bayyinaat

Published time: 11 ,November ,2018      23:11:43
Aure alaka ce kebantacciya ta shari’a ko al’ada wacce ake kulla ta tsakanin mace da namiji, da lafazi na musamman,
Lambar Labari: 270
BANGARE NA BAKWAI
A nan kuma zamu yi bayani ne kan Hikimar aure da muhimmancin sanya hankali wurin zabar juna, sai kuma bahasin gina iyali da hadafin aure a matsayin abin da zai shata manufar yin aure tun farko. Daga nan kuma sai muka shiga bayanin wanda za a zaba da wacce za a zaba don tafiyar rayuwar tare tare da bayanin sharuda da siffofinsu, sai kuma batun da ya shafi neman aure da yadda ake yin sa da kuma yadda ake kulla shi da sharudan kulla auren kamar sadaki da siga tare da bayanin wadanda suka haramta a aura da wadanda suka halatta na daga maza da mata. Sannan sai muka shiga bayanin Wali ga budurwa da sharudansa da muhimmancinsa saboda abin da rashin kiyayewa yake haifarwa na matsaloli a rayuwar 'yan mata. Daga nan kuma sai muka shiga bayanin angwanci da amarci da bukin aure duka cikin bayanai masu zuwa kamar haka.
HIKIMAR AURE
Aure alaka ce kebantacciya ta shari’a ko al’ada wacce ake kulla ta tsakanin mace da namiji, da lafazi na musamman, wacce take halatta wa kowanne daga bangarori biyu junansu ta fuskacin mu'amalar kebewa, haifar da 'ya'ya, da sauransu. Shari’ar musulunci ta nisantar da mutane daga zaman gwagwarci, ta kwadaitar da su yin aure domin samun al’umma ta gari mai kame kai, da renon manyan gobe wadanda zasu ci gaba da shiryar da na baya zuwa ga tafarkin tsira. Aure yana bayar da damar kusanci tsakanin namiji da mace; sai dai ba shi kadai ne yake bayar da halaccin kusancin ba , shari’a ta bayar da damar kusantar abin da namiji ya mallaka na bayi mata da ta kira su "mulku yamin”.
Aure ya kasu gida biyu ne a shari’ar musulunci, ya hada da Aure maras iyaka  da aka fi sani da "Da’imi” da kuma aure mai iyaka da aka fi sani da "Mutu’a”, duk wadannan biyun shari’a tana da hikima, kuma an sanya musu sharuda, sannan aka kwadaitar da yin su. Yawancin aure maras iyaka yakan kasance don hada gida da tara iyali, da renonsu, da samar da al’umma ta gari wacce zata gaji na baya.
Amma aure mai iyaka yakan kasance ne domin kariya daga zina, da fadawa cikin haramun; wannan yana da amfani matuka ga mutane mabambanta; muna iya kawo misalin matafiyi, da wanda ya kasa aure, ga shi kuma yana jin tsoron fadawa cikin zina, da maras ikon sama da mata hudu; ga shi kuwa yana iya fadawa fasadi, da sauran misalai masu yawa. Don haka ne Imam Ali (a.s) ya ce: "Ba don Umar ya haramta auren mutu’a ba, da babu mai yin zina sai fasiki” . Wannan lamarin kamar yadda yake ga maza, haka nan yake ga mata; sau da yawa macen da ba ta samun aure, sannan tana son kiyaye kanta daga zina da fada wa cikin sabon Allah madaukaki sakamakon ba zata iya kame kanta ba, ko kuma tana cikin yanayin rayuwa a al’ummar da ko dai ta fada wa fasadi, ko kuma ta zabi kiyaye dokar Allah. Sai dai wannan bayani ne kawai na wasu daga cikin hikimomin aure mai iyaka, amma ba su ne kawai dalilan sanya shi a shari’a ba, domin akwai bambanci tsakanin wadannan abubuwa biyu. Allah yana da hikimomin da yakan sanya shi zartar da hukunce-hukuncensa, muna iya fahimtar wasu sashe, wasu kuwa ba ma iyawa.

Ayoyin Kur'ani
Ayoyin masu yawa ne suka zo a cikin littafi mai girma na Kur'ani suna nuni zuwa ga dokokin zamantakewar aure da zamu kawo su a dunkule kamar haka:
1- Namiji shi ne shugaba a cikin iyali: Nisa’I: 34.
2- Mace nutsuwar mijinta ce: Rum: 21.
3- Miji da mata tufafin juna ne: Bakara: 187.
4- Kyautata zaman tare da mata: Nisa’I: 19.
5- Kiyaye adalci tsakanin mata: Nisa’I: 3.
6- Namiji da mace daidai suke a kamalarsu ta ‘yan adamtaka: Nahal: 97.
7- Kiyaye hakkokin mata: Nisa’I: 7.
8- Abin da namiji zai yi wa mace mai kin shimfidarsa; Na farko: Wa’azi. Sannan sai: kauracewa shimfidarta. Sannan sai: sanya karfi da duka da takurawa daidai yadda shari’a ta gindaya. Nisa’I: 34.
9- Kyautata wa mace yayin da ake ci gaba da zaman tare ko yayin da za a rabu: Bakara: 231.
10- Bayar da kyauta mai dacewa ga mace yayin da za a rabu: Ahzab: 49.
11- Bayar da kyauta ga mace daidai ikonsa idan za a rabu kuma ba a san juna ba a shimfida, kuma ba a aiyana sadaki ba: Bakara: 236.
12- Bayar da rabin sadaki ga mace yayin rabuwa kuma an aiyana sadaki amma har suka rabu din ba su san juna ba a shimfida: Bakara: 237.
13- Kada a takura wa mace domin ta halatta masa sadakinta: Nisa’I: 19.
14- Dokokin hakkokin mace bayan rabuwa, kamar wajan zamanta, da rashin kuntata mata, da ciyar da ita: Dalak: 6.
15- Rashin halaccin cin sadakin mace ga miji yayin rabuwa: Bakara: 229.
16- Sulhu tsakanin miji da mata: Nisa’i: 35 .
Asasin Hankali
Aure alaka ce mai karfi tsakanin jinsin namiji da mace, kuma tsari ne da rayuwar dan'adam ta ginu a kansa, babu bambanci tsakanin mutumin zamanin farko da na wannan zamanin, ko mutumin gabas da na yamma. Addinin Allah tun daga annabawan farko har na karshe sun ba wannan lamarin muhimmanci, sun shata wa kowane jinsi iyakokinsa bisa tsari mai kayatarwa da zai kai ga tausayi da jin kai da taimakekeniya tsakanin wannan jinsin guda biyu domin samun alakar halas da ci gaban samuwar dan'adam.
Tun farko idan za a farar da alaka tsakanin namiji da mace a matakin farko ana sanya hankali ne domin rayuwa ta yi karfi da inganci, amma bayan an shiga fagen rayuwar tare wato bayan aure, to a lokacin kuma ana son yin alakar soyaiya ne. Don haka wadanda suke fara rayuwarsu da soyaiya suka yi wurgi da hankali to ba zasu ji dadin rayuwarsu ba lokacin da suka shiga fagen rayuwar aure, don haka hankali ne matakin farko sai soyaiya ta biyo baya. Masu juya lamarin su fara da soyaiya sannan kuma daga baya su ce zasu sanya hankali a rayuwarsu zasu samu cewa lokaci ya kure masu ba zasu iya ba.
Wannan ne ake nufi da cewar masu fara rayuwa bisa dogaro da hankali to zasu iya ci gaba da rayuwa bisa soyaiya, amma wadanda suke fara rayuwa bisa soyaiya to ba zasu iya ci gaba da rayuwa bisa hankali ba. Idan rayuwar ma'aurata ta fara da tsari da hankali da tunani mai kyau to zata kai su ga cin nasara da samun nutsuwar rayuwa, al'ummar da ta doru kan wannan tunanin zata samu rayuwar iyalinta cikin annashuwa da nutsuwar rai da jin dadin rayuwar tare.
Kuma tun da tsarin nan yana bukatar wanda ba shi da wata maslaha a cikinsa kuma ya san halittar mutum da bukatunsa, don haka da bukatar koma wa mahaliccin mutum don sanin takamaimai me ya dace da shi da rayuwarsa a daidakunsa ko a al'ummance. Wannan lamarin ne ya sanya muke jin kiraye-kiraye a kasashen yammacin duniya kan a koma wa addinan Allah cikin abin da ya shafi tsarin rayuwar iyali don samun nutsuwa da daidaito a ciki.
Idan muka duba Musulunci zamu ga yadda ya ba wa gina iyali da rayuwar aure muhimmancin gaske don karfafa matakin farko na gina al'umma, sai ya sanya wasu ladabobi, da ka'idoji, da sharadodi masu kiyaye wa kowane bangare yanayin halittarsa ta yadda babu wani bangare da ya dora wa wani abu da ba zai iya yin sa ba, tare da kiyaye alakar kauna da so da tausaya wa juna, da kuma karfafa alakarsu ta yadda zasu kasance tamkar jiki da rai, da kare su daga tozarta da bin son rai mai lalata rayuwarsu.
Sai ya kalli rayuwarsu tun kafin su yi aure, da lokacin yin aure kafin haihuwa, da bayan haihuwa, da bayan aure ma, ya sanya wa kowace marhala dokar da ta dace da ita, ya kawo dokokin alaka tsakanin daidaikun mutane da suke cikin iyali daya. Mu a nan zamu so kawo muku bayanai ne masu muhimmanci kan wadannan lamuran da suka hada zabar abokin/abokiyar rayuwa, yadda ake gina rayuwar iyali, hakkokin iyali, sabani tsakanin iyali da hanyar magance shi, alakar da take tsakanin iyali da mutanen da suke kusa da su, alakar da take tsakanin jinsin namiji da mace, da wani abu da ya shafi hukuncin muharramai (wadanda aka haramta aurensu).

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: