbancin da ke tsakanin mahdawiyya a wajen Ahlulbaiti (a.s), da mahdawiyyancin mafi yawan malaman musulmai, yana komawa ne, zuwa mas’alar imamamnci, haqiqa dai shi Mahdi (a.s) a mahangar makarantar Ahlulbaiti (a.s) shi ne Imami na goma sha biyu, a yayin da a wajen makarantar sahabai mas’ala ce ta abin da zai faru nan gaba kawai. 
3- A yayin da mas’alar Imam Mahdi (a.s) a wajen Ahlulbaiti (a.s) ta zama mas’alace ta Imami na goma shi biyu wanda al’umma ba su da wani Imam a bayansa, daga nan ne ya zama fahimtar mahdawiyya a wajensu ta siffatu da kevance-kevance guda uku, waxanda su ne haihuwar Imam Mahdi (a.s) a asirce a voye, kuma ya zama imami yana qarami, da kuma fakuwarsa da ta lazimta masa rayuwa mai tsawon zamani kuma waxannan kevance-kevance guda uku sun tabbata ta hanyar tabbatar asalin imamanci Imamai sha biyu ma’asumai (a.s), wanda daga nan ne ya samo asali, ballantana ma mun riga mun jero muku dalilansa dalla-dalla, xaya bayan xaya tun a baya. 
4- Haqiqa waxannan kevance-kevancen guda uku ba a tabbatar da su ta hanyar dalilai na aqida da hankali da na gamsuwa ba, kuma sam ba wani ishakali da yake lazimtarsu, na hankali ne ko na addini, ma’ana; (ba kawai sun kuvuta daga ishkalin hankali ko na addini kawai ba ne), bisa haqiqa su ne ma ke fitar da ma’ana ta kamala wajen fahimtar mahdawiyyanci kuma su mayar da shi ya zama faminta mai qima ta aqida mai qima ta mutuntaka maxaukakiya wacce ke tattare da kyawawan halaye a matakin al’umma, wacce ta zama ta sami kamala kuma ta dace da abin da tushen addini ya xoru a kai a cikin rayuwar xan’Adam.  
                                                                
Tsira da aminci su qara tabbata a bisa Manzon Allah Muhammad  (s.a.w) tare da alayensa tsarkaka (a.s).

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA
Mail= munirsaid92@gmail.com 
Whatsapp da telegram +2348038557822.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: