bayyinaat

Published time: 12 ,October ,2018      22:11:22
Shi ne mai yin ayyukansa bisa yanayin da ya tabbatar da ya yi su daidai
Lambar Labari: 266
Mas'aloli Game Da Koyi Da Malami Mujtahidi
1 >(m.1) Bai halatta ba a yi dogaro da fatawar wani a cikin shika-shikan ginshikin addini, domin wannan yana nufin karbar maganar wani ba tare da dalili ba. Don haka wajibi ne a akida ta kasance ta doru bisa dalili, koda kuwa a dunkule ne.
 Amma hukunce-hukuncen ayyuka na rassan addini  an ba wa baligi zabi da ya kasance:-
1- Mujtahidi; Sai ya tsamo hukunce- hukuncen addini daga matsamar dalilansu (Kur'ani da sunna da hankali da ijma'in malamai) bayyanannu.
2- Ko Mukallidi; Mai biyayya ta hanyar karbar fatawar mujtahidi don aiki da ita.
3- Ko Muhtadi; Shi ne mai yin ayyukansa bisa yanayin da ya tabbatar da ya yi su daidai, ga misali; idan wasu gungu daga mujtahidai suka haramta wani abu, wasu kuma suka halatta shi, sai ya bar wannan abin. Idan kuma sashinsu, ya wajabta wani abu dayan kuma ya mustahabbantar da shi, sai ya aikata shi, da haka zai zama mai kamanta hukunce-hukuncen shari`a gwargwadon yadda suka hau kansa. 
Saboda haka idan har baligi ba mujtahidi ba ne, kuma ba muhtadi ba ne, wajibi ne ya yi taklidi (ya yi aiki da fatawa) 
2 > (m.2) Taklidi shi ne yin aiki da fatawar mujtahidi, kuma dole mujtahidin ya kasance:
Namiji
Mai hankali
Mumini
Rayayye
Mai tsarkin haihuwa
Adali: Shi ne wanda yake aikata wajibi kuma yake barin haram
Mafi ilimin mujtahidan zamaninsa
 3> (m.11) Wajibi ne baligi ya nemi sanin mas`a`lolin da suke ba shi matsala (da yake fuskantar su) a mafi yawan lokuta. 
Hukunce-hukuncen Najasosi
"A cikinsa akwai mutane da suke son su tsarkaka lallai Allah yana son masu tsarki". Kur`ani mai girma.
"Tsafta Tana Daga Cikin Imani", Hadisi madaukaki.
"An Gina Musulunci A bisa Tsafta", Hadisi madaukaki.
 4> (m.84 dab) Najasosi su ne:-
 1, 2- Bawali da Gayadi: Idan suka kasance daga dan Adam ko dabbar da aka haramta cin namanta bisa sharadin kasancewarta wacce take da jini mai gudana (ta yadda idan aka yanke jijiyoyin wuyanta jini zai fita tare da zuzzubowa da tunkudowa).
Kashin tsuntsu ba ya cikin wannan lissafi, hatta wanda aka haramta cin naman sa.
 3,4 da 5.- Maniyyi, mataccen abu, da kuma jini: na dan Adam da ma na dukkan dabbar da take da jini mai gudana, face jinin da ya kan yi saura a cikin naman abin da aka yanka, hakika wannan mai tsarki ne bayan fitar jini na dabi'a (gwargwadon yadda aka saba).
 6 da 7- Kare da Alade na doron kasa, (banda na ruwa) da dukkan abin da ke jikinsu, na daga gashi da kashi da farce da ma dukkan dansashe-dansashensu (kashi da fitsari dss), dukkanin (abin da ke fita daga jikinsa).
 8- Kafiri: Kafiri najasa ne da dukkan yanki-yankinsa da dansoshin sa (abin da ke fita daga jikinsa)  
Kafiri shi ne wanda yake musunta samuwar Ubangiji, ko yake yin shirka da shi, ko yake musa annabcin Cikamakin Annabawa (S.A.W), ko kuma wanda ya musanta daya daga larurorin addinin musulunci, kamar salla da azumi.
 9- Giya. Giya najasa ce haka ma dukkan abin da ke sa maye, idan ya kasance narkakke ne a asali.
 10- Burkutu. Ita ce abin sha mai sa maye da ake yin ta da alkama ko sha`ir ko masara da sauransu. Ita ma najasa ce, amma ruwan sha'ir din da ake amfani da shi bisa horon likita, mai tsarki ne. 
 11- Gumin Rakumi mai cin najasa, (wanda ya ke cin gayadin dan Adam) shi ma najasa ne.
 5> (m.126) Da najasa za ta fada cikin tukunya a lokacin da take tafasa, abincin da tukunyar sun najastu, tafasar tukunya da zafin ta ba sa tsarkake su.
 6> (m.142) Haramun ne cin najasa ko shan ta haka ma sabbabawa wani cinta ko shanta.
 7> (m.126) Idan wani abu mai tsarki ya hadu da najasa, kuma ya zama dayan su ko dukkaninsu suna da danshi mai naso, to mai tsarkin ya najastu.
 8> (m.124) Idan yana da masaniya da najastuwar wani abu, kuma sai ya yi shakku a kan tsarkinsa, to najasa ne. Idan kuma yana da masaniya da tsarkin wani abu sai ya yi kokwanto a kan najastuwarsa, to tsarkakakke ne.
 9> (m.136) Haramun ne najastar da takardar Kur'ani ko rubutunsa, haka ma dukkan abin da aka rubuta sunan Allah Ta`ala a kansa ko sunan Annabawa (A.S) ko dayan Imamai (A.S). Idan daya daga cikin wadannan abubuwa da aka ambata ya najastu ko ya fada a waje mai najasa, wajibi ne a fitar da shi a tsarkake shi da gaggawa.
 10> (m.59-64-80-81) Haramun ne tsuguno (kama ruwa) tare da fuskantar alkibla da gaban jiki, haka ma ba alkibla baya. Kamar yadda ya haramta biyan bukata (kashi ko fitsari) a kan hanya ko kwararo ko lokon (da ba ya bullewa) sai da izinin masu wajen, ko a cikin mulkin wani ba tare da izininsa ba, ko a cikin wuraren da aka yi wakafinsu ga wasu mutane na mussamman, kamar sashin makarantun addini wadanda aka yi wakafin su ga daliban makarantun addini, kuma an karhanta biyan bukata a tituna da hanyoyi, da kusa da kofofin gidaje da karkashin bishiya mai 'ya`'yan itaciya, da kasa mai fako da gidajen kananan kwari, da cikin ruwa musamman ma wanda yake tsaye, kamar yadda ba a son yin bawali a tsaye. 
 Istibra`i mistahabbi ne ga maza. Amfaninsa shi ne samun yakini da tsarkakar magudanar bawali. Yadda ake yin sa shi ne: a matso/tatso tun daga mafitar gayadi har zuwa tushen al`aura da danyatsansa na tsakiya da kuma babban dan yatsa duka na hagu sau uku, sannan a matso/tatso tun daga tushen al'aura har zuwa karshenta sau uku, sannan a matse kan al`aura sau uku.
Hukunce-hukuncen Masu Tsarkakewa
"A cikinsa akwai mazaje masu neman tsarkaka, hakika Allah yana son masu son tsarkaka". Kur`ani Mai Tsarki.
 "An sanya kasa a gare ni wajen sujjada da tsarki". Hadisi Madaukaki.

Masu Tsarkakewa Guda Goma Su Ne 
1- Ruwa
2- Kasa
3- Rana
4- Canjawa
5- Ciratuwa
6- Musulunci
7- Bibiya
8- Gushewar ainihin najasa
9- Tsarkake dabba mai cin gayadin mutum
10- Boyuwa ko nisantar musulmi.
 
Ruwa 
 11> Za a iya yin amfani da ruwa mudlaki (wato ruwa da bai jirkita ba) don wanke abubuwa da suka najastu.
 12> (m.47- 48) Ruwa mai jirkita (ana cewa da shi mudhafi) (shi ne wanda yake daga wani abu kamar ruwan Ruman, ko wanda aka cakuda shi da wani abu, ta yadda ba za a kira shi da sunan ruwa kai tsaye ba, kamar idan aka cakuda ruwa da kasa ko makamancinta) ba zai tsarkake najasa ba, kuma alwala da wanka ba sa inganta da shi, kuma ruwa majirkici yana najastuwa idan ya hadu da najasa koda kuwa ya kai gwargwadon kur ko sama da haka. 
 13> (m.16-17) Ruwan kur (shi ne mai nauyin Kilogram 376) ko wanda gaba dayan yawan sa ya kai (kamun rutsin 'yanyatsu 43) ta bangren tsawo da fadi da zurfi. Kuma ruwa kur ba ya najastuwa da saduwa da najasa, har sai in launinsa ko dandanonsa ko kanshinsa sun canja, kuma za a iya tsarkake abin da ya najastu da ruwan kur.
 14> (m.28-29-44) Ruwa mai gudu (wanda yake bubbugowa daka kasa kuma yake gudana a kanta kamar idaniyar ruwa da tafkuna) to hukuncinsa hukuncin ruwan kur ne, koda bai kai yawan kur ba.
 15> (m.37) Najestaccen abu yana tsarkaka idan ruwan sama ya dake shi bisa sharadin tabbatar da yanayin da za a kira shi da dukan ruwan sama, don haka kenan yayyafi ba ya isarwa.
 16> (m.150-151) Kwanukan da suka najastu suna tsarkaka idan aka wanke su sau uku da ruwa kankani, amma a hukuncin ruwa idan ruwa ya kasance kur ne ko ruwa mai gudana, to ya isar a wanke su sau daya bayan gusar da ainihin najasa. 
 17> (m.151) Kwanon da kare ya yi lallage a cikinsa (wato; ya sha ruwa ko wani abu narkakke a cikinsa ko kuma ya lashe shi da harshensa) yana tsarkaka ta hanyar wanke shi da kasa mai tsarki da farko, sannan a wanke shi a cikin kur ko mai gudana sau daya ko kuma da kankanin ruwa sau biyu.
 18> (m.219) Wanda ya kasance yana wanke wani abu mai najasa, to hannunsa yana tsarkaka bayan tsarkakar wannan abin.
 
Kasa
 19> (m.184) Kasa tana tsarkake tafin kafa da kasan takalmi, idan najasar jikinsu ta gushe sakamakon tafiya ko ta hanyar goge su a kasa ba bambanci tsakanin kasancewarta najasa ce ta ainihi kamar jini da bawali, ko kuwa abu ne da ya najastu, kamar tabon da ya najastu. Da sharadin kasar mai tsarkakewa ta kasance turbaya ko dutse ko shimfidaddiyar farar kasa da makamancinta, amma tafin kafa da kasan takalmi ba sa tsarkaka ta hanyar yin tafiya a kan tabarma. 

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: