bayyinaat

Published time: 11 ,November ,2018      23:56:41
ban yanke buri na ba sabida tsananin kyan girman ka, ya Allah idan zunubai na sun nesanta ni daga gareka, ka yafe min da sabida kyautata dogaro na da kai,
Lambar Labari: 278
الثاني : يقرأ هذه المناجاة التي رواها ابن خالويه وقال إنها مناجاة أمير المؤمنين والأئمة من ولده عليهم السلام كانوا يدعون بها في شهر شعبان، وهذه المناجاة جليلة القدر مشتملة على مضامين عالية ويحسن أن يدعى بها عند حضور قلب وهو :
اَللّـهُمَّ صَلِّ عَلى مُحَمَّد وَآلِ مُحَمَّد، وَاسْمَعْ دُعائي اِذا دَعَوْتُكَ، وَاْسمَعْ نِدائي اِذا نادَيْتُكَ، وَاَقْبِلْ عَليَّ اِذا ناجَيْتُكَ، فَقَدْ هَرَبْتُ اِلَيْكَ، وَوَقَفْتُ بَيْنَ يَدَيكَ مُسْتَكيناً لَكَ، مُتَضرِّعاً اِلَيْكَ، راجِياً لِما لَدَيْكَ ثَوابي، وَتَعْلَمُ ما في نَفْسي، وَتَخْبُرُ حاجَتي، وَتَعْرِفُ ضَميري، وَلا يَخْفى عَلَيْكَ اَمْرُ مُنْقَلَبي وَمَثْوايَ، وَما اُريدُ اَنْ اُبْدِيَ بِهِ مِنْ مَنْطِقي، واَتَفَوَّهُ بِهِ مِنْ طَلِبَتي، وَاَرْجُوهُ لِعاقِبَتي، وَقَدْ جَرَتْ مَقاديرُكَ عَليَّ يا سَيِّدي فيما يَكُونُ مِنّي اِلى آخِرِ عُمْري مِنْ سَريرَتي وَعَلانِيَتي، وَبِيَدِكَ لا بِيَدِ غَيْرِكَ زِيادَتي وَنَقْصي وَنَفْعي وَضرّي، اِلـهي اِنْ حَرَمْتَني فَمَنْ ذَا الَّذي يَرْزُقُني، وَاِنْ خَذَلْتَني فَمَنْ ذَا الَّذي يَنْصُرُني، اِلـهي اَعُوذُ بِكَ مِنَ غَضَبِكَ وَحُلُولِ سَخَطِكَ، اِلـهي اِنْ كُنْتُ غَيْرَ مُسْتاْهِل لِرَحْمَتِكَ فَاَنْتَ اَهْلٌ اَنْ تَجُودَ عَليَّ بِفَضْلِ سَعَتِكَ، اِلـهي كَأَنّي بِنَفْسي واقِفَةٌ بَيْنَ يَدَيْكَ وَقَدْ اَظَلَّها حُسْنُ تَوَكُّلي عَلَيْكَ، فَقُلْتَ ما اَنْتَ اَهْلُهُ وَتَغَمَّدْتَني بِعَفْوِكَ، اِلـهي اِنْ عَفَوْتَ فَمَنْ اَوْلى مِنْكَ بِذلِكَ، وَاِنْ كانَ قَدْ دَنا اَجَلي وَلَمْ يُدْنِني مِنْكَ عَمَلي فَقَدْ جَعَلْتُ الاِقْرارَ بِالذَّنْبِ اِلَيْكَ وَسيلَتي، اِلـهي قَدْ جُرْتُ عَلى نَفْسي في النَّظَرِ لَها، فَلَها الْوَيْلُ اِنْ لَمْ تَغْفِرْ لَها، اِلـهي لَمْ يَزَلْ بِرُّكَ عَلَيَّ اَيّامَ حَياتي فَلا تَقْطَعْ بِرَّكَ عَنّي في مَماتي، اِلـهي كَيْفَ آيَسُ مِنْ حُسْنِ نَظَرِكَ لي بَعْدَ مَماتي، وَاَنْتَ لَمْ تُوَلِّني إلاّ الْجَميلَ في حَياتي، اِلـهي تَوَلَّ مِنْ اَمْري ما اَنْتَ اَهْلُهُ، وَعُدْ عَلَيَّ بِفَضْلِكَ عَلى مُذْنِب قَدْ غَمَرَهُ جَهْلُهُ، اِلـهي قَدْ سَتَرْتَ عَلَيَّ ذُنُوباً في الدُّنْيا وَاَنَا اَحْوَجُ اِلى سَتْرِها عَلَيَّ مِنْكَ في الاُْخْرى، اِذْ لَمْ تُظْهِرْها لاَِحَد مِنْ عِبادِكَ الصّالِحينَ، فَلاتَفْضَحْني يَوْمَ الْقِيامَةِ عَلى رُؤُوسِ الاَْشْهادِ، اِلـهي جُودُكَ بَسَطَ اَمَلي، وَعفْوُكَ اَفْضَلُ مِنْ عَمَلي، اِلـهي فَسُرَّني بِلِقائِكَ يَوْمَ تَقْضي فيهِ بَيْنَ عِبادِكَ، اِلـهىِ اعْتِذاري اِلَيْكَ اعْتِذارُ مَنْ لَمْ يَسْتَغْنِ عَنْ قَبُولِ عُذْرِهِ، فَاقْبَلْ عُذْري يا اَكْرَمَ مَنِ اعْتَذَرَ اِلَيْهِ الْمُسيئُونَ، اِلـهي لا َتَرُدَّ حاجَتي، وَلا تُخَيِّبْ طَمَعي، وَلا تَقْطَعْ مِنْكَ رَجائي وَاَمَلي، اِلـهي لَوْ اَرَدْتَ هَواني لَمْ تَهْدِني، وَلَوْ اَرَدْتَ فَضيحَتي لَمْ تُعافِني، اِلـهي ما اَظُنُّكَ تَرُدُّني في حاجَة قَدْ اَفْنَيْتُ عُمْري في طَلَبَها مِنْكَ، اِلـهي فَلَكَ الْحَمْدُ اَبَداً اَبَداً دائِماً سَرْمَداً، يَزيدُ وَلا يَبيدُ كَما تُحِبُّ وَتَرْضى، اِلـهي اِنْ اَخَذْتَني بِجُرْمي اَخَذْتُكَ بِعَفْوِكَ، وَاِنْ اَخَذْتَني بِذُنُوبي اَخَذْتُكَ بِمَغْفِرَتِكَ، وَاِنْ اَدْخَلْتَني النّارَ اَعْلَمْتُ اَهْلَها اَنّي اُحِبُّكَ، اِلـهي اِنْ كانَ صَغُرَ في جَنْبِ طاعَتِكَ عَمَلي فَقَدْ كَبُرَ في جَنْبِ رَجائِكَ اَمَلي، اِلـهي كيف اَنْقَلِبُ مِنْ عِنْدِكَ بِالَخْيبَةِ مَحْروماً، وَقَدْ كانَ حُسْنُ ظَنّي بِجُودِكَ اَنْ تَقْلِبَني بِالنَّجاةِ مَرْحُوماً، اِلـهي وَقَدْ اَفْنَيْتُ عُمْري في شِرَّةِ السَّهْوِ عَنْكَ، وَاَبْلَيْتُ شَبابي في سَكْرَةِ التَّباعُدِ مِنْكَ، اِلـهي فلَمْ اَسْتَيْقِظْ اَيّامَ اغْتِراري بِكَ وَرُكُوني اِلى سَبيلِ سَخَطِكَ، اِلـهي وَاَنَا عَبْدُكَ وَابْنُ عَبْدِكَ قائِمٌ بَيْنَ يَدَيْكَ، مُتَوَسِّلٌ بِكَرَمِكَ اِلَيْكَ، اِلـهي اَنَا عَبْدٌ اَتَنَصَّلُ اِلَيْكَ مِمَّا كُنْتُ اُواجِهُكَ بِهِ مِنْ قِلَّةِ اسْتِحْيائي مِنْ نَظَرِكَ، وَاَطْلُبُ الْعَفْوَ مِنْكَ اِذِ الْعَفْوُ نَعْتٌ لِكَرَمِكَ، اِلـهي لَمْ يَكُنْ لي حَوْلٌ فَانْتَقِلَ بِهِ عَنْ مَعْصِيَتِكَ إِلاّ في وَقْت اَيْقَظْتَني لَِمحَبَّتِكَ، وَكَما اَرَدْتَ اَنْ اَكُونَ كُنْتُ، فَشَكَرْتُكَ بِاِدْخالي في كَرَمِكَ، وَلِتَطْهيرِ قَلْبي مِنْ اَوْساخِ الْغَفْلَةِ عَنْكَ، اِلـهي اُنْظُرْ اِلَيَّ نَظَرَ مَنْ نادَيْتَهُ فَاَجابَكَ، وَاْستَعْمَلتُهُ بِمَعونَتِكَ فَاَطاعَكَ، يا قَريباً لا يَبْعُدُ عَنِ المُغْتَرِّ بِهِ، وَيا جَواداً لايَبْخَلُ عَمَّنْ رَجا ثَوابَهُ، اِلـهي هَبْ لي قَلْباً يُدْنيهِ مِنْكَ شَوْقُهُ , وَلِساناً يُرْفَعُ اِلَيْكَ صِدْقُهُ، وَنَظَراً يُقَرِّبُهُ مِنْكَ حَقُّهُ، اِلـهي إنَّ مَنْ تَعَرَّفَ بِكَ غَيْرُ مَجْهُول , وَمَنْ لاذَ بِكَ غَيْرُ مَخْذُول، وَمَنْ اَقْبَلْتَ عَلَيْهِ غَيْرُ مَمْلُول، اِلـهي اِنَّ مَن انْتَهَجَ بِكَ لَمُسْتَنيرٌ , وِاِنَّ مَنِ اعْتَصَمَ بِكَ لَمُسْتَجيرٌ، وَقَدْ لُذْتُ بِكَ يا اِلـهي فَلا تُخَيِّبْ ظَنّي مِنْ رَحْمَتِكَ، وَلا تَحْجُبْني عَنْ رَأفَتِكَ، اِلـهي اَقِمْني في اَهْلِ وِلايَتِكَ مُقامَ مَنْ رَجَا الزِّيادَةَ مِنْ مَحَبَّتِكَ، اِلـهي وَاَلْهِمْني وَلَهاً بِذِكْرِكَ اِلى ذِكْرِكَ , وَهَمَّتي في رَوْحِ نَجاحِ اَسْمائِكَ وَمَحَلِّ قُدْسِكَ، اِلـهي بِكَ عَلَيْكَ إلاّ اَلْحَقْتَني بِمَحَلِّ اَهْلِ طاعَتِكَ , وَالْمَثْوىَ الصّالِحِ مِنْ مَرْضاتِكَ، فَاِنّي لا اَقْدِرُ لِنَفْسي دَفْعاً، وَلا اَمْلِكُ لَها نَفْعاً، اِلـهي اَنَا عَبْدُكَ الضَّعيفُ الْمُذْنِبُ، وَمَمْلُوكُكَ الْمُنيبُ، فَلا تَجْعَلْني مِمَّنْ صَرَفتَ عَنْهُ وَجْهَكَ، وَحَجَبَهُ سَهْوُهُ عَنْ عَفْوِكَ، اِلـهي هَبْ لي كَمالَ الانْقِطاعِ اِلَيْكَ، وَاَنِرْ اَبْصارَ قُلُوبِنا بِضِياءِ نَظَرِها اِلَيْكَ، حَتّى تَخْرِقَ اَبْصارُ الْقُلُوبِ حُجُبَ النُّورِ , فَتَصِلَ اِلى مَعْدِنِ الْعَظَمَةِ، وَتَصيرَ اَرْواحُنا مُعَلَّقَةً بِعِزِّ قُدْسِكَ، اِلـهي وَاْجَعَلْني مِمَّنْ نادَيْتَهُ فَاَجابَكَ، وَلاحَظْتَهُ فَصَعِقَ لِجَلالِكَ، فَناجَيْتَهُ سِرّاً وَعَمِلَ لَكَ جَهْراً، اِلـهي لَمْ اُسَلِّطْ عَلى حُسْنِ ظَنّي قُنُوطَ الاِْياسِ، وَلاَ انْقَطَعَ رَجائي مِنْ جَميلِ كَرَمِكَ، اِلـهي اِنْ كانَتِ الْخَطايا قَدْ اَسْقَطَتْني لَدَيْكَ، فَاصْفَحْ عَنّي بِحُسْنِ تَوَكُّلي عَلَيْكَ، اِلـهي اِنْ حَطَّتْني الذُّنوبُ مِنْ مَكارِمِ لُطْفِكَ، فَقَدْ نَبَّهَني الْيَقينُ اِلى كَرَمِ عَطْفِكَ، اِلـهي اِنْ اَنَامَتْنِى الْغَفْلَةُ عَنِ الاسْتْعِدادِ لِلِقائِكَ، فَقَدْ نَبَّهَني الْمَعْرِفَةُ بِكَرَمِ آلائِكَ، اِلـهي اِنْ دَعاني اِلى النّارِ عَظيْمُ عِقابِكَ، فَقَدْ دَعاني اِلَى الْجَنَّةِ جَزيلُ ثَوابِكَ، اِلـهي فَلَكَ اَسْأَلُ وَاِلَيْكَ اَبْتَهِلُ وَاَرْغَبُ، وَاَساَلُكَ اَنْ تُصَلِّيَ عَلى مُحَمَّد وَآلِ مُحَمَّد، وَاَنْ تَجْعَلَني مِمَّنْ يُديمُ ذِكَرَكَ، وَلا يَنْقُضُ عَهْدَكَ، وَلايَغْفُلُ عَنْ شُكْرِكَ، وَلا يَسْتَخِفُّ بِاَمْرِكَ، اِلـهي وَاَلْحِقْني بِنُورِ عِزِّكَ الاَْبْهَجِ، فَاَكُونَ لَكَ عارِفاً، وَعَنْ سِواكَ مُنْحَرِفاً، وَمِنْكَ خائِفاً مُراقِباً، يا ذَالْجَلالِ وَالاِكْرامِ، وَصَلَّى اللهُ عَلى مُحَمَّد رَسُولِهِ وَآلِهِ الطّاهِرينَ وَسَلَّمَ تَسْليماً كَثيراً .

Na biyu: Zai karanta wannan munajatin da xan Khuwailid ya rawaito ya ce: haqiqa wannan munajatin Amirul Muminin da 'ya'yan sa Ayimma (AS) ne, sun kasance su na addu'a/munajati/roqon Allah da shi cikin watan sha'aban, wannan munajati na da qarfin gaske ya tattaro tare da qunsar abubuwa maxaukaka masu yawan gaske wanda zai yi kyau ace mutum ya tsayar da hankalin sa wuri guda tare da tunani mai zurfi yayain karanta adduar, itace:
Ya Allah ka yi salati ga Annabi Muhammad da Iyalan sa, ka ji roqo na idan na na roqe ka, ka ji kira na idan na kira ka, ka karva daga gare ni idan na munajance ka, ina mai gudowa zuwa gareka, na tsaya wajen ka ina abin tausayi, ina miqa roqo na gare ka, mai kwaxayin sakamakon da ke hannun ka, ka san abinda ke cikin zuciya ta, ka san buqatu na, ka san abinda rai na ta qunsa, ba abinda zai vuyar maka nawa cikin zuciya da sakamako na, kai kaxai ne abinda na ke son kasancewa da shi, kai na nufa da dukkan makoma ta, na gudanar da daidai nawa akan kai na ya majivinci na cikin abinda ya zama nawa har zuwa qarshen rayuwa ta cikin sirri na da bayyana ta, raguwa ta da qaruwa ta amfani na da cutuwa ta na hannun ka ba hannun wanin ka ba, ya ubangiji na, idan ka hana ni wa ya isa ya azurta ni, idan ka tavar da ni wa ya isa ya taimake ni, ya Allah ina neman tsarin ka daga fushin ka da saukar fushin ka, ya Allah idan ban cancanci rahamar ka ba, kai ne mafi girman mai kyautar da za ka iya sanya ni cikin falalar ka mai yalwa, Allah ina tsaye da kai na tsakanin hannayen ka ina mai shiga inuwar ka sabida kyakykyawan zato na gare ka, ka aiwatar da dukkan abinda ka cancantar min da shi ka lulluve ni da afuwar ka, ya Allah idan ka yafe shin wa ya kai ka iya afuwa, idan kuma ajali na ya kusanto alhalin buqatu na sun qaranta da na kusance ka haqiqa ka sanya sai na yi iqrarin zunubai na zuwa gare ka, ya Allah na cuci kai na yayin da na ke duban ta, tir da ita idan baka gafarta mata ba, ya Allah biyyar ka baza ta gushe ba cikin ranakun rayuwa ta kada ka yanke ta gareni yayin mutuwa ta, ya Allah ta yaya zan fidda rai daga kyakykyawan kallon da nake maka bayan mutuwa ta, alhalin baka jiyar da ni komai sai kyakykyawa cikin rayuwa ta, Ya Allah ka jivinci lamura na domin kai kafi cancantar ka jivince ni, ka yi min alqawarin falalar ka don na ksance ina mai zaluntar kai na sabida jahilcin da ya rufe ni, Ya Allah haqiqa ka suturta min zunubai na a duniya alhalin na fi buqatar ta suturtu a lahira, matuqar baka bayyana ta ga bayin ka salihai ba, kada ka tashe ni da ita ranar al'qiyama a idon shaidu, ya Allah kayautar ka ta faxaxa buri na, ya Allah ka daxaxa min haxuwa da kai ranar da zaka tashe ni a gaban bayin ka, Ya Allah ina neman uzuri wajan ka irin uzurin wanda bai saki jiki da amintar uzurin sa ba, ka karvi uzuri na ya mafi girman wanda kewa masu munana aiyyuka uzuri, ya Allah kada ka mayar da buqata ta, kada ka tavar da kwaxayi na, kada ka yanke min fata na da buri na kan ka, ya Allah da ka yi nufin qasqantar da ni ba zaka shirye ni ba, da ka yi nufin kama ni da laifi ba za ka yi min afuwa ba, ya Allah bana zaton zaka juyar min da buqatun da na qarar da rayuwa ta ina nema daga wajan ka, ya Allah godiya gareka dawwamammiyar ta har abadan abada, mai qaruwa ba mai qarewa ba kamar yadda kake so kuma ka yarda, ya Allah idan ka kama ni da laifi na zan kama ka da afuwar ka, idan ka kama ni da zunubai na zan kama ka da gafarar ka, idan ka shigar da ni wuta zan gayawa ahalin ta cewar ni masoyin ka ne, ya Allah idan aiki na ya yi kaxan ya shigar da ni rahamar ka to kuma kwaxayi na da rahamar ka shi ma ya girmama gare ni, ya Allah ta yaya zan juyo daga gaban ka ina mai tavewa kan abinda na je roqo, bayan dukkan kyautata zaton da nake da shi kanka cewar zaka tseratar da ni da kyautar rahamar ka, ya Allah haqiqa na qarar da rayuwa ta cikin qwazon mantuwa wajan ka, na qarar samarta ta cikin yawan nisantar ka, ya Allah me ya sa na kasa tuna ruxuwa ta da lalaci na kan ka, na nutsu kan tafarkin fushin ka, ya Allah ni bawan ka ne xan bawan ka a tsaye gaban ka, yana mai kamun qafa da girman ka zuwa gare ka, ya Allah ni bawa ne shin zan iya jingina maka abinda na kasance ina fuskantar ka da shi na qarancin kunyar kallon ka, na kuma nemi afuwa gareka duk da cewa afuwa ni'imar girman ka ce, ya Allah bani da katavus wajan bautar ka tare da cewa na juya motsi na zuwa savon ka saidai cikin lokacin da ka tashe ni da soyayyar ka, kamar yadda na so zama, sai na shigar da kaina cikin girman ka, ka tsarkake zuciya ta daga dauxar gafala daga gareka, ya Allah ka dube ni duban wanda ka kira shi ya amsa maka, wanda ka qarfafae shio da taikon ka ya yi maka biyayya, ya wanda ke kusa bai nisanta ga wanda ya rude kan sa ba, ya mai kyautar da baya rowa ga wanda ke neman sakamakon sa, ya Allah ka hore min zuciyar da zata kusanta ni da kai sabida xaukinta zuwa gareka, da harshen da zai xagu zuwa gareka da gaskiyar sa, da kallon da haqqin sa ya kusance ka, ya Allah idan duk wanda ya san ka bai zama jahili ba, wanda ya xanxani soyayyar ba zai tave ba, wanda ka karva daga gareshi bai zai tava zama mai damuwa ba, ya Allah idan wanda ke kusa da kai zai zama wayayye, wanda ya yi riqo da kai zai nasara, haqiqa na shauqantu zuwa gareka ya ubangiji kada ka tavar da zato na ga rahamar ka, kada ka kange ni daga rangwamen ka, ya Allah ka tsayar da ni cikin ma'abota wilayar ka masu kwaxayin qarin soyayyar ka, ubangiji ka sanar da ni ta hanyar ta ambaton ka zuwa ambaton ka, ka sanya himma ta wajan taka rawar tsira na don sunayen ka da muhallin tsarkin ka, ya Allah ina roqon ka da girman ka ka sada ni da bigiren biyayyar ka, da sakamakon salihai daga yardaddun ka, domin ba zan iya karewa kaina komai ba, ba kuma zan iya mallakawa kaina komai ba, ya Allah ni awan ka ne mai rauni mai zunubi, abin mulkin ka ta dukkan vangarorin sa, kada ka sanya ni cikin waxanda ka xauke fuskar ga garesu, mantuwar sa ta rufe masa ido kan neman afuwar ka, Ya Allah ya bani kamalar dogaron kakaf gareka, ka ganar da banin zuciyoyin mu da hasken dubanta zuwa gareka, har ka qona ganin mummanan ganin zukatan mu da hasken haske, sai ta isa zuwa muqamin girma, ka zamar da rayukan mu rataye da izzar tsarkin ka, ya Allah ka sanya ni daga cikin waxanda idan ka kirasu su amsa maka, waxanda ke girgiza da girman zatin ka, wanda ke kusantar ka a sirrance ya yi aiki a bayyane, ya Allah ban dogara kan mummunan zatona na xauke tsammani daga gare ka, ban yanke buri na ba sabida tsananin kyan girman ka, ya Allah idan zunubai na sun nesanta ni daga gareka, ka yafe min da sabida kyautata dogaro na da kai, ya Allah idan ka shafen zunubai na sabida girman rangwamen ka, to haqiqa girman luxufin ka zai matuqar ladabtar da ni, ya Allah idan gafalata ta sa ni ina ganin nisan haxuwa da kai, haqiqa tunani zai ladabtar da ni yayin da na kallon alamomin ka, ya Allah idan tsananin azabar ka ya kiraye ni zuwa wuta, haqiqa girman sakamakon ka zai kira ni zuwa gwagwavan laxa, ya Allah gareka nake roqo kuma gareka na ke na fake ina mai kwaxayi, ina roqon ka da yin salati ga Annabi Muhammad da Iyalan sa, ka sanya ni matsayin dauwwama cikin girman ka, mara sava al'qawarin ka, marar gafala daga godiyar ka, wanda baya wulaqanta umarnin ka, ya Allah ka sada ni da hasken buwayar ka mafi kamala, na zama masanin ka, na juyawa duk mai kishiyantar ka, na zama mai tsoron ka tare da bibiyar lamuran ka, ya ma'abocin girma da buwaya, Allah ya yi salati ga Muhammad da Iyalan gidan sa tsarkaka da salamawa sallamawar gaskiya mai yawa.

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: