bayyinaat

Published time: 11 ,November ,2018      23:33:56
A farkon al’amari na san garin Dir’iyya gari ne mai tsananin talauci amma bayan wani lokaci sai ya koma daya daga cikin garuruwa masu arziki, ta yadda ya kasance har makamansu ana yi musu kawa ta musamman.
Lambar Labari: 277
Taimakonsa Ga Ali Sa'ud
Muhammad Bn Abdulwahab ya fara da’awarsa domin karfafa hukumar Bn Sa’ud kamar yadda suka yi alkawari. Sakamakon haka ne ba da jimawa ba a ka fara kai hare-hare zuwa garuwan kabilolin da suke kusa ana kashe su ana kuma kwashe musu dukiya. Wadannan dukiyoyi kuwa ba wasu ba ne sai dukiyoyin garuruwan Musulmin Najad wanda an kai musu wannan hari ne sakamakon tuhumarsu da ake yi a kan yin shirka da bautar gumaka, sakamakon haka ne dukiyarsu da rayukansu suka zama halas ga Muhammad Bn Sa’ud wanda yake shi ne hakimin Dir’iyya kamar yadda muka fada a baya, kamar yadda aka sani Alusi yana karkata ne zuwa ga akidar wahabiyanci amma a cikin littafinsa yana hikaitowa daga wani malamin tarihi mai suna Ibn bushr cewa:
A farkon al’amari na san garin Dir’iyya gari ne mai tsananin talauci amma bayan wani lokaci sai ya koma daya daga cikin garuruwa masu arziki, ta yadda ya kasance har makamansu ana yi musu kawa ta musamman. Sannan sun kasance suna hawan dawakai na asali, sannan duk wani abin jin dadi sun kasance suna da shi a wannan lokaci ta yadda harshe ba zai iya siffanta wannan jin dadi ba.
Ya ci gaba da cewa wata rana ina cikin kasuwar Dir’iyya ina kallo yayin da mata da maza kowane yana bangarensa. Sannan a cikin wannan kasuwa akwai zinari da azurfa da sauran kayan ado, sannan ga kayan abinci kamar alkama nama da dai sauran kayan abinci ta yadda mutum ba zai iya fadarsu ba. Na kasance ina jin hayaniyar masu saye da sayarwa a wannan kasuwa kamar yadda kudan zuma ke wucewa, ta yadda wancan yana cewa na sayar wancan yana cewa na siya (Tarihk iBn Bushr Najdi 1:shafi na 23).
Abubuwa guda biyu ne suka taimaka wajen yaduwar da’awar Bn Abdulwahab musamman a kauyuka.
1-Karfin ikon hukumar Ali Sa’ud.
2-Nisantar mutanen Najad daga cigaban Musulunci da hakikanin musulunci.

Hare-Haren Wahabiyawa A Kan Garuruwan Musulmi
Yakokin da wahabiyawa suka yi a a garuruwan Najad da wajensu sun kasance masu janyo hankali kamar yadda idan aka kai hari a wani gari to duk dukiyar da aka samu a wannan gari ta mayakan ce, wato idan har suna iyawa zasu iya mayar da har gidaje da gonaki wadanda suna iya mayar da su mallakinsu, idan kuwa haka ba ta yiwu ba, to sai su hakura da abin da suka samu na ganima daga dukiyoyi (Jaziratul arab fi karnil Ishirin shafi na 341.).
Kowace sabuwar akida idan ta bayyana musaman idan tana kira ne zuwa ga tauhidi to farko tabbas zata ja mutane, musamman a inda mutanen wurin ba su da cikkiyar masaniya a kan addini. Lokacin da Muhammad Bn Abdulwahab ya fara kiransa a kan tauhidi da yaki da shirka, wasu daga cikin manyan Najad da Yaman sun karbi wannan kira nasa. A matsayin misali a lokacin da guguwar kiransa ta isa Yaman sai Sarki Muhammad Bn Isma’il mawallafin littafin nan mai Subulu Salam fi sharhi bulugul muram ya yi wata kasida a kan yabon Muhammad Bn Abdulwahab in da yake cewa:
Aminci ya tabbata ga Najad da wanda ya sauka a Najad
Duk da cewa sallamata daga nesa ba zata amfanar ba.
Amma lokacin da shi wannan mutum ya samu labarin hare-hare da kisa da kwace dukiyar da wahabiyawa suke yi a garuruwan musulmi sai ya fahimci cewa Bn Abdulwahab yana kafirta muslmi ne, sannan ba ya ganin darajar jini da dukiyoyinsu, sai ya yi nadama a kan wakar da ya yi ma shi a baya, sai ya yi wata sabuwar kasida wacce take cewa:
Na warware maganar da na yi kan Najad
Domin kuwa ya iganta a gare ni sabanin abin da nake tunani a kansa.
Kisan da wahabiywa suka yi wa al’ummar musulmi a wajen ziyarar Imamai (a.s) wani bakin shafi ne a tarihin musulunci. Wani daga cikin marubutan wahabiyawa mai suna Salahuddin Mukhtar yana rubutawa kamar haka:
A shekara ta 1216 sarki Sa’ud ya tanadi wata runduna wacce ta kunshi mutanen Najad da sauran kabilolin kudanci da na Hijaz da dai sauran al’ummu daban ya nufi Iraki da niyyar kai hari. Ya isa Karbala a watan zulkida yayin da ya kewaye garin Karbala. A lokacin ne sojojinsa suka rusa garun Karbala da karfi suka shiga cikin garin suka kashe mafi yawan mutanen da suke waje da cikin gida da kasuwa. Sannan gab da azahar suka fita daga garin Karbala tare da ganimar da suka kwasa, sannan suka sauka a wani wuri mai ruwa inda ake kira Abyadh. Sai shi Sa’ud da kansa ya dauki kashi daya daga cikin biyar din dukiyar da suka kwaso saura kuwa mayaka suka kassafa a tsakaninsu. Wato duk sojan kasa zai dauki kashi daya sojan saman doki kuwa zai dauki kashi biyu, da haka ne kowa ya dauki rabonsa (Tarikhul mamlakatul arabiyatus sa’udiyya 3:shafi na 73).  
Ibn Bushr wanda yake masanin tarihi ne kuma mutumin Najad dangane da harin da wahabiyawa suka kaiwa Najaf yana rubuta cewa:
A shekara ta 1220BH Sa’ud ya jagoranci runduna mai yawa ya nufi garin nan mai tsarki shaharare na Iraki (wato Najaf) yayin da ya isa wannan gari sai ya zuba sojojinsa a wajen garin. Sannan ya bayar da umurnin kai hari da ruguza wannan gari, amma lokacin da suka isa bakin garin sai suka tarar da katon rami a gefen garin ta yadda ba zasu iya shiga ba. Sakamakon haka ne suka ci gaba da yaki ta hanyar musayar kibau, da haka ne a ka kashe da yawa daga cikin sojojin Sa’ud a wannan lokaci, sannan saura kuwa suka koma da baya, sai suka ci gaba da wawashe dukiyoyin kauyukan da suke gefen garin (Unawanul majd fi tarikhi Najd 1 shafi na 337).
Mai yiwuwa a yi tunanin cewa Wahabiyawa sun kasance suna kai hari zuwa garuruwan da ‘yan Shi’a suke zaune ne, amma abin ba haka yake ba, domin kuwa sun kasance suna kai hari ga dukkan garuruwan da musulmi suke zaune abin da ya hada da garuruwan Iraki Sham Hijaz kamar yadda tarihi ya ruwaito da yawa a kan wannan mugun aiki na wahabiyawa, ta yadda a nan ba zamu iya fadar duk abin da ya faru ba, sai dai kawai zamu yi nuni da wasu daga ciki a matsayin misali:
Jamil sadiki Zahawi yana rubutawa musamman dangane da harin da wahabiyawa suka kai wa garin Da’if yana cewa: Daya daga cikin mafi munin ayyukan wahabiyawa shi ne kisan gillar da suka yi wa al'ummar musulmin Da’if ta yadda ba su tausaya wa kowa ba, babba da yaro, mace da namiji, ta yadda har da yaro mai shan nono sukan kwace shi daga mamansa su yanka shi. Wasu mutanen da yawa sun kasance suna cikin koyon karatun Kur’ani duk suka kashe su. A lokacin da ya kasance babu kowa a cikin gida sai suka nufi shaguna da masallatai duk wanda suka samu har suka tarar da wasu suna cikin ruku’u da sujjada duk suka kashe su. Littattafan da suka kasance a hannun mutane wadanda suka hada da Kur’ani mai tsarki da sauran Littattafan hadisi kamar su Sahih bukhari da Muslim da sauran Littattafan hadisi da na Fikh duk suka yi daidai da su. Wannan kuwa ya faru ne a shekara ta 1217Bh (Alfajrus Sadik shafi na 22).  
Bayan kisan gillar da wahabiyawsa suka yi wa mutanen Da’if, sai suka rubuta takarda zuwa ga malaman Makka suna kiran su zuwa ga wannan Mazhaba tasu. Sannan suka yi hakuri har lokacin ayyukan hajji su wuce, ta yadda mahajjata zasu fita daga garin Makka ta yadda zasu kai wa garin Makka hari.
Kamar yadda Sha Fadhl Rasul Kadiri Hindi yake rubuta cewa: Ya ga malaman Makka sun kasance duk sun taru a gefen Ka’aba ta yadda zasu amsa takardar da Wahabiyawa suka aiko musu, suna cikin tattaunawa sai wasu daga cikin mutanen Da’if wadanda aka zalunta suka shigo cikin Harami, sannan suka yi musu bayanin abin da ya auku a garesu. Kuma ya yadu a cikin mutane cewa ai wahabiyawa sun riga sun shigo cikin garin Makka kuma zasu yi wa mutane kisan gilla. Mutanen Makka suka shiga cikin tsoro da tararrabi, kai ka ce kiyama ce ta tsaya, malaman da suke gefen mimbari a cikin masallacin ka’aba duk suka taru waje guda. Sai Abu Ahmid Khadib ya ta shi ya hau mimbari ya karanta takardar da Wahabiyawa suka aiko da amsar da malaman Makka suka rubuta musu a kan raddin akidojinsu. Sannan ya juya ga malamai da alkalai da duk masu bayar da fatawa ya ce: Kun ji abin da mutanen Najad suka ce kuma kun ji dangane da akidunsu. Saboda haka me zaku ce dangane da akidunsu? A wannan lokacin dukkan malaman Makka da ko’ina daga mazhabobin Sunna guda hudu da suka halarci garin Makka domin gabatar da ayyukan hajji suka bayar da fatawa a kan kafirtar Wahabiyawa, Sannan suka yi kira ga Sarkin Makka a kan wajibci a kan ya yi gaggawa ya tashi domin fito na fito da Wahabiyawa. Sannan suka kara da cewa ya wajabta a kan musulmi su taimaka masa a kan wannan al’amari su halarci wannan jihadi na yaki da Wahabiyawa. Sannan duk wanda bai bi wannan umurnin ba kuma ba tare da wata matsala ba to ya yi babban zunubi, sannan duk wanda ya halarci wannan kira yana matsayin mujahidi a tafarkin Allah, sannan idan aka kashe shi yana matsayin shahidi. Dukkansu suka amince da wannan takarda sannan suka sanya hannu a kan wannan fatawa da aka ambata (Saiful Jabbarul Maslul alal a’ada’iSha fadhl Kadiri bugun Istanbul shekara ta 1395 daga shafi na 2).  
Daga nan ne zamu fahimci cewa dukkan bangare guda biyu na musulmi wato sunni da Shi’a ba su amince da wannan akida ta wahabiyawa ba, duk sun tafi a kan rashin ingancinta.
Raddi na farko da aka yi wa wannan mazhaba ta wahabiyanci kuwa ya kasance daga dan’uwan shi kansa Muhammad Bn Abdulwahab wato Sulaiman Bn Abdulwahab, yayin da ya rubuta littafi a kan haka mai suna Assawa’ikul Ilahiyya (wato tsawar Ubangiji) a cikin wannan littafi ga abin da yake rubutawa:
Abubuwan da Wahabiyawa suke cewa shirka ne wanda sakamakonsa ne suke halatta rayuka da dukiyoyin musulmi dukkansu sun kasance ana yin su a zamanin Imamai na musulunci (Shugabannin mazahabobi) amma ba a taba jin wata magana ba daga su wadannan shugabanni, suna cewa masu yin wadannan ayyuka kafirai ne ko kuma sun yi ridda daga addini, ko ba da fatawa a kan a yaki wadanda suke aikata wadannan ayyuka, ko su ambaci garuruwan musulmi da sunan garururwan kafirci kamar yadda wahabiyawa suke yi (Al’islam fikatnil Ishrin shafi na 126-137).

Malaman Da Suka Fara Yin Raddi A Kan Akidun Wahabiyanci
Bayan shi Sulaiman Bn Abdulwahab malamai da dama sun ta shi a kan kalu balantar wannan akidu na wahabiyanci. Wasu kuwa daga cikin wadannan malamai na Ahlussuna su ne kamar haka:
1-Abdullahi Bn latif shafi’i marubucin (Assawa'ik warrudud)
2-Muhammad Bn Abdurrahaman Bn Afalik Hanbali (Tahakkumul mukalidin)
3-Afifuddin Abdullahi Bn Da’ud Hanbali (Assawai’ku war rudud)
4-Ahmad Bn Ali kabani Basri ya yi (risala a kan raddin iyalan Abdulwahab).
5-Shaikh Ada’illahi Makki marubucin (Al’arimul Hindi fi unkil Najdi)
Wadannan wasu daga cikin malamn Ahlus-suna kenan wadanda suka rubuta kalubale a kan akidar wahabiyawa, wanda yake so ya ga sunan wasu daga cikin wadannan malamai sai ya koma littafinmu na Milal wannanhl (juzu’i na 4 shafuka na 355-3 59 domi Karin bayani.
Amma daga cikin malaman Shi’a da suka yi raddi a kan wahabiyawa na farko babban malamin nan ne wato Shaikh Ja’afar Kashiful Gida wanda ya rubuta littafi mai suna (Manhajir rashad liman aradas sadad) wanda a cikinsa ne ya bayyanar da hakikanin al’amurra sannan ya aika wa sarkin Makka Bn Abdul Aziz wanda yake mai tsattsauran ra’ayi ne a kan wahabiyanci.
Sannan daga cikin iyalansa masu girma marigayi sheikh ayatulla Muhammad Husain Asli Kashiful Gida ya rubuta littafi mai suna (Ayatul bayyinat) a lokacin da wahabiyanci suka rushe makabartar Ahlul Baiti (a.s) a Madina ta yadda ya yi raddin akidojinsu tare da amfani da Kur’ani da Sunna.
Littafi mafi girma da aka rubuta dangane da raddin akidun wahabiyawa shi ne (kashiful irtiyab an atba’i Muhammad Bn Abdulwahab) wanda Ayatullahi Muhsin Amuli ya rubuta, yana da muhimanci ga wanda yake so ya samu masaniya sosai a kan wahabiyanci ya duba wannan littafi (Wanda yake so ya kara samun bayani sai ya duba littafinmu na milal wannahl juzu’I na 4 shafi na 359-360).  
 
Ibrahim Muhammad Sa'id
+989368244976, +2348068985568
Ibraheemsaeedkano@gmail.com,


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: