bayyinaat

Published time: 11 ,November ,2018      23:12:46
Aure shi ne hanyar samar da alaka da sabawa da soyaiya da shakuwa da juna, da taimakon al'umma kan kamewa daga fasadi
Lambar Labari: 271
Iyali a nan muna nufin mutanen gida daya masu damfaruwa da juna da kusancin jini, nasaba, aurataiya, wato su ne wadanda suke da alakar gina zuriya da take kunsar miji, mata, da 'ya'yansu, wani lokaci tana hada uwa, uba, kaka, jika, 'yan'uwa, surukai, da sauran makusanta a gida daya . Yin aure wani abu ne da yake mustahabbi a shari'a kuma yana da muhimmanci mai girma domin shi ne hanyar hayaiyafar iyali da kiyaye cigaban samuwar dan'adam, don haka ne sai mustahabbancinsa ya zama mai karfi sosai.
Aure shi ne hanyar samar da alaka da sabawa da soyaiya da shakuwa da juna, da taimakon al'umma kan kamewa daga fasadi, da kawar mata matsalar tunani da rashin nutsuwar rai, da kawar mata da bala'in fasadi, don haka ne sai aure ya kasance wani mustahbbai mai karfi kuma sunnar annabin rahama (s.a.w) da ya kwadaitar. Hatta da bayi da wancan lokacin akwaisu Musulunci ya yi musu hukunci daya kan wannan lamarin a matsayinsu na mutane yayin da yake cewa: "Ku aurar da bayi daga cikinku da salihai daga bayinku maza da mata, idan sun kasance matalauta to da sannu Allah zai wadatar da su daga falalarsa, kuma Allah mai yalwatarwa masani ne" .
Ruwayoyi masu yawa ne suka zo suna kwadaitar da yin aure, kuma shi ne babbar kariya daga duk wani rashin nutsuwar rai da hankali, da kare mutum daga fadawa munanan halaye da sabo. Sai ya sanya mutum ya zama mai iyakantuwa da hankali da watsar da son rai da sha'awa da suke yi masa dabaibayi suke shagaltar da shi da dauke masa hankai daga matsayinsa na rayuwa. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Wanda ya so sunnata, to aure yana daga sunnata" . Da fadinsa: "Me yake hana mutum yin iyali ne, ta yiwu Allah ya arzuta shi da 'ya'ya da zasu cika duniya da fadin La'ilaha illal-Lah" . Da fadinsa: "Wanda ya yi aure ya kare rabin addininsa, to sai ya ji tsoron Allah a cikin sauran rabi" . Da fadinsa: "Raka'a biyu da mai aure yake yi, ta fi raka'a saba'in da maras aure yake yi" .
Muhimmancin da aure yake da shi ne ya sanya shi matakin daraja ta biyu bayan Musulunci; babu wani abu da ya fi zama ni'ima bayan Musulunci irin matar da idan mijinta ya kalle ta sai ta faranta masa rai, idan ya umarce ta sai ta bi shi, idan ba ya nan sai ta kare masa kanta da dukiyarsa. Munin gwagwarci ne ya sanya Musulunci ya karhanta shi domin yana kai wa zuwa ga halaye munana da sanya mutum mai matsalolin fushi da kuncin rayuwa, da jefar da bukatun asasi na sha'awa, ko dai ta hanyar yakar su, ko kuma ta hanyar jefa rai cikin aiyukan fasadi masu hadari.
Wasu mutane suna kin yin aure saboda tsoron talauci, sai dai tsoron talauci ya saba da talauci, idan mutum ya ki yin aure saboda yana da talauci wannan yana da uzuri kuma shari'a ta ba shi shawarar yin azumi. Wasu kuwa suna iya auren amma suna tsoron ka da su yi aure abin da suke rayuwa da shi ya yi musu karanci, tare da cewa suna da sana'a da ta dace da halin yanayinsu da matsayinsu gwargwadon yadda ya dace da rayuwarsu, to irin wadannan mutanen ne shari'a ta soke su. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: " Duk wanda ya bar yin aure don tsoron talauci to hakika ya munana wa Allah zato" .
Bincike ya tabbatar da cewa mafi munin mutane karkacewa daga hanya ta gari su ne wadanda suke gwagware, domin mai aure yana da abin da ya yi masa iyakar da yakan samu karancin tunanin saba wa sha'awarsa musamman don kare mutuncin matarsa, iyalinsa, 'ya'yansa da danginsa, sai wannan lamarin ya sanya shi ya fi kusa da nisantar alfahasha, hada da cewa yana da inda yake iyakance shi duk lokacin da sha'awa ta dame shi.
Munin gwagwarci ne ya sanya Musulunci ya yi wasiiya ga wadanda ba zasu iya yin aure ba da su karfafi yin azumi . Yin azumi wata garkuwa ce da take iya kashe fushin sha'awar da take addabar su. Da azumi ne saurayi zai iya rage karfin sha'awar da take addabarsa ya rage mata tasirin bacin rai, da damuwar rai da bakin cikinta da yake iya bujuro masa sakamakon rashin aure ba tare da ya yaki sha'awarsa ko ya fada cikin fasadi da lalacewar halaye ba. Hada da cewa mazhabar da ta yarda da auren mutu'a ta sanya shi daya daga cikin hanyoyin da zasu kawar da fasadi cikin al'umma. Yayin da wasu mazhabobin suka karhanta ko suka haramta saboda ittifakin da aka samu cewa sarkin musulmi Umar dan Khaddabi ya haramta shi.
Bayan mustahabbantar da aure sai Musulunci ya zarce wannan marhalar ya kwadaitar da mutane masu yalwa da wadata ko gwamnati da su taimaka wurin aurar da gwagware, zaurawa, 'yan mata, da samari. Wanda ma kuma ba shi da wannan ikon yin haka to ya taimaka wurin hada aure idan ya samu dama. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Wanda ya yi kokari wurin hada aure tsakanin muminai biyu har ya hada tsakaninsu to Allah zai aura masa hurul'in dubu daya" . Kuma yana cewa: "Mutane Uku zasu shiga inuwar al'arshi ranar kiyama ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa: Mutumin da ya aurar da dan'uwansa musulmi, ko ya yi masa hidima, ko ya boye masa sirrinsa" .
Addu'ar Aure
Duk sa’adda ake son zama tsakanin namiji da mace to dole ne su san cewa akwai yarjejeniyar zo mu zauna tare don mu tsara tare mu tsira tare. Kafin aure dole ne su san juna sani mai zurfi ta yadda kowa zai gaya wa kowa halayensa kyawawa da munana don su samu damar sanin yadda zasu tsara rayuwarsu. Karya a cikin rayuwa ce ta yi mana yawa, don haka ne tun farko ba ma gaya wa juna gaskiya balle har mu san yaya zamu zauna cikin soyaiya da jin dadi bayan aure.
Sannan kuma bayan sun tsara zamansu kan yadda ya dace sai kuma su bai wa Allah sauran lamura hannunsa, a nan ne Musulunci ya karfafi yin addu'a domin samun dacewa wurin Allah madaukaki. Yin addu'a yana daga mafi muhimmancin abin da ya kamata mai neman aure ya himmantu da shi, sai ya roki Allah ya sa su dace wurin zabar abokin zama, domin zabar abokin rayuwa yana nufin mu shata wa kanmu rayuwar da zamu zaba har mutuwarmu ko kuma mai tasiri a kanmu har karshen rayuwarmu, kuma zamu fahimci cewa wannan lamari ba karami ba ne domin yana da tasiri a rayuwarmu.
Daga cikin addu'o'in da suka zo akwai yin salla raka'a biyu, da gode wa Allah, sannan sai a ce: Ubangiji ni ina son yin aure, Ubangiji ka kaddara mini wacce ta fi kame kai daga cikin mata, ta fi kiyaye mini kanta da dukiyata, wacce ta fi su yalwar arziki, ta fi su girman albarka, kuma ka kaddara mini da mai tsarki daga gare ta wanda zaka sanya shi na gari a rayuwata da bayan mutuwata.
اللهم إني أريد أن أتزوج، اللهم فاقدر لي من النساء أعفهن فرجا، وأحفظهن لي في نفسها وفي مالي، و أوسعهن رزقا، وأعظمهن بركة، وأقدر لي منها ولدا طيبا تجعله خلفا صالحا في حياتي و بعد موتي.
Sannan a ko'ina ana son kiyaye sharuddan addu'a da ladubanta, mai son sanin hakan da fadadawa yana iya koma wa littafinmu na addu'o'i don sanin hakan.

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: