bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      16:26:17
makaminsu wanda jagora zai fuskanta a ranar da aka yi alqawari, duk lokacin da aka qara jinkirta bayyanarsa
Lambar Labari: 253
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
Ta bangaren buqatun jiki kuma ta yiyu sharaxin sabuwar rayuwar buqatun jiki su zama sun fi iko fiya da sharaxin rayuwa a da, a lokaci irin lokacin fakuwa, wajen isar da saqon a matakin duniya baki xayanta, wannan kuwa saboda abin da zamanin ya tabbatar da shi na kusanto da nesa da iko mai mai qirman gaske kan kai-kawo tsakanin al’ummun duniya, da yalwatar hanyoyi da kayan aikin da hedkwata ke da buqatuwa zuwa gare su don gudanar da ayyukan wayar da kan mutanen duniya, da cigabantar da su kan asasin sabon manzanci (saqo).  
Amma abin da aka yi nuni kan sa a cikin tambaya na qaruwar karfin soji da makaminsu wanda jagora zai fuskanta a ranar da aka yi alqawari, duk lokacin da aka qara jinkirta bayyanarsa, wannan abu ne ingantacce, sai dai da me qara ci gaban qarfin soji zai amfanar tare da faxuwar ruhi da zukata warwas daga cikin jiki. Tare da zubewar ginin ruhin xan’adam din da ya mallaki waxannan makaman qasa-qasa makami ba shi da wani tasiri? Sau nawa ya faru a tarihi, sai kaga ginin ci gaba mai girma a zube sakamakon xan qaramin kai hari na farko, saboda dama a zube yake kafin nan, kuma ya riga ya rasa qwarin guiwa kan samuwarsa da gamsuwa kan kasancewarsa, da samun nutsuwa kan haqiqaninsa”  . A nan ne abin da - Sayyid Shahid Sadar - ya fa’idantar ya qare, Allah Ta'ala ya tsarkake ruhinsa.  
Kuma zamu iya yin bayanin abin da mutumtaka zata samu daga mahdawiyyanci a mahangar Ahlulbaiti (a.s) ta wani vangaren. 
Sai mu ce: 
Haqiqa qudurcewa da mahdawiyyanci (Imam Mahdi (a.s),  wanda ya faku daga idanuwa duk da yana raye kuma yana yin tasiri wajen gudanar lamura, haqiqa al’ummar muminai tana cin ribar hakan, kuma Imam na xauke da dukkanin khususiyyar Imamanci na daga Isma da nassin Annabci da kamala ta ilimi da aiki, kuma yana daga cikin sha’aninsa  yaxa wannan jawwin (wato yanayin da lamarin) na imamanci da Qanshinta na ma’anawiyya (na ma’ana wato mai tasiri a voye) da na ruhi maxaukai, kuma mutum yana jin ya qoshi da kyakkyawan shu’uri mai daxi saboda samuwar xorewar alaqa tsakanin  sama da qasa da ci gaban samun kulawar sama ga doron qasa, da canja haka zuwa ma’ana da ake xosana sosai da tafi tasiri a zuciya, bayan hakan ya kasance abu karvavve a tushenta na aqida, kuma za a tafiyar da hukumar tauhidi a fagen rayuwar zamantakewar mutane da siyasa, kuma zai sanya ta ta zama tana da tasirin da yake kusa da riskar xan’adam, la’akari da cewa lalle mahdin nan (a.s) da ya faku ba mutum ne game gari ba, lalle shi ne Imami na goma sha biyu wanda aka ayyana daga sama wanda ya hau kujerar imamanci har zuwa qarshin tarihi, da gaske ne cewa mutane ba su saduwa da shi a sarari, sai dai aqidantuwa da kasancewar sa haqiqa wacce ake riska, wacce riskar mu ta tawaya daga ganota, hakan na sa ruhi ya zama cikin yanayin jin alaqa ta ruhi mai kyau da tafarkin imamamanci ma’asumi na ubangiji a matsayinsa na cewa shi cigaban hukumar tauhidi ne a doron  qasa. 
Kuma wannan alaqa na bayyana sosai a lokacin fakakkiyar mahdawiyya ma’asuma wacce zata yi bayanin kanta bayani na siyasa a sarari, ta hanyar farkon fara gamemmen wakilci na musamman na (na wakilia huxu) a lokacin gajeriyar fakuwa. Da kuma fara gamemmen wakilci na musamman na faqihai a lokacin doguwar fakuwa a matsayunsu na jagorori na siyasa ta shari’a da al’uammar musulmai, ta yadda matsayin nan mai girma na imamanci zai wanzu, tamkar mai sa ido yana bibiyar gogayyar siyasa da ta zamantakewa yana temaka musu, kuma tamkar wata mashaya da take temaka musu a shari’ance idan ya ga ta dace da musulunci. ..
Daga cikin tarin waxannan bayanan ma’anar kamala a cikin abin da Imam Mahdi (a.s) zai gabatar za ta bayyana a sarari, na daga abin da mutumtaka zata bayar, kuma abu ne da ya dace xari bisa xari da tsaftatacciyar mahangar mahdawiyyanci, domin haqiqa mahdawiyyanacin da yake ma’asumi wanda da ya faqu mahdawiyyanci ne mai motsi mai tasiri mai amfani ga xan’adam, kuma ba ta wuce bada labarin abin da zai zo nan gaba ba. Kai ka ce mahdin Ahlulbaiti (a.s) ya xauki nauyin abin da aka xora masa ta hanyar motsa ainihin yadda xan’adam yake da kuma yin alaqa mai kyau da shi. 
Kuma wannan a kan kansa shi ne mafi kyau abin da za a iya bayyana ma’anar sauraro da shi domin sauraron yayewa ba shi ne yin shiru da nuna gazawa ba, kaxai da shi ruhi ne mai amfani mai motsi zuwa tafarkin kawo canjin da ake buqata a mahdawiyyance. 
Sakamakon Bincike  
A qarshen wannan zagayen, zamu iya rairayo abin da sakamakon wannan bahasin ke xauke da shi, da waxannan ‘yan kalmomi kamar haka: 
1- Haqiqa addini shi ne mafi kamalar bayani kan haqiqar xan’adam kuma musulunci ne bayani mafi cika kan haqiqanin addini, kuma shi’anci shi ne bayani mafi kamala kan haqiqanin musulunci, baya ga haka mahdawiyyancin Ahlulbaiti (a.s), shi ne mafi kamalar bayani kan asalin mahdawiyyanci, wanda dukkanin musulmai suka haxu kan aqidantuwa da shi. 
2- Haqiqa zinaren banbancin da ke tsakanin mahdawiyya a wajen Ahlulbaiti (a.s), da mahdawiyyancin mafi yawan malaman musulmai, yana komawa ne, zuwa mas’alar imamamnci, haqiqa dai shi Mahdi (a.s) a mahangar makarantar Ahlulbaiti (a.s) shi ne Imami na goma sha biyu, a yayin da a wajen makarantar sahabai mas’ala ce ta abin da zai faru nan gaba kawai. 
3- A yayin da mas’alar Imam Mahdi (a.s) a wajen Ahlulbaiti (a.s) ta zama mas’alace ta Imami na goma shi biyu wanda al’umma ba su da wani Imam a bayansa, daga nan ne ya zama fahimtar mahdawiyya a wajensu ta siffatu da kevance-kevance guda uku, waxanda su ne haihuwar Imam Mahdi (a.s) a asirce a voye, kuma ya zama imami yana qarami, da kuma fakuwarsa da ta lazimta masa rayuwa mai tsawon zamani kuma waxannan kevance-kevance guda uku sun tabbata ta hanyar tabbatar asalin imamanci Imamai sha biyu ma’asumai (a.s), wanda daga nan ne ya samo asali, ballantana ma mun riga mun jero muku dalilansa dalla-dalla, xaya bayan xaya tun a baya. 
4- Haqiqa waxannan kevance-kevancen guda uku ba a tabbatar da su ta hanyar dalilai na aqida da hankali da na gamsuwa ba, kuma sam ba wani ishakali da yake lazimtarsu, na hankali ne ko na addini, ma’ana; (ba kawai sun kuvuta daga ishkalin hankali ko na addini kawai ba ne), bisa haqiqa su ne ma ke fitar da ma’ana ta kamala wajen fahimtar mahdawiyyanci kuma su mayar da shi ya zama faminta mai qima ta aqida mai qima ta mutuntaka maxaukakiya wacce ke tattare da kyawawan halaye a matakin al’umma, wacce ta zama ta sami kamala kuma ta dace da abin da tushen addini ya xoru a kai a cikin rayuwar xan’Adam.  
                                                                
Tsira da aminci su qara tabbata a bisa Manzon Allah Muhammad  (s.a.w) tare da alayensa tsarkaka (a.s).

MUNIR MUHAMMAD SA’ID.
KANO, NIGERIA
Mail= munirsaid92@gmail.com 
Whatsapp da telegram +2348038557822.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: