bayyinaat

Published time: 11 ,November ,2018      22:53:35
Muhimmancin soyaiya a nan ba karamin abu ba ne domin ita ce kashin bayan tafiyar juna da hadin kai domin gina rayuwa mai ma’ana da rabauta, kuma hanyar samar da iyali masu annashuwa da nagarta.
Lambar Labari: 269
Soyaiya tana bambanci tsakanin kafin aure da bayan aure domin kafin aure tana da sauki tun da kowanne ba ya jin yana da wani nauyi da dayan yake da shi a kansa, amma bayan aure a nan ne za a iya sanin cewa waccan soyaiyar ta farko bisa gaskiya take ko karya ce.
Muhimmancin soyaiya a nan ba karamin abu ba ne domin ita ce kashin bayan tafiyar juna da hadin kai domin gina rayuwa mai ma’ana da rabauta, kuma hanyar samar da iyali masu annashuwa da nagarta. Duk wani aure da tushensa bai kasance kan soyaiyar gaskiya da nuna wa juna hakikanin abin da suke tunani kan junansu ba, to wannan auren a yi masa albishir da rushewa, da rashin kwanciyar hankali, da rashin jin dadin zaman tare. Wani abokina ya ba ni labari cewa, a lokacin da yake saurayi wata rana yana cikin addu'ar Allah ya ba shi mata ta gari, Sai wani tsoho ya ji shi, sai ya ce masa: Yaro ka ce Allah ya ba ka mata mai sonka, idan ka samu mai sonka, ka samu ta gari. ya ce: Bai san muhimmancin maganar ba sai da ya yi aure.
Kamar yadda muka samu daga wasu masu hikima cewa so kala-kala ne, kuma kowanne yana da mahallinsa, zamu ga kuma Shehu Dan Fodio da ya kawo kashe-kashen so  ya kasa su zuwa Son Imani, da Son Jini, da Son Kauna. Idan mun duba misalin Son Imani shi ne irin son da ake wa Allah da Manzonsa da jagororin addini. Saiyidi Ali (a.s) yana cewa: Da na sari hancin mumini da takobina wannan a kan ya ki ni da bai ki ni ba, kamar yadda da na tara wa munafuki duk duniya gaba dayanta a kan ya so ni da bai so ni ba, saboda an riga an hukunta ya kuma zartu a harshen Annabi Ummiiyi (s.a.w) cewa: Ya Ali! Munini ba zai taba kin ka ba, kuma munafuki ba zai taba son ka ba . Haka nan Imam Ali (a.s) ya taba yanke hannun wani barawo bayan barawon ya fita daga wajansa, sai wasu muminai suka hadu da shi a hanya suka ji yana ta yabon Amirul mimin (a.s), sai suka zo suka gaya wa Imam Ali (a.s) suna mamakin irin yabo da godiya da yake yi wa Imam din, Sai Imam ya yi umarni a ka kirawo shi ya mayar masa da hannun bisa karama da mu'ujiza. Barawon ya kasance yana furtawa da cewa ba abin da yanke hannun ya kara masa sai son Imam Ali (a.s) ! Idan mun lura son imani ya fi kowane irin so karfi, kuma a kan kare shi ana iya saba wa duk wani irin so!.
Amma idan muka duba sauran nau'o'in so da suka hada da Son Jini zamu ga shi ne son tausayi da kauna kamar irin son Uwa da Uba ko 'Ya'ya da suke yi wa junansu, so ne mai karfi da ba ya rabuwa duk yadda aka samu sabawa da juna, so ne mai cike da kauna da alakar jini mai karfi.
Sai kuma nau'in Son Kauna ko Kyawun Halitta Kamar son da wani yake yi wa wata domin yana ganin kyawunta ko da kuwa addininsu ya saba, kamar dai son da musulmi zai iya yi wa wata mata da ba musulma ba domin dabi’ar kyawunta. Ga wanda yake son mace kada ya duba kyau na halitta kawai ya kamata ya sa hankali ya duba so na farko wato imani da kyawawan dabi’u, kuma wannan shi ne zai iya sanya shi ya cimma nasarar kafa gida na gari.
Masu soyaiya suna da hadafofi daban-daban da soyaiyar da suke yi wa juna, wani lokaci suna da hadafi mai kyau wani lokaci kuwa hadafinsu ba shi da kyau, wasu ma samari ne da suke son kawai su yi lalata da budurwa su lalata mata rayuwa sannan su kauce su bar ta, wadannan ne aka fi sani da mayaudaran samari. Amma wasu samarin kuwa suna da addini da tsoron Allah da kunya da sanin yakamata da mutunta budurwa, kuma da gaske ne sun zo wurinta ne don su aure ta don kafa gida na gari mai albarka. Idan kuwa lamrin ya kasance haka ne to ya kamata a sanya hankali a soyaiyar da ake yi kafin aure, hasali ma bai kamata ya zama mun kira shi soyaiya ba da ma'anar da ake nufi a wannan zamanin domin lamari ne na neman aure kawai da sanya hankali don zabar abokin ko abokiyar rayuwar aure.
1. Soyaiyar Marasa Kunya
Kunya ce asasin da ya kamata ya kasance ga mai neman aure ko wacce ake neman aurenta, idan mutum ya kasance ba ya jin kunya to zai rasa duk siffofin kamala da ya dace da mutum, don haka ne ma wata ruwaya ta zo da cewa "... idan ba a jin kunya... to a yi abin da ka ga dama ..." tana mai nuni da cewa maras kunya duk abin da ya so yi na ashararanci sai ya yi. Yawancin masara kunya suna da wannan mummunan halin ne sakamkaon sun jahilci kansu da ubangijin da ya yi su, sai suka rungumi shedan a matsayin ubangijin aiyukansu.
Ba a son a samu shakuwa sosai sai da wanda za mu yi aure da shi bisa yakinin hakan, don haka irin soyaiyar da ake yi ta al’adun da suka shigo cikin al’ummar Hausa mai rusa kunyar samari da 'yan mata musamman daga yammacin duniya, ba ta da kyau matukar ba aure za a yi ba, domin sau da yawa takan kai ga aikata haram wanda zai yi tasiri a kan saurayi da budurwa har karshen rayuwarsu, kuma sau da yawa rayuwar ‘yan mata ta lalace ta hakan sakamakon irin wadannan miyagun al’adu. Sau da yawa mace mai saukin hali da samari sukan iya shawo kanta ta hanyoyi daban-daban wani lokaci ma har wani shakiiyi yakan ce da ita: Idan kika yarda da ni muka kwanta to lallai zan aure ki. Irin wannan da yake son sha’awa ne ba na Allah da Annabi ba da zaran ya san ta a ‘ya mace sai ya yi wurgi da ita ya watsar, ba ma zata san cewa mugu ba ne mai tsananin wulakanci sai idan ta samu cikin dan shege ta wannan mummunar hanya a lokacin ne zata san cewa ba ya kaunarta koda kwayar zarra.
Sau da yawa ‘yan mata suka kashe kan su saboda wannan mummunan hali da mayaudaran samari suka jefa su a ciki kuma rayuwa ta gurbace musu  suka koma abin tausayi bayan da suna abin haushi, ko kuma suka gudu daga garuruwansu ko ma suka haife dan amma suka yarda shi a kwararo suka gudu. Da yawa 'yan mata suna da saukin hali shi ya sa suka yaudaru da wuri, wasu kuma kwadayi ne yakan kai su ga fadawa irin wannan mummunan hali musamman idan saurayi yana zuwa wurinsu zance da mota ko yana ba su kudi mai yawan gaske, wasu kuwa lalacewar halaye ce ta sanya su yarda da fasikanci da samarin, don haka yana kan iyaye su rika sanin mene ne ‘yarsu take yi a waje kuma da wadanne irin kwaye ne take mu’amala, sannan kuma su waye suke zuwa zance wajenta da sunan suna son aurenta.
Idan mace ta lalace ta hanyar samun cikin banza sai mu ga al'umma tana kin ta ba tare da ta tsani saurayin da ya yi cikin ba, wani abin takaici ma saurayin yana iya zama mai burgewa gun wasu lalatattun samari, sai su rika zuga shi suna wane ka gama da ita, ai ka yi maganinta, ai nan ta ki yarda da mu, da sauran kalomomin da Allah yake fushi da masu yin su.
Yana da kyau wannan al'ummar ta fara daukar mataki mafi muni kan mayaudarin fasikin saurayin kafin ta fara kan wannan budurwa da ya yaudara mai karancin wayewa da sanin lamuran rayuwa, bai kamata ba a dora mata duk wata tsana ba tare da an dora komai kansa ba. Sannan yana da kyau a sanya tsananin fushin al'umma kan duk wani fasikin saurayi da ya yi wannan mummunan danyen aiki.
Sau tari matsalar cikin shige ta sanya canja wa 'yan mata garuruwa suka haife su a wasu garuruwan da ba a san su ba, kuma don kare mutuncinsu aka aurar da su irin wadannan 'yan matan ko ma aka aurar da 'ya'yan zina ba tare da an sanar da mai neman aurensu ba, wannan ya taso sakamakon gudun wulakanci da gori da kin yarda da aurensu da al'umma take yi ne. Bai kamata ba ga wanda ya zo neman aure a boye masa hakikanin wacce zai aura, haka nan bai kamata ba ga wacce aka zo nema a boye mata hakikanin wanda ya zo neman aurenta. Yana da muhimmanci al'ummar nan ta dora komai kan gaskiya ta kare hakkin masu neman aure samari ne ko 'yan mata, ta nisanci yaudararsu da kin gaya musu gaskiya, domin duk ranar da gaskiyar lamari ya baiyana gare su to wannan yana nufin rusa rayuwarsu baki daya.
2. Soyaiyar Masu Kunya
Samari da 'yan mata masu kunya su ne wadanda suka siffantu da kamalar addini da take hana su aiwatar da fasikanci, kuma tsoron ubangijinsu ya hana su fadawa halin ashararanci. A wannan bangaren ne muke samun samari da 'yan mata masu kamala da kame kai da sanin yakamata, samari da 'yan mata da tsoron Allah da son ambatonsa da wayewar tunani da kishin al'umma da sanin kansu suka mamaye su, sai suka kasance masu siffofin kamala da tunani da sanin ubangijinsu. Irin wadannan sune masu wayewa da sanin yakamta, suna iya kasancewa sun yi karatun boko ko kuma sun yi karantun islamiiya duk babu bambanci, kyawawan halayen siffantuwa da aiki na gari da abin da mutum ya sani gwargwadon iyawarsa ne muhimmi gun musulunci.
Irin wadannan samari da 'yan mata su ne wadanda suke duba irin hukunce-hukuncen Allah da muka kawo a bayanan sama sai suka aiwatar da su a rayuwarsu, suka zama suna kishin kansu da 'yan'uwansu sai suka nisanci lalata da fasadi, suka kasance masu bin shari'ar ubangijinsu sai suka nisanci miyagun halaye. Alakarsu da 'yan mata baki daya ko samari sun dora ta kan ma'aunin addini da koyarwar annabin rahama (s.a.w). wannan lamarin ne ya sanya su masu neman aure kamar yadda aka gindaya musu, masu alakar soyaiya da juna ba tare da ketare iyakarsu ba, nemansu da aurensu ya kasance bisa izini kamar yadda shari'a ta shata musu.
Duk da kunya ta kasance asasin kyawawan halaye a soyaiya da neman aure sai dai wuce gona da iri a wannan siffa yana cutar da ma'abocinta. Idan mun duba kowace siffa a kyawawan halaye ba a son takaitawa a cikinta ko wuce gona da iri duk biyun kuskure ne, wato kamar yadda ake kin maras kunya haka nan ma ake kin mai wuce gona da iri da sunan kunya ta yadda zai bar komai ya lalace da sunan kunya. Irin wadannan samarin da 'yan matan sun ga wadanda suke so daga salihan samari ko 'yan mata kuma suna da cancantar aurensu amma sai suka yi nauyin baki har wadancan samari ko 'yan mata suka kubuce musu suka auri wasu daban ba su ba, sai wannan ya zamar musu cewa a rayuwarsu da suke dandanan kudar azabar abin da ya kubuce musu har karshen rayuwarsu.
A irin wadannan samarin da kunya ta hana su fadin ra'ayin zuciyarsu akwai wanda ya yi kuka mai yawa ranar auren yarinyar kuma ya gaya mata yana son ta amma ya kasa fada sai ita ma wannan ya zama mata ciwo a rayuwarta domin tana matukar son sa fiye da kowane saurayi. A bisa shawara ga irin wadannan salihan samari da 'yan mata yana da kyau idan suka ga wanda suke so sai su sanar da shi/ita, idan kuwa ba zasu iya da kansu ba to akwai hanyoyin isar da sako masu yawan gaske a wannan zamanin. Suna iya sanar da su ta hanyar rubuta takarda ko aika musu abokansu/kawayensu don su sanar da su, ko kuma su aika musu da sako ta email, message, da sauran hanyoyin sadarwa.
Da wannan ne zamu san cewa ana son mai kame kai mai kunya amma a lokaci guda mai iya isar da sakon soyaiyarsa ga wacce yake so, ka da a rike soyaiya ba tare da baiyanar da ita ba matukar mun san da gaske muke kuma mun cika sharudan shelanta hakan. Kuma yana da kyau mu san cewa wanda duk ya furta yana son mu ta hanyar hankali da mutunci kamar ya aiko mutanen gidansu ko abokansa to da gaske mafi yawa soyaiyar gaskiya ce don haka ka da mu yaudare shi, idan ba ma son sa mu sanar da shi gaskiya ta hanyar da ba zai bugi zuciyarsa ba, amma idan ana son sa da gaske yana da kyau a sanar da shi. Sannan yana da kyau mu sani ka da mu wana wanda yake son mu ko mu yi masa wasa da hankali, sai mu fito fili mu sanar da shi abin da yake hakikanin zuciyarmu. Kuma idan muka san ba ma son mutum sai kuma muka samu shigar soyaiyarsa saboda halayensa na kirki to yana da kyau a sanar da shi hakan, a daya bangaren kuwa shi kuma yana da kyau ya san ana iya ki yau gobe kuma a so saboda baiyanar wani lamari.
Mas'aloli ne masu yawan gaske, sai dai a cikin takaitaccen bayanin da muka gabatar akwai abin lura ga masu tunani.

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: