bayyinaat

Published time: 02 ,February ,2017      07:42:33
Allah madaukaki yana cewa: “Kuma idan kuka ji tsoron ba zaku yi adalci ba a game da marayu, to sai ku auri abin da ya yi muku dadi daga mata, biyu-biyu, uku-uku, da hudu-hudu, amma idan kuka ji tsoron ba zaku yi adalci ba, to (ku auri mace) daya ko abin da hannayenku suka mallaka…” .
Lambar Labari: 28
A wannan bangaren muna kawo muku bayanai kan abin da ya shafi "Auren mace fiye da Daya" bisa mahangar al'adu da musulunci da hikimar zartar da shi har zuwa hudu a musulunci, da soke-soke da suka babaye shi tare da amsoshinsu, hada da bayanin sukan yawan matan fiyaiyen halitta da amsar hakan. Lamari ne da ya samu kallo iri-iri da suka doru kan al'adu ko bahasin amfaninsa da rashin amfaninsa a cikin al'ummu, sai dai mafi muhimmanci shi ne mayar da lamarin bisa maslahar al'ummu da kasashe tare da la'akari da zamani da wuri. 
Auren Mace Fiye Da Daya
Allah madaukaki yana cewa: "Kuma idan kuka ji tsoron ba zaku yi adalci ba a game da marayu, to sai ku auri abin da ya yi muku dadi daga mata, biyu-biyu, uku-uku, da hudu-hudu, amma idan kuka ji tsoron ba zaku yi adalci ba, to (ku auri mace) daya ko abin da hannayenku suka mallaka…” . 
Musulunci ya halatta auren mace sama da daya sakamakon yana son ya yi iyaka ga abin da ya taras na auren mata barkatai ba tare da wata iyaka ba, don haka yin auren mace sama da daya bai samo asali daga musulunci ba sai dai musulunci ya yi kokarin ganin yi wa abin iyaka da hudu ne daidai maslahar da Allah (s.w.t) mahaliccin mutum ya gani. Bayan iyaka da musulunci ya bayar sai kuma ya sanya sharadin adalci a ciki, don haka ba kowane mutum ne zai auri mace sama da daya ba sai wanda yake da hujjar zai iya adalci. Wannan adalcin idan ya kasance da ma’anar da ya zo a fikihu ne, to zai yi wahala a samu masu damar yin mace sama da daya ke nan sai daidaiku matukar gaske. Amma idan ya kasance yana nufin iyakacin tsakanin matan to wannan zai iya bude kofa ga wasu mutane da zasu iya haka ne kawai. Sannan ta wani bangaren kuma sharadi ne sai mace ta yarda a duk aure kowane iri ne, wannan sharadi hakki ne na mace da zata yi aure ko da kuwa da wanda ba shi da mata ne. Don haka da zata ce ba ta yarda ta auri mai mata ba, da ba ta yi laifi ba a mahangar musulunci, haka nan da namiji ya ki auren mace sama da daya a shari’ar musulunci bai yi laifi ba. 
Wannan yana nuna cewa dokar an sanya ta ne don wanda suka ga dama kuma zasu iya, asali ma da wani ya ce ba zai yi aure ba bai yi laifi a shar’ance ba matukar zai iya kare kansa da kamewa daga fasadi sai dai ya bar sunnar annabi (s.a.w) mai karfi. Musulunci yana ganin halaccin auren mata har hudu a aure na da'imi, sai dai da sharadin adalci tsakaninsu, da wannan ne musulunci ya warware matsalar mata marasa aure da zaurawa, kuma abin da aka sani a cikin al'umma wanda ya tabbata a ilmance shi ne cewa a mafi yawan al'ummu mata sun fi maza yawa, idan da babu wannan doka to wannan yana nufin mata da yawa su zama ba su da ma'aurata. 
Musulunci ya gindaya sharadin adalci tsakanin mata a zaman tare, da kwanan daki, da ciyarwa, ba kowa zai iya ciyar da ko da biyu ba sai mai yalwa, sannan kuma akwai hanya ta addini ta shari’a da mace za ta iya sanyawa na ka da a yi mata kishiya, kamar idan ba ta so kuma suka yi sharadi yayin aure kan cewa ba zai mata kishiya ba to dole ne ya kiyaye sharadin matukar wannan bai saba wa dokar nan ta "Sai dai sharadin da ya halatta haram ko ya haramta halal” , ko da yake wannan mas'ala ce da aka yi sabani tsakanin malamai. 
Auren mace fiye da daya wani abu ne da ya kasance mahallin binciken malamai da masana a wannan zamani ta yadda ya kasance duniya tana ganin sa a matsayin wani abu na danne hakkin mace, kuma tun da musulunci ya baiyanar da halaccinsa a fili don haka ne ya kasance abin suka ga masu binciken hakkin dan'adam musamman a kasashen yammacin duniya. Ga dukan alamu sukan da yammancin duniya yake yi wa musulunci sakamakon wannan lamarin na auren mace fiye da daya saboda tasirin al'adun da suke ciki ne na hanin auren mace fiye da daya da Coci ta yi ne. Sai suka taso ba su san da shi a cikin al'adunsu na yau ba, don haka ne ya kasance abin tattaunawa a teburin bincike kan hakkin dan'adam musamman mace. 
A bisa hakika akwai tasirin mazhaba, addini, da ala'adu a cikin sukan wannan lamari da suke yi, ta yadda ko da kuwa zai kasance hanya ce ta warware matsalolin zaman tare da ta al'umma to ba zai samu karbuwa ba domin wani abu ne da ya saba wa al’adar yammacin duniya. Kuma kamar yadda Imam Ali (a.s) yake cewa: "Mutane makiya abin da suka jahilta ne" . zamu ga yammancin duniya yana kin wannan lamarin saboda ya jahilce shi ko ya tsane shi.
Ko da yake a yau hatta da wasu masanan musulmi sun fara binciken cewa shin halaccin yin auren mace fiye da daya ya kebanta da lokacin Annabi (s.a.w) ne, ko kuwa yana nan har a wannan zamanin. Wannan kuwa yana da tasiri da yanayin da duniya ta samu kanta a ciki na wayewar zamani. Ta yadda wasu suna ganin idan nan gaba duniya ta kasance duk ko'ina musulunci ne to zai iya yiwuwa wannan dokar ta fadi. Sai dai idan mun duba abin da ya zo na cewa: "Halal din Muhammad halal ne har zuwa ranar kiyama, haram dinsa haramun ne har zuwa ranar kiyama" . Zamu samu amsar cewa lallai wannan bai kebanta da lokacin Annabi ba kamar yadda bai kebanta da wadancan mutane da suka rayu tare da shi ba. 
Wani abin da ya sanya wadannan soke-soken shi ne; Yammancin duniya sun kalli musulmi ne da suka yi mummunan amfani da wannan doka ta halaccin auren mace fiye da daya, ta yadda a wasu yankunan ko gun wasu mutanen ya kasance an dauke shi domin biyan bukatun sha'awar duniya. Hada da wani lokacin sukan fifita wata a kan wata sai a samu gaba tsakanin matan da kuma 'ya'yansu da aka fi sani da 'ya'yan kishiyoyi. Sai maimakon su soki abin da wadancan musulmin suke yi da ya saba wa musuluncin sai suka koma sukan ainihin musuluncin. Hada da cewa addinin Kiristanci da shi ne ya yadu a yammacin duniya yana gasa da musulunci duk inda yake a matsayin wani addini da zai iya samun ci gaba fiye da duk wani addini. Musamman idan mun duba cewa; musulunci ya hada duk abin da ya shafi duniya da lahira ne, kuma wadannan abubuwa biyu ne ya sanya su gaba da shi domin yana da hanyar da ta bambata da hanyar da suka nuna wa duniya a matsayin hanyar warware wa dan'adam abin da yake damun sa.
Hikimar Wannan Halaccin
Dalilan da suka sanya wannan halaccin a musulunci suna da yawa, sai dai zamu yi nuni da wasu daga ciki kamar haka: 
1- Yanayin Halitta: Idan mun duba nau'in halitta da rayuwar namiji da mace zamu samu cewa; Mata suna balaga da wuri fiye da maza, ta yadda zasu iya samun haihuwa da wuri. A kasashen da suke da madaidaicin yanayi mata suna balaga a shekara ta goma namiji kuwa sai a shekara ta sha biyar. Don haka da zamu kaddara cewa a wuri daya an haifi yara maza  mata ma 50 a duk shekara zuwa shekaru 20, idan mun kaddara babu wanda ya mutu daga cikinsu, to za a samu yara maza 1000 ke nan, da mata 1000. 
A nan ke nan idan aka samu shekaru 20 zamu samu mata 550, da maza 300 da suka isa aure ke nan. Wannan jadawalin yana nuna mana adadin matan da suka isa aure daga cikin 'yan mata 1000 da ake da su cikin shekaru 20: 
'Yan mata guda 50, 'yan shekaru 20
'Yan mata guda 50, 'yan shekaru 19
'Yan mata guda 50, 'yan shekaru 18
'Yan mata guda 50, 'yan shekaru 17
'Yan mata guda 50, 'yan shekaru 16
'Yan mata guda 50, 'yan shekaru 15
'Yan mata guda 50, 'yan shekaru 14
'Yan mata guda 50, 'yan shekaru 13
'Yan mata guda 50, 'yan shekaru 12
'Yan mata guda 50, 'yan shekaru 11
'Yan mata guda 50, 'yan shekaru 10
Adadinsu: 550
Amma daga cikin maza 1000 da ake da su 300 ne kawai suka isa aure kamar haka: 
'Yan maza guda 50, 'yan shekaru 20
'Yan maza guda 50, 'yan shekaru 19
'Yan maza guda 50, 'yan shekaru 18
'Yan maza guda 50, 'yan shekaru 17
'Yan maza guda 50, 'yan shekaru 16
'Yan maza guda 50, 'yan shekaru 15
Adadinsu su 300 ne suka isa aure
Wannan yana nuna cewa a cikin shekaru 20 adadin 'yan mata da zasu iya haihuwa ya ninka na maza sau biyu ke nan. 
2- Sannan lissafi ya nuna cewa a cikin al'umma adadin mata ya fi na maza yawa saboda wasu dalilai kamar haka: 
a- Rashin lafiya ya fi kashe maza fiye da mata, musamman da yake jikin mata ya fi karfin yakar kwayoyin cuta . 
b- Aikin da maza suke yi na karfi yana sanya asararsu da yawa fiye da mata; wannan ya hada da tafiye-tafiye kan teku da koguna, da na kasa, da tukin mota, da haka kasa, da fitar da ma'adinai, da haka fayef, da dakon kaya masu nauyi, da sauran wahalhalu yawanci aikin maza ne. wadannan wahalhalun sukan sanya asarar maza da yawa. 
c- Lissafi ya nuna cewa adadin mata ya fi na maza yawa, Lissfi ya nuna cewa a Faransa adadin mata 'yan shekara 60-65 ya ninka na maza masu wadannan shekarun. Tafsirin Dandawi yana kawo wani lissafi kamar haka: 
- A Italiya yawan mata ya fi na maza yawa da adadin miliyan biyu. 
- A Ingila kuwa mata sun fi maza yawa da miliyan daya da rabi. 
- A Jamus mata sun fi maza yawa da miliyan biyu. 
- A Faransa kuwa mata sun fi maza yawa da miliyan daya da rabi. Wadannan matan da suke rara ne da suka wuce adadin maza, babu mazan da zasu aura ke nan. (Tafsirin Dandani: J; 16, S; 54). 
3-Yaki yana cikin abin da yake rage mazaje a ko da yaushe, tarihin dan'adam cike yake da rigima da yake-yake, abin da mutanen duniya suke gani a kullum ba a boye yake ba, kashe-kashen da ake fama da su da sanya bama-bamai a kasashen duniya musamman a kasashen Gabas ta Tsakiya, da yakokin da ake fama da su a yau a gabashin duniya, da kuma rigingimun kasashen Afrika, bai buya ga kowa ba. Sannan idan mun duba babu wanda yake salwanta a wannan hare-hare galibi sai mazaje. 
4- Al'adar nan ta mata ta yin jinin haila a duk wata tana daga cikin abin da yake hana su gamsar da mazajensu a cikin wadannan kwanankin, wasunsu sukan yi kwanaki goma ko kasa da hakan. Idan mun duba kuwa zamu ga mazajensu suna bukatarsu a irin wadannan lokutan. Hada da cewa akwai lokutan da ba sa kaunar namiji ya kusance su musamman idan suna da ciki tara. A duk wannan yanayin zamu ga musulunci ya dauki matakin halatta wa namiji yin sama da mace daya idan dai yana bukatar hakan tare da kiyaye sharudan da ya gindaya. 
5- Mata sukan daina haihuwa a wasu lokuta na rayuwarsu; idan mace ta kai shekaru hamsin zamu ga ta daina haihuwa, yayin da namiji yakan kai shekaru casa'in ko sama da hakan yana iya haihuwa. Sannan akwai wasu mazajen da matansu sun kai wadannan shekarun amma suna bukatar haihuwa. Don haka babu abin da zai hana namiji yin aure domin ya samu ci gaba da haihuwa idan dai akwai bukatar hakan gare shi ko ga al'umma. 
A nan musulunci bai haramta masa yin wani aure ba domin akwai zabi uku ne da ya rage gabansa. Ko dai a hana masa yin wani aure sai ya yi zina domin ya samu 'ya'ya, ko kuma a hana shi samun 'ya'yan gaba daya, ko kuwa ya yi aure da mace ta biyu. Don haka ne musulunci ya guje masa wadancan hanyoyin na farko ya zaba masa mafificiyar hanya ta uku, ta yin aure domin samun 'ya'ya na halal. 
Bayan duk wadannan bayanai, zamu ga cewa musulunci da ya sanya halaccin yin auren sama da mace daya, ya yi kokarin ganin kare hakkin mata ne, da samar musu mafita kan matsalolin rasa mijin aure. Domin idan babu wannan dokar wasu da yawa daga cikinsu ba zasu samu aure ba bayan kuwa suna bukatar yin sa. Da musulunci ya hana wannan auren da ya sanya mata da yawa cikin matsalolin bakin ciki da na tunani ta yadda zasu ga sun kasa samun mazajen aure da zasu nutsu a wurinsu alhalin sauran mata 'yan'uwansu suna da su. 
A cikin duk dokokin da musulunci yake sanyawa yana kiyaye maslahar al'umma ne kafin ya duba ta mutum daya don haka ne ya sanya irin wadannan dokoki. Sau da yawa daidaikun mata sukan ji zafin yi musu kishiya sai dai wannan zafin bai kai kimar zafin rashin doka da lalacewar al'umma da fasadi da daure hannun mazaje masu sharudan auren sama da daya ba. Don haka duk sa'adda maslahar daidaiku ta hadu da ta jama'a ko gyara al'umma da sawwaka mata hanyoyin rayuwa, sai musulunci ya fifita maslahar jama'a a kan ta daidaiku. 
Babu kokwanton cewa matsaloli ba zasu faru ba idan babu wannan dokar domin wannan lamari ne da zai iya haifar da fasadi mai tsanani. Wadancan matan da zasu rasa aure, to babu makawa akwai masu yawa daga cikinsu da zasu bi wasu mazajen kamar yadda hakan yake faruwa a yankunan da babu wannan doka kamar yammacin duniya. Sa'annan su ma mazaje a irin wadancan yankunan sukan yi kawance da mata barkatai saboda ba su da ikon karawa bisa doka, sai suka yawaita na shasahnci da sunan 'yancin dan'adam. 
Wasu suna nuni da cewa dokar halaccin auren mace fiye da daya tana sanya wasu mazajen su kara aure don su takura ta farko ko su dauki fansa kanta saboda wani bacin rai da suka samu da ita don haka ke nan an bude kofar da zasu yi mummunan amfani da ita. A nan a fili yake cewa mazajen da suke yin aure don wadannan mugayen halaye tun farko ba sa cikin wadanda shari'a ta halatta wa yin auren mace fiye da daya domin sun rushe sharadin da zai ba su wannan damar, idan kuwa suka yi to su saurari sakamakon keta hurumin Allah da suka dauki keta shi wasa. 
Masu ilimi sun kawo bayani kan cewa a bisa gwaji namiji yana neman dandano ne don haka sau tari ba ya wadatuwa da mace daya yayin da mace kuwa tana neman gamsuwa ne, da wannan ne suka fitar da natijar cewa lallai dokar tana da amfani wurin warware matsalar al'umma baki daya ba kawai namiji ba. Masu wannan binciken suna ganin rashin dokar zai sanya namiji yawo barkatai ba tare da wata iyaka ba, don haka daure shi da iyakance karfinsa da mata har zuwa hudu zai yi maganin yawonsa barkatai. Suna kari da cewa hatta a kalmar so namiji yana iya gamsuwa da kalma daya kawai yayin da matarsa ta ce ina son ka, amma shi yana bukatar ya rika maimaita wannan kalmar lokaci bayan lokaci. 
Wasu kuwa suna kawo lamarin ta fuskacin lafiyar mace da kiyaye mata yarintarta yayin da suke ganin cewa namiji zai iya auren mata biyu ko uku, sai kowacce ta haifi 'ya'ya biyu ko uku sai su kulle mahaifunsu. Suna ganin maimakon auren mace daya ta kawo ‘ya’ya tara, to sai a auri mata biyu kowacce ta kawo 'ya'ya biyu ko uku ta tarbiiyantar da su, sai ta saura a matsayin budurwa ba zata tsufa da yawa ba tare da samun kiyaye lafiyarta, kuma idan ta tsufa ba zata rakwarkwashe sosai ba. Wannan ra'ayin yana ganin bisa gwaji cewa duk sa'adda mace ta haifu to tana samun hasarar wasu kwayoyi masu amfani da yawa a jikinta kuma rashinsu da karancinsu yana sanya ta tsufa da wuri, amma karancin haihwa zai sanya ta kiyaye karfinta da lafiyarta har tsufa. 
Munin Rashin Dokar
Idan aka rasa irin wannan doka to babu makawa za a samu fasadi mai yawa da hadari da zai durfafi al'umma. Bincike ya nuna cewa al'ummar da ta rasa wannan dokar tana fuskantar matsaloli masu yawan gaske da zamu yi nuni da wasu kamar haka. 
1- Yawaitar 'ya'yan zina, ta yadda kula da su zai zama nauyi ne babba a kan kasa. 
2- Cututtuka da matsalolin tunani da damuwa zasu durfafi mata fiye da yadda ake tsammani ta yadda zasu zama hadari ga al'umma. 
3- Kame kai da kunya zasu yi karanci matuka, ta yadda zasu yi fata-fata da mutuncin al'umma. 
4- Karancin al'umma, domin matan da zasu shiga fasadi zasu yi kokarin ganin ba su kawo wa al'ummarsu 'ya'ya ba saboda hadarin da zai biyo baya bisa al'ada, ga kuma wahalar daukar nauyinsu. Sabanin idan ya kasance akwai hanyar da zasu samu aure, wannan tsoro babu shi a wurinsu. 
Don haka ne zamu ga al'ummar da ba ta da wannan dokar mata marasa mazaje sun yawaita, don haka sai ya kasance ana samun yawaitar hana daukar ciki ko zubar da shi idan an samu. Idan mun duba wadannan lamurran da kyau zamu ga sun mamaye kasashen yamma masu sukan wannan dokar ta musulunci. Hada da cewa za a iya samun matsaloli sama da hakan idan babu wannan doka kamar cewa: Idan mace ba ta haihuwa, ga mijinta yana son ya samu 'ya'ya, kuma mijinta ba ya son rabuwa da ita. Idan mace ba ta da lafiya kuma likita ya hana ta daukar ciki ko saduwa da namiji, sannan mijinta ba ya son rabuwa da ita. A irin wannan ba shi da wata mafita sai kara wata matar.
Da yawa masu tunani a yammacin duniya suka yi wa al'ummarsu tunanin samun mafita da ta yi daidai da ta musulunci sai dai al'adu da dokoki da addininsu ba su yarda ba. Har ma wata masaniya tana cewa: "Da za a halatta yin auren mace fiye da daya, da ba a samu wannan azabar ba ta samun 'ya'yan banza da uwaye marasa galihu da kaskanci da tabewa irin wannan ba ". Kamar yadda Shupanhawar ya yi nuni da cewa; da akwai irin wannan doka a turai da mata da yawa ba su rayu babu mazaje ba . 
Wasu kuma suna sukan lamarin ne bisa la’akari da yadda musulmi suka yi amfani da wannan dokar ta yadda bai dace ba; kamar mutanen da suke da burin kuntata wa matansu sai kawai su fanshe da yi masu kishiyoyi, ko kuma su rika nuna bambanci tsakanin wadannan matan nasu. Sai dai masu wannan tunanin ana iya ba su amsa da cewa: Ai tun farko musulunci bai yarda wadannan mutanen su yi mata sama da daya ba, musulmi da yawa sun jahilci wannan dokar, da yawa sun dauka suna iya yin mata biyu alhalin bai halatta gare su ba. Musulunci ya bayar da izinin wannan lamarin ne ga mutanen da suke adalai kan lamarin . 

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: