bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      16:32:57
Amma ukun da suka kebanta da mace su ne:-
Lambar Labari: 254
Hukunce-hukuncen Wankan Wajibi
 39> Wanka yana wajaba a gurare bakwai, hudu daga ciki maza da mata sun yi tarayya a cikin su. Wadannan hudun su ne:- 
1. Wankan janaba.
2. Wankan taba mamaci 
3. Wankan mamaci.
4. Wankan da ya wajaba da bakance ko rantsuwa da makamancinsu.
Amma ukun da suka kebanta da mace su ne:- 
1. Wankan haila; (bayan tsarkaka da daukewar jini).
2. Wankan istihala; kamar yadda bayaninsa zai zo.
3. Wankan jinin biki ko nifasi; shi ne wanda yake fita bayan haihuwa, kuma mafi yawansa kwana goma ne.
 40> (m.351) Janaba tana da sababai guda biyu:
1. Jima'i (saduwa ko yaya ya shiga cikin farji).
2. Fitar maniyyi a cikin bacci ko a farke.
 41> (m.361) Abubuwa biyar sun haramta ga mai janaba, su ne:- 
1. Taba rubutun Kur'ani mai girma, ko taba sunan Allah madaukaki ko taba sunayen Annabawa da Imamai (A.S)
2. Shiga masallacin haramin Makka da masallacin Annabi (S.A.W) koda da nufin wucewa ne.
3. Zama a cikin sauran masallatai da kaburbura masu daraja na Imamai (A.S) sai dai babu laifi da wucewa ko shiga cikinsu dan dauko wani abu.
4. Ajiye wani abu a cikin masallaci.
5. Karanta ayar sujjada, daga cikin madaukakan surori. Su ne:- surar (As-sajdah) aya ta <15> da surar (fussilat) aya ta <37> da (Najami) aya ta <62> da (Alaki) aya ta <19>. 
 42> (m.363) Wankan janaba mustahabbi ne a kan kansa, kuma yana wajaba ne don yin sallar wajibi da makamancinta.
 43> (m.397) Idan mutum ya yi wankan janaba to ya isar masa daga yin alwala.
 44> (m.446) Jinin haila ba ya gaza kwana uku kuma ba ya wuce kwana goma.
 45> (m. 456) Ya haramta ga mai haila ta yi ibadar da aka shardanta tsarki a cikinta kamar salla da azumi, amma banda wacce ba a shadanta tsarki a cikinta ba kamar sallar gawa, kuma an haramta mata dukkan abin da aka haramta wa mai janaba, kamar yadda aka haramta mata yin jima'i, to haka ma mijinta an haramta ya yi jima'i da ita.
 46> (m.472) Idan mace ta yi tsarki daga haila, wajibi ne ta yi wanka don salla da sauran aikin da aka shardanta tsarki dominsu. 
 47> (m.514,517,519) Nifasi shi ne jinin da yake fita bayan haihuwa, mafi yawansa kwana goma ne kuma hukuncin mace a lokacin nifasi daidai yake da hukuncinta a lokacin haila.
 48> (m.535,527) Wanda ya taba wata gaba daga jikin mamaci bayan sanyayar jikinsa kuma kafin a yi masa wanka wajibi ne ya yi wankan taba mamaci, haka nan wanda ya taba guntuwar tsoka mai kashi wacce ta fita daga jikin mutum rayayye ko mamacin da ba a wanke shi ba.
 49> (m.530) Ya wajaba a yi wanka sakamakon taba mataccen yaro/yarinya koda kuwa bari ne wanda ya cika wata hudu.
Yadda Ake Yin Wanka
 50> (m. 367…) Wanka kala biyu ne.
1. Jerantau (tartibi)
2. Gamau ko nitsau (irtimasi)
 A wanka jerantau wajibi ne a yi niyyar neman yardar Allah (S.W.T) yayin wanke kai da wuya, sannan ya wanke dukkanin jikinsa, ya gabatar da bangaren dama sannan na hagu, domin samun tabbacin wanke dukkanin bangarorin jikin sa guda uku, wajibi ne yayin wanke kowane bangare, ya dan shigar da daya bangaren a cikin wankewar.
 Yayin yin wanka nutsau (na nutsewa a cikin ruwa) dole ne ruwan ya game dukkan jiki a lokaci guda, idan ya nutse a ruwa da nufin yin wanka irtimasi kuma ya zamana kafarsa tana cikin kasa da makamancin haka to wajibi ne ya dan daga kafar tasa.
 51> (m.378) Yayin wanka dole ne dukkanin gabbai su kasance tsarkakakku daga najasa dama daudar da za ta hana ruwa taba jiki. 
 52> (m.380) Da a ce ruwa bai taba wata gaba ta jiki ba koda da kwatankwacin kan gashi guda daya ne, to wankansa ya baci, sai dai ba wajibi ba ne wanke abin da ba a gani daga gabban jiki, kamar cikin kunne da hanci da makamancinsu. 
 53> (m.387-389) Wanka yana baci idan aka yi shi da ruwan kwace ko wajen kwace, haka nan ma yana baci idan ya yi niyya kin biyan kudin shiga bandakin ko ya yi niyyar bayarwa daga dukiyar haram, ko kudin da ba a fitar masa da khumusi ba, ko ya gina mu'amalarsa a kan jinkiri, ba tare da sanin mai hayar bandakin ba. 
 55> (m.395) Idan akwai wanka da yawa a kansa, wanka daya ya isar masa tare da niyya.

Hukunce-hukuncen Mamaci
 56> (m,539) Wajibi ne a fuskantar da musulmi wanda zai rasu zuwa alkibla (yayin fitar ransa) a rigingine (a  kwantar da shi bisa bayansa), ta yadda zai zama tafukan kafarsa suna kallon alkibla, namiji ne shi ko mace babba ne ko yaro. 
 57> (m.548) Wajibi ne ga dukkan baligi, wajabci na isarwa (kifa'i) a wanke mamaci musulmi haka ma sa masa likkafani da yi masa salla da binne shi. Da wasu za su yi hakan, to wajabcin ya sauka daga kan sauran musulmi. Amma idan ba wanda ya yi, to kowa yana cikin sabo. 
 58> (m.556) Wajibi ne a yi wa mamaci wanka guda uku:-
1. A wanke shi da ruwan da aka gauraya shi da magarya.
2. A wanke shi da ruwan da aka gauraya shi da kafur. Amma fa wajibi ne kada a sa magaryar da kafur din da yawa ta yadda ruwan zai zama majirkici, kuma kada ya zama kadan ta yadda ba za a kira shi ruwan magarya ko kafur ba. 
3. Wanke shi da ruwa zalla. 
 59> (m.564) Wajibi ne wanke bari da yi masa likkafani idan ya cika wata hudu ko sama da haka, amma idan bai kai wata hudu ba, sai a nade shi a kyalle a binne shi ba tare da wanka ba. 
 60> (m.562) An shardanta, yin niyyar ibada a cikin wankan mamaci, ta hanyar yin wankan da nufin yi don Allah (S.W.T). 
 61> (m.573) Karbar lada don wanke mamaci haramun ne kuma idan mutum ya karbi ladan wanke mamaci to wankan ya baci, amma ba laifi a karbi lada don abubuwan da suka gabaci wankan.
 62> (m.591) Wajibi ne shafe mamaci bayan gama yi masa wanka. Abin nufi shi ne a shafa masa kafur a goshi, da tafukan hannu, da gwiwoyi, da kan manyan 'yan yatsunsa na kafafu, kuma lallai ne kafur din ya kasance gari kuma sabon diba wanda kanshinsa bai gushe ba. 
 63> (m.576) Wajibi ne a yi wa mamaci likkafani da tufafi guda uku: Na farkon su gwado; shi ne wanda yake suturce jikin mamace daga cibiyarsa zuwa gwiwarsa. Na biyu riga ita ce ke suturce jikin tun daga allon kafadu har ya zuwa rabin kwauri. Na uku, mayafi, kwatankwacinsa a tsawo shi ne wanda zai yiwu a daure karshensa ta bangaren kai da kafa, amma kwatankwacinsa a fadi shi ne abin da zai lullube bangarorin guda biyu, daya a kan daya.
 64> (m.600-602) Wajibi ne yi wa mamaci salla bayan gama yi masa wanka da sa masa kafur da shafe shi da kuma sanya masa likkafani, kuma wajibi ne a yi wadannan ga yaron da dayan mahaifansa ya kasance musulmi, kuma ya kasance wanda ya kai shekara shida. 
 65> (m.603) Ba a shardanta, tsarkin hadasi (kamar alwala ko wankan janaba) da habasi (kamar wanke najasa) a cikin sallar mamaci ba, kuma ta inganta tare da hadasi kai da ma najasar jiki da tufafi. 
 66> (m.604) An shardanta fuskantar alkibla a cikin sallar mamaci, da kuma ajiye mamaci a gaban mai salla, a kwantar da shi a rigingine, ta yadda kansa zai zama a bangaren daman mai yin sallar, kafarsa kuma a hagunsa. 
 67> (m.615) Kabbara biyar a ke yi a cikin sallar gawa, ya isar bayan yin niyya da kuma ayyana mamacin a yi kabbara sau biyar kamar haka:-
 A Ta Daya:- Allahu akbar "ash'hadu anl'la'ilaha illal Lah, wa ash'hadu anna' Muhammdan, rasulullah".
 A Ta Biyu:- Allahu akbar "Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad".
 A Ta Uku:- Allahu akbar "allahummagfir lilmuminina walmuminat".
 A Ta Hudu:- Allahu akbar "allahumagfir li hazal maiyyit" (idan namiji ne). Ko Allhumagfir li hazihil mayyita (idan mace ce)
 A Ta Bitar:- Allahu Akbar.
 Da wannan kabbara ta biyar sallar gawa take kammala. 
 68> (m.620) Wajibi ne a binne mamaci ta yadda warinsa ba zai fito waje ba kuma zakoki (dabbobi masu cin nama) ba za su tono shi ba.
 69> (m.622) Wajibi ne a sanya mamaci a kabari ta bangarensa na dama ta yadda gaban jikinsa zai fuskanci alkibla.
 70> (m.641-643) Bai halatta a mari fuska, ko a yage fuskar da sauran jiki ba. A wani lokacin ma hakan na wajabta kaffara. (a koma manyan littafai don karin bayani). 
 71> (m.648-649) Haramun ne tone kabarin musulmi ko da kuwa ya kasance yaro ko mahaukaci, in ba a wasu yanayi da aka togace a cikin littattafan fikihu ba, amma babu laifi bayan jikin ya zama kasa. 
 Haramun ne tone kabarin 'ya'yan Imamai da shahidai da malamai da salihai koda kuwa sun shude shekaru masu yawa.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: