bayyinaat

Published time: 12 ,November ,2018      00:16:29
Amma a littafin Buhari kana iya ganin isra’iliyanci a wasu ruwayoyinsa, duba ka ga wasu misalai daga wadannan ruwayoyi domin ka gani a fili:
Lambar Labari: 281
Ban sani ba, yaya Ishak (A.S) ya kasance bai san muryar ‘ya’yansa ba! Kuma yaya babarsa zata nemi albarka daga addu’ar Ishak tana mai yin karya, yaya kuma ‘ya’yanta zasu yi karya, kuma wane Annabi ne wannan da gidansa yake irin wannan gidan, sannan kuma wane irin bayar da ma’anar sunaye ne aka yi wa wadannan ‘ya’ya da aka cirato daga asalin wadannan kalmomin.
Amma a littafin Buhari kana iya ganin isra’iliyanci a wasu ruwayoyinsa, duba ka ga wasu misalai daga wadannan ruwayoyi domin ka gani a fili:
Buhari da sanadinsa daga Abuhuraira ya na cewa: Babu wani Annabi sai shedan ya shfe shi lokacin da za a haife shi sai ya fado ya na mai kuka banda Maryam da danta (Buhari, j 4, shafi: 164).  Ban sani ba idan wannan falala ce, to don me aka hana annabinmu alhalin shi ne: shugaban annabawa, kuma idan ba matsayi ba ne to mene ne amfanin kawo shi, kuma mene ne laifin sauran annabawa da shedan zai shafe su.
Buhari ya kawo da sandinsa zuwa ga A’isha uwar muminai cewa an yi wa Annabi (S.A.W) sihiri har sai da ya kasance ya na ganin kamar ya yi wani abu, amma bai yi shi ba (Buhari, j 4, shafi: 122).
Kuma Buhari ya ruwaito a kissar Musa (A.S) yayin da mala’ikan mutuwa ya zo domin ya karbi ransa sai ya mare shi a kan idanuwansa sai ya cire daya… har sai da Allah ya ce da mala’ikan mutuwa koma zuwa gare shi ka ce masa ya dora hannunsa a kan fatarsa, ya na da yawan shekarun da tafinsa ya rufe na adadin yawan gashi (Buhari, j 4, shafi: 157).
A bisa hakika wannan lamarin ya na da mamaki, domin gashin da hannun tafinsa zai rufe zai iya kaiwa zuwa dubu biyar, kuma shekarun annabin Allah Musa sanannu ne, imma dai wanan ruwaya ta kasance karya, imma kuma mu karyata tarihi.
Buhari ya karbo daga ummul muminin A’isha cewa Annabi (S.A.W) ya zauna kwanaki kaza ya na ganin kamar ya zo wa iyalansa amma bai zo musu ba, har dai ya ce: Ya ke A’isha Allah ya yi mini bayanin wani abu da nake tambayarsa da wasu mutane suka zo min daya ya zauna gun kaina dayan kuma gun kafafuna, sai wanda yake gun kafafuna ya ce da dayan, me ya samu mutumin ne? sai ya ce: an yi masa sihiri, sai ya ce: Waye ya yi masa? Sai ya ce: Lubaid dan A’asam… har dai sammun da aka yi masa ya tafi bayan tsawon lokaci (Buhari, j 8, shafi: 18).
Wato: wannan ruwaya tana nuna cewa Annabi ya rasa hankalinsa ba ya iya gane lokacin da ake yi masa wahayi har tsawon lokaci, idan kuwa ya halatta Annabi ya samu irin wannan rashin lafiyar to yaya kuwa za a aminta da wahayi, kuma ko yaya dai wannan nauyi ya na kan mai ruwaya da Buhari, kuma littafin Buhari ya na kunshe da irin wannan nau’i na akidun isra'iliyanci kamar dai na abin da ya ambata a babin neman izini, a babin yin farawa da sallama, ya ce:
Da sanadinsa daga Abuhuraira daga Annabi (S.A.W) Allah ya halicci Adam (A.S) a bisa kamarsa ne, tsayinsa zira’i sittin yayin da ya halicce shi sai ya ce masa tafi ka yi wa wadancan jama’ar na mala’iku da suke zaune ka ji yaya zasu gasihe da kai domin ita ce gaisuwarka da kai da zuriyarka, sai ya ce: Asslamu alaikum. Sai suka ce: Assalamu alaika wa rahmatul-Lah, sai suka kara wa rahmatul-Lah. Don haka dukkan wanda zai shiga aljanna ya na kasancewa kamar girman Annabi Adam (A.S) ne, kuma halittu ba su gushe ba suna raguwa har yanzu (Buhari, j 8, shafi: 50).
Da sauran dai ruwayoyi irin wadannan wadanda suke da yanayi na nisanta daga musulunci saboda jingina wa Allah jiki, amma duk da haka ba mu samu mai jifan wadannan tunani da cewa fita ne daga musulunci ba ko kuma yahudanci ne, duk da cirato wannan da suka yi daga isra’iliyanci zuwa musulunci, amma da mutum zai yi Shi’anci nan da nan sai a ga shi’ancinsa yahudanci ne ko nasaranci, kuma duk wani mummuna da shara sai a watsa ta kansa tare da cewa duk wani laifi da wani ya yi ya na kansa ne, kuma mun riga mun nuna cewa duk wani abu da ya kore musulunci to Shi’anci ya na kin sa gaba daya.
Idan ma mun kaddara cewa akwai wasu fikirori da farisawan da suka zama Shi'a suka cirato suka taho da su tare da su, kamar fadin cewa akwai hakkin Allah kamar yadda Farisawa suke fada wa game da sarakunansu kuma Shi'a suka fadinsa ga imamansu duk da kuwa akwai bambanci tsakanin wadannan abubuwan biyu, to duk wannan ba zai zama aibi ba ga akida matukar ta samu asasi da asalinta ne da ta dogare da shi daga musulunci kuma wannan la’amari ne da yake sananne gun Shi'a da suke kiyaye su, ta yadda idan dai ka ga sun yi riko da wani abu to musulunci ne.
Kuma mu muna sane da cewa dukkan asasai da suke iyakance musuluncin musulmi to su ne dai abin da Annabi (S.A.W) da kansa ya iyakanta su da kansa kamar yadda ya zo a sahihul Buhari daga Anas cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Duk wanda ya yi sallarmu, ya fuskanci alkiblarmu, kuma ya ci yankanmu, to wannan shi ne muslumi, kuma alkawarin Allah da manzonsa sun hau kansa, don haka kada ku keta wa Allah alkawarinsa.
Kamar yadda Buhari ya fitar da wannan daga Ali (A.S) cewa ya tambayi Annabi (S.A.W) ranar yakin Haibar cewa a kan me zan yaki mutane? Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Ka yake su har sai sun shaida babu wani abin bauta sai Allah kuma hakika Muhammad Manzon Allah ne, idan suka yi haka to sun kare jininksu daga gare ka (Sahih Muslim, j 2, babin falalar Ali (a.s). Buhari, j 3, babin yakin khaibar).
Imam Ja’afar Sadik dan Muhammad (A.S) ya na cewa: Musulunci shi ne shaidawa babu wani abin bauta sai Allah da gaskatawa da Manzon Allah kuma da wannan ne ake kare jini kuma a kansa ne ake yin auratayya da gado." (Fusulul muhimma, Sharafuddin, shafi: 18)  Don haka a bisa zahirin haka ake siffantuwa da musulunci kuma wannan suna ya na tabbata ga wanda ya yi kalmar shahada kuma koda bai yi imani da Imamanci da cewa nassi ne daga Allah ba, da kuma cewa hkki ne na Allah, koda kuwa ya na ganin imamanci ya na tabbata da shura kuma hakki ne na mutane da suke sanya shi inda suka so!
Kai ko da bai yi imani da cewa Imamanci nassi ne ba, kuma ko da ya wuce hakan malaman musulunci ba sa kafirta shi, kuma da yawa daga malamai sun tafi a kan cewa ba a kafirta ko fasikantar da musulmi saboda wani abu da ya kudurce ko ya aikata, kuma dukkan wanda ya yi ijtihadi kan wani sai ya bi abin da yake ganin gaskiya ne, to za a ba shi lada guda biyu idan ya dace, idan kuwa ya yi kuskure zai samu lada daya, kuma wannan shi ne fadin Ibn Abi-laili da Abuhanifa da Shafi'i da Sufyanus sauri da Dawud dan Ali kuma shi ne fadin da yawan sahabbai (Alfusul, Ibn hazam, j 3, shafi: 247).
An ruwaito daga Ahmad dan Zahr Sarakhsi, kuma ya na daga sahabban Abul Hasan al’ash’ari, kuma a gidansa ne al’ash’ari ya rasu ya ce: Ash’ari ya umarce ni da in tara masa sahabansa sai na tara su sannan sai ya ce: Ku shaida mini cewa ni ba na kafirta wani daga ma’abota alkibla don wani sabo da ya yi domin ni na ga dukkansu suna nuni ne zuwa ga abin bauta daya, kuma musulunci ya na hada su ya na game su (Alfusulul muhimma, Sharafuddin, shafi: 32).
To duk bayan wannan lamari mene ne abin da ya kawo alakanta Shi’anci da yahudanci ko kuma cewa a cikinsa akwai fikirorin Farisanci ko kuma alamomin Farisanci, sannan kuma idan akwai wasu fikirorin da idan mun kaddara cewa wanda suka muslunta sun kawo su kuma sun bi su, ai ba ta wuce wani ra'ayi ne da ya yi riko da shi da wani dalili ko kuma ya zamanto bidi’a kamar yadda muka kawo, kuma ka san ra’ayoyin malamai a kan hakan.
Wannan irin wuce gona da iri ne kan musulunci da kuma daukar alhakinsu ya na daga kaucewar tunani, kuma da sannu zaka san abin da Shi'a suka tafi a kansa daga Littafi da Sunna, kuma koda wasu sun dauka sun samu ne daga Farisawa sakamakon karancin saninsu ko kuma mummunan nufi da suke da shi, kuma Allah ne magani kan komai.
c- Wannan irin da’awar da ake yi ta Farisancin Shi’anci zamu tabatar maka da cewa lamarin akasin haka ne, kai idan ma ta inganta to ba laifi idan dai bafarise ya kasance musulmi kuma mu muna ganin a addinin musulunci babu kabilanci, kuma takenmu shi ne: "Ya ku wadanda suka yi imani mu mun halitta ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku jama’u da kabilu domin ku san juna, hakika mafi girmanku a wajen Allah shi ne mafi tsoronku gare shi" (Surar Hujurat: 13).
Don haka ne ma wannan mataki ya yi daidai da na musulunci kuma idan muna magana ne ta kabilanci to da sai mu kebanta da luggarmukawai kuma babu wata lugga da zata kasance mun yarda dai ta, tare da cewa hankali ya na kiran ne zuwa ga girmama mutane da kabilu, kuma maganar Imam Sadik (A.S) ta kayatar matuka a nan yayin da yake cewa: Ba ya daga bangaranci (Bangaranci da kabilanci) ka so mutanenka, sai dai ta’asubanci shi ne ka sanya ashararan mutanenka sun fi zababbun wasu mutane da ba su ba.
Musulunci ba ya bambancewa tsakanin wani jinsi da wani, kuma ba ya la’akari da musulmi don ya na da wani yare kawai, amma idan dai mai magana ya na fakewa ne da yare karkashin wata manufa daban da yake da ita, to lallai wannan mutumin da yake ganin mutane kamar gafalallu shi ne hakikanin gafalalle, kuma nan gaba kadan zamu ga hadafin irin wadannan mutane da suke da wannan raye-rayen.


comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: