bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      21:58:54
A nan zamuyi kokarin ganin cewa wannan kalma ta (maula) me take nufi a cikin wannan
Lambar Labari: 264
KAFA HUJJA A KAN HADISIN GHADIR
Daya daga cikin Hadisi mafi muhimmanci shine Hadisin da yake Magana akan wilaya da kuma shugabancin shugaban muminai Aliyu bn Abi Dalib (a.s)  shine Hadisin Ghadir Kum. Manzon Allah (s.a.w) a ranar Ghadir Kum, a hudubarsa ta Ghadir, ya mai maita wannan jumlar akan Aliyu (a.s) ga dukkanin musulmai yake cewa: { من كنت مولاه فهذا علي مولاه} duk wanda na kasance shugabansa to Aliyu ma shugabansa ne. duk da cewa wasu daga cikin Ahlussunnah, da yake sunfahimci wannan hadisin mutawaturi ne ba zai yiwu a karyata shi kaitsaye ba, to sai sukayi kokarin yi mashi tawili akan wannan kalma ta ( maula ) da cewar tana nufin aboki; ba wai shugaba ba.
    A nan zamuyi kokarin ganin cewa wannan kalma ta (maula) me take nufi a cikin wannan hadisin shin tana nufin abokine ko kuwa shugaba take nufi a cikin wannan Hadisi na Ghadir Kum.
1 A littattafan Ahlussunnah, wannan hadisin bai zo da kalma daya ba wato Kalmar ( maula ) din, sai dai yazo da kalmomi daban-daban; yazo da kalmomi kamar haka: { مولا, ولي, أمير,}, Saboda haka idan a Kalmar (maula) akwai yuwar tanada wata ma’anar bata shugaba ba, ko kuma zata bada wata ma’anar ta daban; to ai a Kalmar ( Amir ) ba bu wannan ihtimalin. Daya daga cikin wasu ruwayoyin akan wannan hadisi na Ghadir itace ruwayar da take cewa: { من كنت أميره فعليّ أميره} wanda duk na kasance shugabansa to Aliyu ma shugabansa ne. wannan kam ba wani tawili a cikin wannan ruwayar.
2 A cikin Alkur’ani mai girma Kalmar (maula) tazo a wurare daban-daban. Wanda kuma a littattafan Tafsiri na Ahlussunnah, wadannan kalmomin sun fassara su da ma’anar shugaba ne, misalin haka kuwa shine a suratul ma’ida yazo: { قل لن يصيبناالاماكتب الله لنا هو مولانا...} ta yadda malaman Tafsiri na Ahlussunnah suka fassara wannan kalma ta (maula) da ma’anar mai taimakonmu mai bamu kariya ( wato shigabanmu). Hakama kuma a suratu ( Muhammad ) yazo da irin wannan ma’anar: { ذلك بأن الله مولى الذين ءامنوا وأن الكافرين لا مولالهم} Inda ita ma wannan aya malaman Tafsiri na Ahlussunnah suka fassara Kalmar (maula) da ma’anar shugaba.
3 Manzon Allah (s.a.w) a hudubar da ya yi a Ghadir Kum,ya tambayi mutane  cewa: { ألست أولي بكم من أنفسكم؟ قالوا بلي يا رسول الله.من كنت مولاه فهذاعلي مولاه. اللهم وال من والاه وعا د من عا داه وانصر من نصره واخذل من خذله  } shin banfiku cancanta akan kawunan ku ba? Suka ce hakane ya ma’aikin Allah! Sai ya ce: to duk wanda na kasance shugabansa wannan Aliyu ma shugabansa ne. Allah ka jibinci duk wanda ya jibince shi kayi gaba da duk wanda ya yi gaba dashi kuma ka tai maki duk wanda ya taimake shi. Shin duk wannan bayanin da Manzon Allah (s.a.w) ya yi ya so ya nunawa mutane Aliyu (a.s) abokinsa ne kawai? Shin wannan bayanin ashe baya nuni da cewa Manzon Allah (s.a.w) ya nasafta Aliyu (a.s) a matsayin shugaba ne?
4 Bayan Manzon Allah (s.a.w) ya gama yiwa mutane hudubar Ghadir, mawakan larabawa a wannan rana sunyi wakoki daban-daban ta yadda suka sarrafa waccan hudubar ta Manzon Allah (s.a.w) kuma suka juyata zuwa waka. Daya daga cikin mawakan mai suna, Hisan bn Sabit da ke wurin wanda sannannen mawakin Manzon Allah (s.a.w) ne, ya yi waka da irin salon hudubar Manzon Allah (s.a.w) kamar haka: 
يناديهم يوم الغدير نبيّهم # بخم وأسمع بالرسول مناديا.    يقول فمن مولاكم ووليّكم# فقالوا ولم يبدوا هناك التعاميا.  الهك مولانا وأنت وليّنا # ولم تر منا فى الولاية عاصيا. فقال له قم يا علي فاننى # رضيتك  من  بعدى  اماما   وهاديا.                        Wannan waka ta Hisan bn Sabit tana tabbatar mana da wannan kalma ta ( maula ) ta nufin shugaba ne kuma Manzon Allah ( s.a.w ) ya tabbatar da shi ranar ghadir a matsayin shuga.
5 Daga cikin bayanin da Manzon Allah (s.a.w) ya yi  wa mutane a ranar Ghadir, akwai inda yake cewa: idan Aliyu (a.s) ya yi muku umarni ku aikata abinda ya umarce ku, zaku same shi shiryayye kuma mai shiryarwa domin Aliyu (a.s) ahlin shiriya ne kuma kuma zaku shiryu dashi.
6 A hudubar Ghadir, hadisin Ghadir ya kara tabbatar wa da mutane Tauhidunsu da kuma shadarsu tunta farkon shiga musuluncin su. Ta yadda a cikin bayanin da ya yi wa  mutane Manzon Allah (s.a.w)  ya ce: { يا أيهاالناس بما تشهدون؟ قالوا: نشهد أن لا اله الاالله قال: ثم ماذا؟ قالوا وأن محمدا عبده ورسوله  قال: فمن وليّكم: قالوا : الله ورسوله مولانا ثم ضرب بيده الى عضد علي, فقامه فقال: من يكن الله ورسوله مولاه  فان هذا مولاه. { Ya ku mutane da me kuka shaida? Sai suka ce: Munshaida da babu wani Ubangiji sai Allah, sai ya ce: sannan sai me? Sai suka ce: kuma munshaida tabbas Muhammad Bawansa ne kuma Manzonsa ne, sai ya ce: waye shugabanku? Sai suka ce: Allah da Manzonsa sune shuwagabanninmu, sannan sai ya kama hannun Aliyu ya dago shi sannan ya ce: duk wanda ya yadda Allah da Manzonsa sune shugabansa to wannan ma shigabansa ne.
7 Sannan Manzon Allah (s..a.w) ya kamala bayani da kawu hadisin Ghadir ya yi wasu kebantattun kabbarori, inda ya rinka cewa: الله أكبر على اكمال الدين واتمام النعمة ورضا الربّ برسالتى والولاية لعليّ من بعدى . Allah mai girma ya cika addini ya kuma cika ni’ima kuma Ubangiji ya yadda da sakona da kuma wilaya ga Aliyu a bayana.
8 Sannan Manzon Allah (s.a.w) a wannan hudubar, ya bada labarin cewa ya kusa yin wafati wato kamar yana bankwana da Al’ummarsa ne, shi yasa ake cewa da wannan hajjin hajjin bankwana Manzon Allah (s.a.w) hajjin bankwana. Inda yake cewa:  {كأنى دعيت فأجبت} (kamar ankirani na kusa amsawa) ma’ana Ubangiji ya kusa kirana ni kuma na kusa amsa kira. Daya daga cikin mas’alar da shugaba yake gabatarwa a karshen rayuwarsa itace mas’alar shugabanci da sanar da mutane wanda zai gaje shi bayan mutuwarsa. Manzon Allah ( s.a.w) ya sanar da mutane cewa Aliyu ne zai zama shugaba bayan wafatinsa.
9 Sannan bayan gama hudubar Annabi a ranar Ghadir ya yi wa mutane umarni da suyi masa murna shida Aliyu (a.s); { هنّئونى هنّئونى.} sannan kuma ya bada umarnin cewa a yi wa Aliyu (a.s) murna da unwanin shugaban Muminai; { سلّموا على عليّ بامرة المؤمنين وقولوا: الحمد لله الذى هدانا لهذا وما كنا لنهتدي لولا أن هدانا الله فان الله يعلم كل صوت وخائنة كل نفس فمن نكث فانما ينكث على نفسه ومن أوفى بما عاهد عليه الله فسيؤتيه أجرا عظيما... } Kuyiwa Aliyu (a.s) murna da unwanin shugaban muminai sai suka ce: Godiya ta tabbata ga Ubangiji wanda ya shiryar damu da wannan ( ma’ana wilayar Ali ) wanda ba dan ya shiryar damu ba da baza mu shiryu ba, Tabbas Allah ya san ko wace fuska da tayi ha’inci da kuma ko wace rai, duk wanda ya yi ha’inci to kanshi ya yi wa ha’inci wanda duk kuma ya cika alkawarin da ya yi wa Allah to da sannu zai bashi lada mai girma…  Daga nan sai Umar dan khaddabi ya taso ya cewa Aliyu (a.s): Kai ina yi maka murna ya kai dan Abu Dalib, ka zama shugabana da shugaban ko wane mumini da mumina. Ko kuma kamar ruwayar da tafi shahara madalla madalla da kai ya dan Abu Dalib. { هنيئا لك يابن أبى طالب, أصبحت وأمسيت مولاي  ومولى كل مؤمن ومؤمنة. أو بخّ بخّ لك يا بن أبى طالب   .  shin duk wannan ba dalili bane na cewa wannan Kalmar ta ( maula ) tana nufin shugaba bane?
10 Kuma sannan bayan Annabi ya gama hudubar Ghadir din, ya nemi gaba dayan musulmai Maza da Mata da suyiwa Aliyu bn Abi Dalib (a.s) bai’a daya bayan daya. Kuma haka suka tashi suka aiwatar da wannan umarnin na Manzon Allah (s.a.w) wanda Umar bn Khaddabi shine mutum na farko da ya fara yiwa Imam Ali (a.s) bai’a.
11 Haka kuma dai bayan gama hudu a wannan lokacin Manzon Allah (s.a.w) ya yi ta’akidin cewa lallai wanda yaji ya sanar da wanda bai jiba, wanda yazo ya sanar da wanda bai zo ba. { فليبلّغ الشاهد الغائب} wannan duk wace ma’ana yake dashi? Ma’anar Aboki kawai ko kuma kawai Manzon Allah (s.a.w) yana son nunawa mutane cewa yana son Ali ne ko kuma Aliyu (a.s) Abokinsa ne? wannan bai kamata ma mutum mai hankali ya fadi irin wannan maganar ba.
Wannan Shine karshen wannan bayani da zamu iya kawu a nan, munyi Magana a kan abinda ya faro a ranar Ghadir wato ranar 18 ga watan zul hijja hijira na da shekara 10, sannan kuma mun kawo muku bayanai akan hudubar da Manzon Allah (s.a.w) ya yi a wannan wuri da yadda ya nasabta Aliyu bn Abi Dalib (a.s) a matsayin khalifansa, mun kuma kafa hujja akan hadisin Ghadir musamman ma a littattafan Ahlussunnah munga kuma yadda ma’anar Kalmar maula take a wannan hadisi na Ghadir.
 Shiriyar Allah ta kara tabbata ga wadanda suka ga shiriyar kuma suka bita batareda wani shakku ko taraddudi ba. Wassalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: