bayyinaat

Published time: 11 ,November ,2018      23:24:39
Shin baka ga wanda ke qaryata ranar sakamako ba. فَذَلِكَ الَّذِي يَدُعُّ الْيَتِيمَ (2) Wannan shine wanda ke tunkuxe maraya (daga haqqin sa).
Lambar Labari: 274
سورة الماعون
SURATUL MA'UUN (SURA TA 107)
Wannan sura da mu ka sani da suratul ma'uun ko da hausa mu ce surar taimako/agazawa, wannan sura ta sauka tana mai gargaxi ga masu rowa da hana dukiyar su ko wani abu da Allah ya azurta su, domin rowa na kashe rayuwar jama'a, koda addini ne yayin da masu wadatar cikin sa su ka yi masa rowa zaka same shi baya ci gaba, da fatan Allah ya tsare mu da wannan mummunar xabi'a.
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ (1)
Da sunan Allah mai rahama (mai faxin da take ko ina) mai jin qai(rahama ce kevantacciya wadda bata haxe komai ba kamar yadda rahmaniyya ba).
أَرَأَيْتَ الَّذِي يُكَذِّبُ بِالدِّينِ (1)
Shin baka ga wanda ke qaryata ranar sakamako ba.
فَذَلِكَ الَّذِي يَدُعُّ الْيَتِيمَ (2)
Wannan shine wanda ke tunkuxe maraya (daga haqqin sa).
وَلَا يَحُضُّ عَلَى طَعَامِ الْمِسْكِينِ (3)
Baya kwaxaitarwa kan ciyar da miskini.
فَوَيْلٌ لِلْمُصَلِّينَ (4)
Narko/azaba ta tabbata ga masallata.
الَّذِينَ هُمْ عَنْ صَلَاتِهِمْ سَاهُونَ (5)
Waxanda ke shagalta su bar sallar su.
الَّذِينَ هُمْ يُرَاءُونَ (6)
Waxanda ke riya (wajen aiwatar da ayyukan alheri).
وَيَمْنَعُونَ الْمَاعُونَ (7)
Kuma su ke hana taimako (ga mabuqata).

Domin faɗaɗa bayani a bincika tafsirin Qur'anin Al-mizan na Allama Ɗaba-Ɗaba'i.

Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: