bayyinaat

Published time: 26 ,January ,2017      15:19:17
Makarantun fikihu su ne madafa ta farko na cigaban ilimi da tunani ga kowane shi’a duk inda yake, domin shi’anci a yau bai gushe ba yana samun haske daga akida da akhlak da kuma ayyuka a matsayin daidaiku da kuma jama’a gaba daya, daga hauzozi da marja’o'i.
Lambar Labari: 26
Godiya ta tabbata ga Allah (s.w.t) Kuma Aminci ya k'ara tabbata ga bayinsa wad'anda ya zab'a.
"… sa'annan abin da kuka ji dad'i da shi daga gare su to ku ba su ladansu bisa farilla sadaki…" .

Ba ya buya ga ma’abota hankula da tunani cewa fikihu yana daga mafi muhimmancin ilimomin musulunci har ma da 'yan'adamtaka, domin shi yana lamunce bayani game da koyarwa da tarbiyyar ruhin mutum da kuma kyautata aikinsa da zancensa bisa shiryarwar shari’a mai tsarki. Domin shi ne madaukakin ilimi bayan ilimin akida, kuma yana kunnen doki da ilimin kyawawan halaye.
Wadannan ilimomi uku su ne uwayen ilimomin muslunci kamar yadda ya zo a hadisin Annabi (s.a.w) cewa: "Ilimomi uku ne: Aya Muhkama, ko Farilla Adila, ko Sunna Tsayayyiya, amma waninsu saura ne". Da wannan ne mutum yake samun daraja da daukaka da rabauta da rabautar duniya da lahira.
Tsayuwa a kan wannan tafarki madaidaici da kuma riko da shi a rayuwar mutum, yana samuwa ne a shari’ar Allah mai sauki, domin Ubangiji madaukaki shi ne masani da komai mai iko a kan komai, babu wata kwayar zarra da take buya daga iliminsa ko a sama ko a kasa, iliminsa shi ne ainihin zatinsa, kuma zuwa gare shi ne ilimin kowane mai ilimi zai koma.
Maudu’in Ilimin Fikihu: 
 Sanannen abu a rayuwar al'ummar musulmai shi ne cewa Allah madaukaki yana tsara rayuwarsu da aikace-aikacensu ta hanyar dokokinsa ne, don haka ne babu wani mutum da ya isa ya yi rayuwa kubutacciya mai dadi matukar bai tsinkayi dokokin da Allah ya tsara ba, kuma ya tafiyar da sha’anoninsa da al’amuransa bisa garesu ba. Idan dan Adam bai yi haka ba, to rayuwa zata shiga matsaloli da rikece-rikice da rauwawa. Ubangiji madaukaki yana cewa: "Duk wanda ya ketare dokokin Allah hakika ya zalunci kansa” .
A kan wannan mataki na hankali da shari’a ne ya wajaba kan kowane mumini ya tsinakayi wannan dokoki, kuma ya nemi saninsu, tun ma kafin ya shiga shekarun balaga; namiji ne ko mace.
Muna iya cewa; maudu'in ilimin fikihu shi ne abin da ya kunshi ayyukan baligai na ibada da mu’amala, da zamantakewa, da siyasa da tattalin arziki da makamantasu. Kuma duk wanda ya lizimci abin da Allah ya umarta kuma ya soyar zuwa gareshi, ya kuma tsoratar ga barin abin da ya hana, wannan shi ne mai rabauta da rabo mafi girma, kuma shi ne wanda ya hau daraja madaukakiya: kamar yadda ya zo a hadisi madaukaki cewa: "Bawa yana kusanta zuwa gareni da nafiloli har sai in zama sonsa, idan na so shi sai in zama jinsa da yake ji da shi da ganinsa da yake gani da shi da hannunsa da yake riko da shi".

Fikihun Kwarewa: 
Shari’ar musulunci ta kai matuka wajan kwadaitarwa a kan tsara rayuwar zamantakewa kuma ba ta takaita ga sanya dokoki ga mutum ba ne kawai, ko kuma kira zuwa ga aikata su, ko kuma kwadaitar da iyaye kan tarbiyyatar da ‘ya’yansu kafin balaga, har ma ta kara da karfafa kiran muminai gaba daya zuwa zabar wasu jama’a daga cikinsu ta musamman da zata dauki nauyin aikin karanta fikihu da kwarewa a cikinsa domin ta dauki nauyin sanin dokoki da tunani a cikin al’ummar musulmi, ubangiji madaukakin sarki yana cewa: "Da dai daga kowace al’umma wasu jama’a daga cikinsu sun tafi domin su san ilimin addini domin su yi wa mutanensu gargadi idan suka koma zuwa garesu ko sa tsoratu".
Ta haka ne ilimin fikihu ya bayyana a matsayin ilimi na kwarewa da yake bukatar malamai da kwararru, da tsarin karatu, da kuma lizimtar samuwar dalibai da suke karatu a Hauza, sannan suke zurfafa wa a ciki marhala bayan marhala har sai sun kai marhalar ijtihadi a fikihu (fitar da huknce-hukuncen shari’a na rassa daga dalilanta).

Cigaban Ilimin Fikihu: 
Ilimi fikihu ya ci gaba kamar sauran ilimomi musamman a mazhabin Ahlul-bait (a.s) kuma ya rabauta da jaddaduwa da ci gaba tare da zamaninsa a kowace kasa da kuma kowane yanayi, musamman a sababbin mas’aloli da mas'aloli masu sabuntuwa, wannan ci gaban ya kai ga karatun ilimin fikihu karatu mai zufi da sabutuwa, yana mai gini a kan dokoki da dalilai daga littafi da sunna da ijma’i da hankali, a kan sabon asasi da sababbin ka'idoji na Usulul fikihu, wanda ya nisanta daga Istihsani da kiyasi wanda riko da su yakan kai ga rushewar addini da karkacewarsa.
Malamanmu sun dauki nauyi kuma ba su gushe ba tun lokacin imamai zuwa yau har bayyanar sahibul asr imam Mahadi (a.s) suna bayanin hukunce-hukuncen fikihu da yadda za a kafa dalili daga dalilan shari’a abin da aka fi sani da Ijtihadi da Istimbadi suna masu tsara su babi-babi.
Ya fara tun daga babin tsarki, salla, zakka, azumi, har zuwa haddi da gado. Kuma sananne ne cewa shagaltuwa da bahasin kafa dalili na fikihu shi ne yake kusantar da dalibi mai azma zuwa ga matsayin ijtihadi.

 Bude Kofar Ijtihadi
Yayin da kofar ijtihadi a fikihun musulunci take bude gun mabiya mazhabar Ahlul-bait (a.s) wannan ya sanya sun samu cigaban ijtihadi da koyar da shi, da kuma cigaban ilimi da ya damfara da wannan ci gaban fikihu wanda yake da asasi daga Ilimin usul.
Sannan sauran ilimomi ta janibobi daban-daban su biyo baya, da suka hada da Ilimin Larabci; kamar nahawu da sarfu da balaga da ilimomin hankali kamar mandik da falsafa, ilimin rijal da diraya da waninsu. Kuma Hauza ta cigaba kamar itaciya mai fitar da 'ya'ya a kowane lokaci da kowane wuri.
Sai Allah ya sanya wannan ilimi mai albarka ga wasu gwarazan mutane masu zurfafawa a cikin bahasi suka kuma gano sababbin ilimomi da wadanda suka rigaye su ba su gano ba, haka nan ilimin fikihu da usul dinsa suka rika cigaba da daduwa da fadada.
A nan kana iya gani a fili cewa Hauza duk da ta kasance tana yakar zaluncin duniya, kuma ana yi mata makirci iri-iri sai dai da godiyar Allah har yanzu ba ta gushe ba ta na mai raya ilimomi, kuma tana taskace da malamai tsarkaka, kuma tana cika makil kullum da masana da ma’abota hadisai daga kowace irin jama’a, suna masu sha daga ilimomi tsarkaka, suna masu koshi daga fannonin ilimi daban-daban, sannan sai haskensu ya watsu sasanni ya yadu a cikin garuruwa domin mutane su haskaka daga iliminsu da tsoronsu ga Allah.

Fikihun Shi’a:
Tarihin fikihun shi'a yana komawa ne zuwa ga annabi (s.a.w), domin shi’anci ya faro ne da faruwar sakon Manzo (s.a.w) domin shi ne ran musulunci kuma makarantarsa, domin fikihun shi’a ya faru ne tare da faruwar musulunci kansa lokacin da aka umarci manzon rahama da ya gargadi makusantansa da kuma gargadi garesu kamar yadda ya zo a ruwayoyi masu yawa tun daga ranar farawar kiran musulunci tun farko. Kuma babu wanda ya isa ya yi inakarin hakan sai mai makauniyar gaba da Ahlul-bait (a.s) mai musun gaskiya. Sannan fikihun shi’a ya samu kammala a tsawon zamani da samuwar imamai (a.s). Sannan sai ya daukaka a lokacin ijtihadi, da ya fara daga fakuwar imam Mahadi babba zuwa yau.
Fikihun shi’a ya fara da tattararrun hadisai ne, da usul guda dari hudu a littattafan al'hada’ikun nadira da jawahirul kalam. Kuma makarantun fikihu sun samu daukaka da cigaba a tsawon tarihinsu da yake cike da nasara da dacewa da aiki da cigaba ba tare da gajiya ba, jirginsa yana mai keta kumfa mai karo da juna da ambaliya domin ta kai ga gaba cikin nutsuwa, sai ta samar da cigaba da wayewa, dan Adam kuwa ya samu daukaka sakamakon kyautar wadannan ilimomi domin rabauta da sa’adarsa.
Fikihu ya kasance kuma ba zai gushe ba shi ne kashin bayan rayuwar mutane da dukkan janibobinta na tattalin arziki da siyasa wadanda suke kunshe a addinin Allah mai sauki.

Makarantun Fikihu Gun Shi’a Imamiyya:
Sanannen abu shi ne cewa zamani da waje da malamai da kuma buduwar kofar ijtihadi, da kubutaccen hankali, da kuma karfin dalili, da kafuwarsa; suna da tasiri matuka wajan samar da fikihun shi’a da kuma cigabansa da kuma daukakar Hauzozi da manyan makarantu, wadanda suke da rassa daban-daban a kasashen msulmi da makamantansu, sai dai wadannan makarantu sun wuce marhaloli daban-daban a zamunan da suka gabata kamar haka:
 1-Makarantar Madina: Wannan makarant ta fara daga da’awar manzo (s.a.w) da sakon musulunci, ita ce ta farko ta sakon Allah na shari’a bayan Makka, ta samu dalibai kamar Ahlul-bait (a.s) da wasu daga manyan sahabbai masu neman ilimi, da jama’a masu yawa daga sasannin kasar musulunci, musamman bayan saukar ayar nafar, makarantar ta cigaba har zuwa tsakiyar karni na biyu bayan hijira. A lokacnin imam Sadik (a.s) gidansa ya zama jami’a ce babba kuma matattara mai girma ta musulunci.
2-Makarantar Kufa: Ta bayyana a tsakiyar karni na biyu sannan ta cigaba har rubu’in karni na hudu na hijira, wato farkon buyan imam Mahadi (a.s) babba, ta daukaka da mazajen ilimi da masu ruwaito hadisai na fikihun shi’a, Kufa ta kasance a wannan lokaci ita ce cibiyar ilimin fikihu na shari’a kuma kambin ilimi a duniyar musulmi, har sai ka ga maruwaicin hadisi ya shiga masallacin Kufa, sai ya ga sama da mutum dubu hudu kowanne malami ne kuma mai ruwaito hadisi dukkkaninsu suna cewa imam Sadik (a.s) ya ba ni labari cewa…
Sai Kufa ta zama daga manyan cibiyoyin musulmi kamar yadda zata sake komawa yayin bayyanar imam Mahadi (a.s) imam Sadik ya zauna a Kufa shekar biyu yana ba wa mutane hadisan kakanninsa tsarkaka, wannan kuma dama da fikihun shi’a ya samu ya faru ne bayan damar da ya samu ta hanyar faduwar hukumar umayyawa, da kuma kafuwar hukumar abbsawa.
3-Makarantar Kum da Rayyi: Ta bayyana a rubu’in farko na karni na hudu, ta shahara har zuwa rabin farko na karni na biyar (lokacin Sayyid Murtada Alamul Huda da Shaihud Da’ifa Shaikh Tusi) kuma ta fitar da maruwaita hadisai manya, jagorancin makarantu a lokacin ya kasance a hannun ash'arawa da kuma zuriyar Saduk (R), kuma ana yi mata kirari da shekar alayen Muhammad, kuma waje ne da ya samu karbuwa ta musamman a wajen Ahlul-baiti (a.s) kuma ita ce haraminsu (a.s).
A cikin garin Kum a lokacin shaikh Saduk (R) akwai masu ruwaya dubu dari biyu, tana da makarantu da masallatai da laburare da kuma majalisan bahasi da koyarwa da tattaunawa da majalisan karatu da muzakara kamar yadda yake a wanan zamani namu, sai dai ta kare tun wannan lokaci, sannan sai ta sake dawowa da ayyukanta a wannan zamamani ta hannun Ayatullahi Uzuma Shaikh Abdulkarim Ha’iri (R), a yau ita ce mafi giman Hauzar shi’a, kuma tana dauke da sama da masu neman ilimi dubu arba’in, kuma daga nan ne ilimi yake yaduwa zuwa duk duniya, har ta isa zuwa ga mata cikin dakunansu.
4-Makarantar Bagadaza: Ta bayyana a rabin farko na karni na biyar har zuwa lokacin da Holakon Tatar na Magol ya mamaye garin Bagadaza, daga cikin manyan malaman da suka jagorance ta akwai shaikh Kulaini da shaikh Dusi, da shaikh Mufid da sayyid Alamul huda (K) da sauransu, na daga manyan mutane da suka fito daga manyan gidaje, makarantar ta fadada, kuma usulul fikhu na shi’a ya daukaka, bayan Kum da Rayyi. 
Ya kasance sama da mutane dari uku mujtahidai malamai masana fikihun shi’a ne suke halartar karatun shaikh Dusi (K) da kuma mutanen gari da ba wanda ya san adadinsu.
5-Makarantar Hilla: Ta bayyana a lokacin da aka mamaye Bagadaza a hannun shahid As'sani (K) daga malamanta akwai Muhakkik Alhilli da kuma Allama Hilli (K).
6-Makakarantar Najaf: An kafa ta kusa da kabarin imam Ali (a.s) kafin shekara dubu da ‘yan kai, da zuwan shaihud Da’ifa shaikh Dusi (K) har zuwa yau, kuma alkalami da harshe ba zasu iya bayanin darajojin Hauzar Najaf ba, da kuma irin manyan mutane da ta fitar masu girma da babu kamarsu a duniyar musulmi.
Akwai wasu makarantu kamar makarantar Samarra da Karbala da Kazimiyya da Isfahan da Mashhad da sauransu, kuma wadannnan hauzozi a yau sun zama kamar taurari ne masu haske a sama da daukaka da falala a kowane bangare na ilimi.
Dukkan wadannan makarantu na fikihu na ilimi duk sun shayo ne daga gidan wahayi da annabta da isma da tsarki, kuma asasinsu daga farfajiyar annabi ne da alayensa tsarkaka, sannan sai malamai suka dauki nauyin ganin rike su da kare su da kula da su da himmantuwa da su a tsawon zamani.
Sannan farkon wanda ya rubuta littatafan fikihu da hadisai da zurfinsu ya kasance a lokacin imam Bakir (a.s) duk da tun farko an fara a lokacin imam Ali (a.s) da dalibansa (R).
Imam Sadik (a.s) yana kwadaitarwa kamar yadda ya karbo daga kakansa mafi girma (s.a.w) a kan rubutu, saudayawa ya ce: "Ku rubuta hakika ku ba kwa iya kiyayewa sai da rubutawa, kuma kiyaye ilimi da rubutu ne". Sannan akwai littattafai na ruwayoyi da sahabbansu da masu ruwaya suka rubuta.

Masdarin Fikihun Shi’a: Fikihun shi’a yana da usul da furu’a da suka dogara a kan madogarar shari’ar musulunci wadanda su ne: 
1. Kur’ani mai girma
2. Sunnar Annabi da ta hada da magana ko aiki ko tabbatarwar ma’asumai (a.s).
3. Ijmai'i: Wato haduwar malamai
4. Hankali
 Amma ijma’i da hankali wadannan a bisa hakika suna komawa ne zuwa ga littafi da sunnan.
Amma malaman fikihun sauran mazhabobi wasunsu sun riki kiyasi kamar hanafiyya mabiya Abu Hanifa, kamar yadda suke riko da istihsani, a gefe guda kuma akwai makarantun sunna mabiyan sunnan halifofi musamman ma halifa na farko da na biyu.
A irin wadannan mazhabobi iri-iri da suke cike da sabani mai yawa, wannan al’amarin ya sanya imamai (a.s) suka kafa wasu dokoki da a kan su ne za a bi domin fitar da hukuncin shari’a, domin haka ne suka koyar da wadannan dokoki da asasai ga malamai da masu ruwayar hadisai, kamar yadda ya zo a hadisansu (a.s): "Yana kanmu mu koyar da ku usul ku kuma ko rarrabe”. sai suka sanya usul da dokoki na farko kamar istishabi da bara’a da ihtiyadi da zabi a lokacin kokwanto ko rashin dalili ko ya zama dunkulalle ko kuma karo da juna, da sauransu na daga ka’idoji, kamar ka’idar tsarki da ta hannu da ta halacci, da sauransu, wadanda zasu taimaka wa malami wajan fitar da hukuncin shari’a.
Malaman fikihu da usul sun yi bayanin wadannan ka’idoji da fadadawa wadanda suka samar da sabon tsari mai fadi na fitar da hukuncin shari’a.


Muhimmancin Hauza A Shi’anci
Makarantun fikihu su ne madafa ta farko na cigaban ilimi da tunani ga kowane shi’a duk inda yake, domin shi’anci a yau bai gushe ba yana samun haske daga akida da akhlak da kuma ayyuka a matsayin daidaiku da kuma jama’a gaba daya, daga hauzozi da marja’o'i.
Duk da wahalhalu da takura akai-akai daga azzalumai da kuma masu mulki amma fikihun shi’a da godiyar Allah bai gushe ba yana nan da karfinsa da nishadinsa, da ilimomi suke bubbugo-wa daga garesu daga fannoni daban-daban, kuma malamai da masu ruwaya ba su gushe ba suna karfafa zukatan mutane da kuma gina hankulansu.
Malaman shi’a sun wallafa littattafai masu yawa da suka kai dubunnan daruruwa, da abin da yazo a cikin littafin "A’ayanus Shi’a" kadai ya ishe ka misali na Sayyid Muhsin Al’amuli da kuma littafin "Zari’a Ila Tasanifis Shi’a” na Shaikh Buzurg Tehrani (K).
Abana bn Taglib yana daga cikin masu ruwaya da ya rawaito hadisai dubu talatin da Muhammad bn muslim da ya rawaito dubu arba’in da sauran irinsu da suke da yawa, har Zahabi yana cewa a littafinsa na Mizanul i’itidal: Da mun cire ‘yan shi’a da suke cikin sanadin hadisai da muke da su da ba wani abu da zai rage mana na sunna a hannunmu sai kadan kwarai.
Sai dai wasu mutane masu makahon tunani sun jahilci muhimmancin hadisan shi’a da masu ruwayarsu, sai dai Allah yana nan tare da mai gaskiya, kuma fikihun alayen Muhammad (a.s) ya zama haske mai walwala a goshin musulunci.
Daga karshe muna neman Allah madaukaki ya game mu da rahamarsa da dacewarsa, ya sanya shi mai amfani ga dukkan musulmi baki daya.

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
Tuesday, October 13, 2009 - Shawwal 24, 1430 - Mihir 21, 1388
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: