bayyinaat

Published time: 11 ,November ,2018      23:14:49
Wannan ya yi daidai da ace wani abu ne na haya tun da kamar yadda ya zo a can baya mace a shari’a, na kama da abin da aka haya.
Lambar Labari: 272
3. Tsayin Lokacin Auren (Mudda)
Tsawan lokacin auran mutu'a dole a tsara shi ta yadda ba za a nemi qara tsawan shi ko rage shi ba. A faxar imami al-Ridah… 'dole mutu'a ta zama qaiyyadajjiya mai qaiyyadajjen lokaci, (Ibid, 479, Hadiss 1) haka nan wata rana' an tambayi Imam ko za a iya qulla auren mutu'a na sa’a xaya ko biyu? sai ya ce: Ba wani lokaci da za a iya tantancewa a sa’a xaya ko biyu.(Ibid, Hadis).
A fatawar Shehul Ansari, duk hadisai sun nuna cewa an yarda tsawan lokaci da aka amince ya fara daga daidai lokacin da aka xaura auren, ko kuma ya fara daga wani lokaci mai zuwa ko a xaga auren zuwa sa’ar da aka shirya. (Ibid, 446 Hadiss 2. da kuma Hadis 4).
Wannan ya yi daidai da ace wani abu ne na haya tun da kamar yadda ya zo a can baya mace a shari’a, na kama da abin da aka haya.  
Dangane da auren mutu'a wanda aka sawa lokacin farawa, akwai tambaya a kan cewa shin mace na iya auren wani mijin kafin lokacin farawar auren ta na farko ya yi? (Kamar idan an kulla auren a watan Muharram amma auren zai fara aiki a watan Jimadal ula, to shin za ta iya aurar wani a wannan tsakanin na watanni 4) A nan akwai Magana guda 2 biyu: ta xaya ita ce; ba a yarda ba, (ba zata iya yi ba ko ka ce bai halatta ba) domin matar ta riga ta zama mai aure; ko kuma ana iya yarda (zata iya yi) saboda kasantuwar tabbatuwar dukkannin abubuwan da ake buqata na auren da kuma rashin abin da zai hana. Abin nufi dai a doka shi ne zata iya yin auren na biyun kuwa; wannan na iya zama halattaccen aure, mutuqar kafin kwanakin auren farkon su fara akwai iashsshen lokacin da zata iya yin idda.
Dangane da xaga lokacin fara muta'a ya danganta da rana da kuma watan da za a fara. misali, idan mutum ya qulla auren na wata xaya amma bai fayya ce yaushe ne watan zai fara ba, to babu auren (auren ya vaci) domin rashin fayyace lokacin. A auren mutu'a duk wani abu mai kama da irin wannan, (wanda zai sa lokaci ya zama ba fayyatacce ko tantattacce ba), rashin qayyade lokaci na sa auren ya zama vatacce. (Matajir 11, 300) Amma idan ba a sa sharaxin wani lokaci na nan gaba (na jinkirta shi) a wajen qulla auren ba, to auren zai fara da zarar an gama kulla shi domin a qa’ida idan an gama qullawa to ciniki ya faxa. (Ibid Jawahir 5, 171).
A fatawar mafi shahara ya zo cewa, idan ba a tantance lokaci a furicin xaura Auren ba to babu wannan auren, kuma bai qullu ba (Matajir 11, 299, Sharhul Lum'a 5, 287 Jawahir 5). Al'umma ta haxu a kan cewa xaya daga cikin ginshiqai biyu da suka bambanta mutu'a da auren da’imi shi ne ambatan lokaci, duk yayin da wannan ginshiqi ya zama babu, duk wani abu da aka qulla a auren ya vaci. Bugu da qari, qulla shi yana bibiyar niyar masu yinsa ne wato idan ba a ambaci qarshe ba, auren ba zai zama ya cenja zuwa da’imi ba, tun da ba shi aka yi niyar qullawa ba. a kan haka an rawaito hadisi daga imam Ja’afar: (a.s) 'babu mutu'a idan babu abu biyu: qaiyyadajjen lokaci da ambataccen sadaki' (Wasa'il, x4 Hadiss 1).
Duk da wannan ra’ayi, mafi yawan malamai sun tafi a kan idan ba a ambaci lokaci ba, auren baya vaci, sai dai auren ya koma da’imi. su waxannan malaman sun ce idan aka xaura aure, ko dai ya zama na wucin gadi ko kuma na da’imi, idan an ambaci lokaci a auren ya zama na mutu'a, idan ba a ambata ba to ya zama da’imi, domin su kare wannan mahangar da fahimtar ta su sun kawo hadisin Imam Ja'afar: (a.s) 'idan an ambaci lokaci auren ya zamana mutu'a idan ba a ambata ba ya zama da'imi (Ibid, 469, Hadiss 1).



Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: